إِذۡ عُرِضَ عَلَيۡهِ بِٱلۡعَشِيِّ ٱلصَّـٰفِنَٰتُ ٱلۡجِيَادُ
(Ka tuna) lokacin da aka jera masa ingarmun dawakai masu tsayawa da qafa uku da yamma
فَقَالَ إِنِّيٓ أَحۡبَبۡتُ حُبَّ ٱلۡخَيۡرِ عَن ذِكۡرِ رَبِّي حَتَّىٰ تَوَارَتۡ بِٱلۡحِجَابِ
Sai ya ce: “Lalle ni na fifita son dukiya (watau dawakai) a kan ambaton Ubangijina (watau sallar La’asar) har sai da (rana) ta faxi.”
رُدُّوهَا عَلَيَّۖ فَطَفِقَ مَسۡحَۢا بِٱلسُّوقِ وَٱلۡأَعۡنَاقِ
(Ya ce): “Ku dawo min da su;” sai ya riqa saran su ta qafafu da wuyoyi
وَلَقَدۡ فَتَنَّا سُلَيۡمَٰنَ وَأَلۡقَيۡنَا عَلَىٰ كُرۡسِيِّهِۦ جَسَدٗا ثُمَّ أَنَابَ
Kuma haqiqa Mun jarrabi Sulaimanu Muka xora wani jiki a kan gadonsa na mulki[1], sannan ya koma (kan mulkinsa)
1- Wannan wata jarrrabawa ce da Allah ya yi wa Annabi Sulaimanu () game da mulkinsa, lokacin da ya xora wani jiki a kan kujerarsa ta mulki. Mafi yawan malamai sun ce wani shaixani ne Allah ya ba shi ikon hayewa kujerarsa.
قَالَ رَبِّ ٱغۡفِرۡ لِي وَهَبۡ لِي مُلۡكٗا لَّا يَنۢبَغِي لِأَحَدٖ مِّنۢ بَعۡدِيٓۖ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡوَهَّابُ
Ya ce: “Ya Ubangijina, Ka gafarta min, Ka kuma ba ni wani mulki wanda bai kamaci wani ba a bayana ya sami irinsa; lalle Kai Kai ne Mai yawan kyauta.”
فَسَخَّرۡنَا لَهُ ٱلرِّيحَ تَجۡرِي بِأَمۡرِهِۦ رُخَآءً حَيۡثُ أَصَابَ
Sai Muka hore masa iska tana tafiya da umarninsa a natse duk inda ya fuskanta
وَٱلشَّيَٰطِينَ كُلَّ بَنَّآءٖ وَغَوَّاصٖ
Da kuma shaixanu masu yin kowane irin gini da kuma masu yin nutso (a ruwa)
وَءَاخَرِينَ مُقَرَّنِينَ فِي ٱلۡأَصۡفَادِ
Wasu kuma an xaxxaure su cikin maruruwa
هَٰذَا عَطَآؤُنَا فَٱمۡنُنۡ أَوۡ أَمۡسِكۡ بِغَيۡرِ حِسَابٖ
Wannan kyautarmu ce, to ka yi kyauta ko ka hana ba da wani bincike ba
وَإِنَّ لَهُۥ عِندَنَا لَزُلۡفَىٰ وَحُسۡنَ مَـَٔابٖ
Lalle kuma shi tabbas yana da kusanci a wurinmu, da kuma kyakkyawar makoma
وَٱذۡكُرۡ عَبۡدَنَآ أَيُّوبَ إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥٓ أَنِّي مَسَّنِيَ ٱلشَّيۡطَٰنُ بِنُصۡبٖ وَعَذَابٍ
Ka kuma tuna bawanmu Ayyuba lokacin da ya kira Ubangijinsa (yana cewa): “Lalle ni Shaixan ya shafe ni da wata wahala da azaba.”
ٱرۡكُضۡ بِرِجۡلِكَۖ هَٰذَا مُغۡتَسَلُۢ بَارِدٞ وَشَرَابٞ
(Aka ce da shi): “Ka hauri qasa da qafarka; (sai ruwa ya vuvvugo, aka ce da shi): “Wannan ruwan wanka ne mai sanyi da na sha.”
وَوَهَبۡنَا لَهُۥٓ أَهۡلَهُۥ وَمِثۡلَهُم مَّعَهُمۡ رَحۡمَةٗ مِّنَّا وَذِكۡرَىٰ لِأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ
Muka kuma yi masa baiwar iyalinsa da kuma (qarin) wasu kamarsu (na `ya`ya da jikoki) don jin qai daga gare Mu da kuma wa’azi ga masu hankula
وَخُذۡ بِيَدِكَ ضِغۡثٗا فَٱضۡرِب بِّهِۦ وَلَا تَحۡنَثۡۗ إِنَّا وَجَدۡنَٰهُ صَابِرٗاۚ نِّعۡمَ ٱلۡعَبۡدُ إِنَّهُۥٓ أَوَّابٞ
Ka xauki danqi na ciyawa da hannunka ka bugi (matarka da shi)[1], kada ka karya rantsuwarka. Lalle Mun same shi mai haquri. Madalla da wannan bawan; lalle shi mai yawan komawa ne (ga Allah)
1- Yayin da matarsa ta yi masa laifi ya yi rantsuwa cewa, idan ya warke sai ya yi mata bulala xari. Allah () ya umarce shi da ya cika rantsuwarsa ta wannan hanyar.
