أَلَمۡ يَرَوۡاْ كَمۡ أَهۡلَكۡنَا قَبۡلَهُم مِّنَ ٱلۡقُرُونِ أَنَّهُمۡ إِلَيۡهِمۡ لَا يَرۡجِعُونَ
Shin ba sa gani ne, al’ummu nawa ne Muka hallaka kafin su, cewa lalle kuwa ba sa dawowa zuwa gare su?
وَإِن كُلّٞ لَّمَّا جَمِيعٞ لَّدَيۡنَا مُحۡضَرُونَ
Kuma duk gaba xayansu wurinmu za a tattara su
وَءَايَةٞ لَّهُمُ ٱلۡأَرۡضُ ٱلۡمَيۡتَةُ أَحۡيَيۡنَٰهَا وَأَخۡرَجۡنَا مِنۡهَا حَبّٗا فَمِنۡهُ يَأۡكُلُونَ
Kuma wata aya ce a gare su (ganin) matacciyar qasar da Muka raya ta Muka fitar da qwaya daga gare ta, wadda kuma ita ce suke ci
وَجَعَلۡنَا فِيهَا جَنَّـٰتٖ مِّن نَّخِيلٖ وَأَعۡنَٰبٖ وَفَجَّرۡنَا فِيهَا مِنَ ٱلۡعُيُونِ
Muka kuma sanya gonaki na dabinai da na inabai a cikinta (qasar), Muka kuma vuvvugo da idanuwan ruwa daga gare ta
لِيَأۡكُلُواْ مِن ثَمَرِهِۦ وَمَا عَمِلَتۡهُ أَيۡدِيهِمۡۚ أَفَلَا يَشۡكُرُونَ
Don su ci daga ‘ya’yan (itacenta) da kuma abin da hannanyensu suka aikata. Me ya sa ba za su riqa godiya ba?
سُبۡحَٰنَ ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلۡأَزۡوَٰجَ كُلَّهَا مِمَّا تُنۢبِتُ ٱلۡأَرۡضُ وَمِنۡ أَنفُسِهِمۡ وَمِمَّا لَا يَعۡلَمُونَ
Tsarki ya tabbata ga wanda Ya halicci dangogin komai na maza da mata daga abin da qasa take tsirowa, kuma daga su kansu, da ma daga abin da ba su sani ba
وَءَايَةٞ لَّهُمُ ٱلَّيۡلُ نَسۡلَخُ مِنۡهُ ٱلنَّهَارَ فَإِذَا هُم مُّظۡلِمُونَ
Dare ma aya ne a gare su, wanda Muka savule yini daga gare shi[1], sai ga su cikin duhu
1- Watau Allah () yana gusar da rana daga dare sai kawai mutane su gan su cikin duhu.
وَٱلشَّمۡسُ تَجۡرِي لِمُسۡتَقَرّٖ لَّهَاۚ ذَٰلِكَ تَقۡدِيرُ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡعَلِيمِ
Rana kuma tana gudu zuwa wurin da aka iyakance mata. Wannan tsari ne na (Allah) Mabuwayi, Masani
وَٱلۡقَمَرَ قَدَّرۡنَٰهُ مَنَازِلَ حَتَّىٰ عَادَ كَٱلۡعُرۡجُونِ ٱلۡقَدِيمِ
Wata kuma Mun qaddara masa masaukai, har ya koma kamar tsohuwar zarbar dabino
لَا ٱلشَّمۡسُ يَنۢبَغِي لَهَآ أَن تُدۡرِكَ ٱلۡقَمَرَ وَلَا ٱلَّيۡلُ سَابِقُ ٱلنَّهَارِۚ وَكُلّٞ فِي فَلَكٖ يَسۡبَحُونَ
Ba zai yiwu rana ta riski wata ba, dare kuma ba zai riga yini ba. Kowanne kuwa yana iyo ne a cikin falaki
وَءَايَةٞ لَّهُمۡ أَنَّا حَمَلۡنَا ذُرِّيَّتَهُمۡ فِي ٱلۡفُلۡكِ ٱلۡمَشۡحُونِ
Kuma wata aya ce a gare su cewa Mu Muka xauki iyayensu a cikin jirgin ruwa wanda aka maqare[1]
1- Watau wanda Allah ya tserar da zuriyar Annabi Adamu () a cikinsa a zamanin Annabi Nuhu () bayan varkewar ruwan Xufana.
وَخَلَقۡنَا لَهُم مِّن مِّثۡلِهِۦ مَا يَرۡكَبُونَ
Muka kuma halitta musu abin da suke hawa kwatankwacinsa
وَإِن نَّشَأۡ نُغۡرِقۡهُمۡ فَلَا صَرِيخَ لَهُمۡ وَلَا هُمۡ يُنقَذُونَ
Idan kuwa da Mun ga dama, sai Mu nutsar da su, don haka babu wani mai taimakon su, ba kuma za a kuvutar da su ba
إِلَّا رَحۡمَةٗ مِّنَّا وَمَتَٰعًا إِلَىٰ حِينٖ
Sai dai rahama daga gare Mu da kuma jin daxi zuwa wani lokaci
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱتَّقُواْ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيكُمۡ وَمَا خَلۡفَكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ
Idan kuwa aka ce da su: “Ku kiyayi abin da yake gabanku da abin da yake bayanku[1], don a ji qan ku”, (sai su bijire)
1- Watau ranar lahira da suke fuskanta da abubuwan ban tsoron cikinta, da kuma duniya wadda suke ba ta baya.
