Surah: Suratu Luqman

Ayah : 31

أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱلۡفُلۡكَ تَجۡرِي فِي ٱلۡبَحۡرِ بِنِعۡمَتِ ٱللَّهِ لِيُرِيَكُم مِّنۡ ءَايَٰتِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّكُلِّ صَبَّارٖ شَكُورٖ

Ba ka gani cewa jiragen ruwa suna tafiya a cikin kogi da ni’imar Allah, don Ya nuna muku (wasu) daga ayoyinsa? Lalle a game da wannan akwai ayoyi ga duk mai yawan haquri, mai yawan godiya



Surah: Suratu Luqman

Ayah : 32

وَإِذَا غَشِيَهُم مَّوۡجٞ كَٱلظُّلَلِ دَعَوُاْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ فَلَمَّا نَجَّىٰهُمۡ إِلَى ٱلۡبَرِّ فَمِنۡهُم مُّقۡتَصِدٞۚ وَمَا يَجۡحَدُ بِـَٔايَٰتِنَآ إِلَّا كُلُّ خَتَّارٖ كَفُورٖ

Idan kuwa wata igiyar ruwa kamar duwatsu ta kere su, sai su roqi Allah suna tsantsanta addini a gare Shi, to kuma idan Ya tserar da su zuwa gaci, to akan sami tsaka-tsaki daga cikinsu. Kuma babu mai yin jayayya da ayoyinmu sai duk wani mayaudari, mai butulci



Surah: Suratu Luqman

Ayah : 33

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱتَّقُواْ رَبَّكُمۡ وَٱخۡشَوۡاْ يَوۡمٗا لَّا يَجۡزِي وَالِدٌ عَن وَلَدِهِۦ وَلَا مَوۡلُودٌ هُوَ جَازٍ عَن وَالِدِهِۦ شَيۡـًٔاۚ إِنَّ وَعۡدَ ٱللَّهِ حَقّٞۖ فَلَا تَغُرَّنَّكُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا وَلَا يَغُرَّنَّكُم بِٱللَّهِ ٱلۡغَرُورُ

Ya ku mutane, ku kiyaye dokokin Ubangijinku, kuma ku ji tsoron ranar da mahaifi ba zai amfana wa xansa komai ba, kuma xan shi ma ba zai amfana wa mahaifinsa komai ba. Lalle alqawarin Allah gaskiya ne; to kada rayuwar duniya ta ruxe ku, kuma (Shaixan) mai ruxarwa kada ya ruxe ku game da Allah



Surah: Suratu Luqman

Ayah : 34

إِنَّ ٱللَّهَ عِندَهُۥ عِلۡمُ ٱلسَّاعَةِ وَيُنَزِّلُ ٱلۡغَيۡثَ وَيَعۡلَمُ مَا فِي ٱلۡأَرۡحَامِۖ وَمَا تَدۡرِي نَفۡسٞ مَّاذَا تَكۡسِبُ غَدٗاۖ وَمَا تَدۡرِي نَفۡسُۢ بِأَيِّ أَرۡضٖ تَمُوتُۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ خَبِيرُۢ

Lalle Allah a wurinsa ne (kaxai) sanin lokacin tashin alqiyama yake, kuma (Shi) Yake saukar da ruwa, (Shi) kuma Yake sane da abin da yake cikin mahaifa[1]; ba kuwa wani rai da yake sane da abin da zai aikata gobe, ba kuma wani rai da yake sane da qasar da zai mutu. Lalle Allah Shi ne Masani, Mai cikakken ilimi


1- Watau ya san komai na halittarsa, tun daga lokacin shigarsa mahaifa har zuwa makomarsa ta qarshe.