وَٱذۡكُرۡ عِبَٰدَنَآ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ أُوْلِي ٱلۡأَيۡدِي وَٱلۡأَبۡصَٰرِ
Ka kuma tuna bayinmu Ibrahimu da Is’haqa da Yaqubu ma’abota qarfi da basira
إِنَّآ أَخۡلَصۡنَٰهُم بِخَالِصَةٖ ذِكۡرَى ٱلدَّارِ
Lalle Mun kevance su da wata kevantacciyar xabi’a, (ita ce) tuna lahira
وَإِنَّهُمۡ عِندَنَا لَمِنَ ٱلۡمُصۡطَفَيۡنَ ٱلۡأَخۡيَارِ
Kuma lalle su a wurinmu tabbas suna daga cikin zavavvu nagari
وَٱذۡكُرۡ إِسۡمَٰعِيلَ وَٱلۡيَسَعَ وَذَا ٱلۡكِفۡلِۖ وَكُلّٞ مِّنَ ٱلۡأَخۡيَارِ
Ka kuma tuna Isma’ila da Alyasa’u da Zulkifli; dukkaninsu kuma suna cikin zavavvu
هَٰذَا ذِكۡرٞۚ وَإِنَّ لِلۡمُتَّقِينَ لَحُسۡنَ مَـَٔابٖ
Wannan kyakkyawan ambato ne (a gare su). Kuma lalle masu taqawa tabbas suna da kyakkyawar makoma
جَنَّـٰتِ عَدۡنٖ مُّفَتَّحَةٗ لَّهُمُ ٱلۡأَبۡوَٰبُ
(Wato) gidajen Aljannar dawwama, alhali qofofi suna buxe saboda su
مُتَّكِـِٔينَ فِيهَا يَدۡعُونَ فِيهَا بِفَٰكِهَةٖ كَثِيرَةٖ وَشَرَابٖ
Suna kishingixe a cikinsu, suna kiran a kawo musu ababen marmari masu yawa da abin sha a cikinsu
۞وَعِندَهُمۡ قَٰصِرَٰتُ ٱلطَّرۡفِ أَتۡرَابٌ
Kuma a wurinsu akwai tsaraikun mata masu taqaita kallo (ga mazansu kawai)
هَٰذَا مَا تُوعَدُونَ لِيَوۡمِ ٱلۡحِسَابِ
Wannan shi ne ake yi muku alqawari da shi a ranar hisabi
إِنَّ هَٰذَا لَرِزۡقُنَا مَا لَهُۥ مِن نَّفَادٍ
Lalle wannan tabbas arzikinmu ne ba mai qarewa ba
هَٰذَاۚ وَإِنَّ لِلطَّـٰغِينَ لَشَرَّ مَـَٔابٖ
Wannan (shi ne sakamakon masu taqawa). Kuma lalle masu xagawa tabbas suna da mummunar makoma
جَهَنَّمَ يَصۡلَوۡنَهَا فَبِئۡسَ ٱلۡمِهَادُ
(Wato) Jahannama wadda za su shige ta, to wannan shimfixar zama ta munana
هَٰذَا فَلۡيَذُوقُوهُ حَمِيمٞ وَغَسَّاقٞ
Wannan (sakamako ne), sai su xanxane shi na tafasasshen ruwa da mugunya
وَءَاخَرُ مِن شَكۡلِهِۦٓ أَزۡوَٰجٌ
Da kuma wani mai kama da shi iri daban-daban
هَٰذَا فَوۡجٞ مُّقۡتَحِمٞ مَّعَكُمۡ لَا مَرۡحَبَۢا بِهِمۡۚ إِنَّهُمۡ صَالُواْ ٱلنَّارِ
(Za a ce da su): “Wannan ma wani gungun ne (na mabiya) mai afkawa tare da ku;” (sai shugabannin su ce): “Ba ma yin maraba da su.” Lalle (su duka) wuta za su shiga
قَالُواْ بَلۡ أَنتُمۡ لَا مَرۡحَبَۢا بِكُمۡۖ أَنتُمۡ قَدَّمۡتُمُوهُ لَنَاۖ فَبِئۡسَ ٱلۡقَرَارُ
(Mabiyan kuma sai) su ce: “A’a, ku dai ne ba ma maraba da ku; ku ne kuka kawo mana shi (wannan mummunan sakamako);” to wannan matabbata ta munana