وَمَا تَأۡتِيهِم مِّنۡ ءَايَةٖ مِّنۡ ءَايَٰتِ رَبِّهِمۡ إِلَّا كَانُواْ عَنۡهَا مُعۡرِضِينَ
Babu wata aya daga ayoyin Ubangijinsu da za ta zo musu sai sun kasance masu bijire mata
وَإِذَا قِيلَ لَهُمۡ أَنفِقُواْ مِمَّا رَزَقَكُمُ ٱللَّهُ قَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَنُطۡعِمُ مَن لَّوۡ يَشَآءُ ٱللَّهُ أَطۡعَمَهُۥٓ إِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ
Idan kuma aka ce da su: “Ku ciyar daga abin da Allah Ya arzuta ku,” sai waxanda suka kafirta su ce wa waxanda suka yi imani: “Yanzu ma ciyar da wanda, da Allah Ya ga dama da ya ciyar da shi? Ba abin da kuke ciki in ban da vata mabayyani.”
وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلۡوَعۡدُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Suna kuma cewa: “Yaushe ne wannan alqawarin, idan kun kasance masu gaskiya?”
مَا يَنظُرُونَ إِلَّا صَيۡحَةٗ وَٰحِدَةٗ تَأۡخُذُهُمۡ وَهُمۡ يَخِصِّمُونَ
Ba abin da suke sauraro sai tsawa guda xaya da za ta far musu, a yayin da suke cikin hayaniyar rayuwa
فَلَا يَسۡتَطِيعُونَ تَوۡصِيَةٗ وَلَآ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِمۡ يَرۡجِعُونَ
Don haka ba za su sami damar yin wata wasiyya ba, kuma ba za su iya koma wa wajen iyalinsu ba
وَنُفِخَ فِي ٱلصُّورِ فَإِذَا هُم مِّنَ ٱلۡأَجۡدَاثِ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ يَنسِلُونَ
Aka kuma busa qaho[1], sai ga su suna fitowa daga qaburbura zuwa wurin Ubangijinsu
1- Watau busa ta biyu domin tashi.
قَالُواْ يَٰوَيۡلَنَا مَنۢ بَعَثَنَا مِن مَّرۡقَدِنَاۜۗ هَٰذَا مَا وَعَدَ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَصَدَقَ ٱلۡمُرۡسَلُونَ
Suka ce: “Kaiconmu, wane ne ya tashe mu daga makwancinmu?” (Sai a ce da su): “Ai wannnan shi ne abin da (Allah) Mai rahama Ya yi alqawarinsa, manzanni kuma sun yi gaskiya.”
إِن كَانَتۡ إِلَّا صَيۡحَةٗ وَٰحِدَةٗ فَإِذَا هُمۡ جَمِيعٞ لَّدَيۡنَا مُحۡضَرُونَ
Ba abin da zai kasance sai tsawa guda xaya, sai ga su gaba xaya an tattaro su gabanmu
فَٱلۡيَوۡمَ لَا تُظۡلَمُ نَفۡسٞ شَيۡـٔٗا وَلَا تُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
To a yau fa ba za a zalunci wani rai da komai ba, ba kuma za a saka muku ba sai da irin abin da kuka zamanto kuna aikatawa
إِنَّ أَصۡحَٰبَ ٱلۡجَنَّةِ ٱلۡيَوۡمَ فِي شُغُلٖ فَٰكِهُونَ
Lalle ‘yan Aljanna a yau suna cikin shagali, suna masu farin ciki
هُمۡ وَأَزۡوَٰجُهُمۡ فِي ظِلَٰلٍ عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِ مُتَّكِـُٔونَ
Su da matansu suna cikin inuwoyi kishingixe a kan gadaje
لَهُمۡ فِيهَا فَٰكِهَةٞ وَلَهُم مَّا يَدَّعُونَ
Suna da kayan marmari a cikinta, suna kuma da duk irin abin da suke nema
سَلَٰمٞ قَوۡلٗا مِّن رَّبّٖ رَّحِيمٖ
Sallama (za a riqa yi musu), magana ce daga Ubangiji Mai rahama
وَٱمۡتَٰزُواْ ٱلۡيَوۡمَ أَيُّهَا ٱلۡمُجۡرِمُونَ
Kuma (za a ce): “Ku ware a yau, ya ku waxannan masu manyan laifuka.”
۞أَلَمۡ أَعۡهَدۡ إِلَيۡكُمۡ يَٰبَنِيٓ ءَادَمَ أَن لَّا تَعۡبُدُواْ ٱلشَّيۡطَٰنَۖ إِنَّهُۥ لَكُمۡ عَدُوّٞ مُّبِينٞ
Yanzu ban umarce ku ba, ya ku ‘yan’adam, da cewa kada ku bauta wa Shaixan; lalle shi maqiyi ne mai bayyana (qiyayya)?