Surah: Suratun Nur

Ayah : 31

وَقُل لِّلۡمُؤۡمِنَٰتِ يَغۡضُضۡنَ مِنۡ أَبۡصَٰرِهِنَّ وَيَحۡفَظۡنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبۡدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنۡهَاۖ وَلۡيَضۡرِبۡنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَىٰ جُيُوبِهِنَّۖ وَلَا يُبۡدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا لِبُعُولَتِهِنَّ أَوۡ ءَابَآئِهِنَّ أَوۡ ءَابَآءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوۡ أَبۡنَآئِهِنَّ أَوۡ أَبۡنَآءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوۡ إِخۡوَٰنِهِنَّ أَوۡ بَنِيٓ إِخۡوَٰنِهِنَّ أَوۡ بَنِيٓ أَخَوَٰتِهِنَّ أَوۡ نِسَآئِهِنَّ أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُنَّ أَوِ ٱلتَّـٰبِعِينَ غَيۡرِ أُوْلِي ٱلۡإِرۡبَةِ مِنَ ٱلرِّجَالِ أَوِ ٱلطِّفۡلِ ٱلَّذِينَ لَمۡ يَظۡهَرُواْ عَلَىٰ عَوۡرَٰتِ ٱلنِّسَآءِۖ وَلَا يَضۡرِبۡنَ بِأَرۡجُلِهِنَّ لِيُعۡلَمَ مَا يُخۡفِينَ مِن زِينَتِهِنَّۚ وَتُوبُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ

Kuma ka ce da muminai mata su kame idanuwansu[1] kuma su kiyaye farjinsu, kada kuma su fito da adonsu sai dai abin da ya bayyana daga gare shi[2]; kuma su sanya lulluvinsu a kan wuyan rigunansu[3]; kada kuma su fitar da adonsu sai ga mazajensu ko iyayensu ko iyayen mazajensu ko ‘ya’yansu ko ‘ya’yayen mazajensu ko ‘yan’uwansu maza ko kuma ‘ya’yan ‘yan’uwansu maza ko ‘ya’yan ‘yan’uwansu mata ko kuma mata ‘yan’uwansu ko kuma bayinsu ko kuma mazaje masu bin su (don neman abinci) ba kuma masu buqatar mata ba[4], ko kuma qananan yara waxanda ba su san sha’awar al’aurar mata ba; kada kuma su buga qafafuwansu don a gane abin da suka voye na adon qafafunsu (watau mundaye). Kuma ku tuba ga Allah gaba xayanku ya ku waxannan muminai don ku rabauta


1- Watau su kawar da idanuwansu daga kallon abin da bai halatta su kalla ba.


2- Watau abin da ba za a iya voye shi ba, kamar tufafi.


3- Watau domin a daina ganin gashinsu da wuyansu da adonsu na wuya.


4- Watau tsofaffi tukub waxanda sun daina sha’awar mata gaba xaya.


Surah: Suratun Nur

Ayah : 32

وَأَنكِحُواْ ٱلۡأَيَٰمَىٰ مِنكُمۡ وَٱلصَّـٰلِحِينَ مِنۡ عِبَادِكُمۡ وَإِمَآئِكُمۡۚ إِن يَكُونُواْ فُقَرَآءَ يُغۡنِهِمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦۗ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٞ

Kuma ku aurar da marasa aure daga cikinku da kuma na gari daga bayinku da kuyanginku. Idan sun zamanto matalauta to Allah zai wadata su daga falalarsa. Allah kuwa Mai yalwa ne, Masani



Surah: Suratun Nur

Ayah : 33

وَلۡيَسۡتَعۡفِفِ ٱلَّذِينَ لَا يَجِدُونَ نِكَاحًا حَتَّىٰ يُغۡنِيَهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦۗ وَٱلَّذِينَ يَبۡتَغُونَ ٱلۡكِتَٰبَ مِمَّا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡ فَكَاتِبُوهُمۡ إِنۡ عَلِمۡتُمۡ فِيهِمۡ خَيۡرٗاۖ وَءَاتُوهُم مِّن مَّالِ ٱللَّهِ ٱلَّذِيٓ ءَاتَىٰكُمۡۚ وَلَا تُكۡرِهُواْ فَتَيَٰتِكُمۡ عَلَى ٱلۡبِغَآءِ إِنۡ أَرَدۡنَ تَحَصُّنٗا لِّتَبۡتَغُواْ عَرَضَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَمَن يُكۡرِههُّنَّ فَإِنَّ ٱللَّهَ مِنۢ بَعۡدِ إِكۡرَٰهِهِنَّ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Waxanda kuma ba su sami wadatar yin aure ba su kame kansu har Allah Ya wadata su daga falalarsa. Waxanda kuwa suke neman fansar kansu daga bayinku[1], sai ku ba su damar fansar kansu, idan kun san suna da halin iya biya; kuma ku ba su wani abu daga dukiyar Allah da Ya ba ku. Kada kuma ku tilasta wa kuyanginku ‘yan mata a kan yin zina idan sun nemi kame kai, don ku nemi amfanin rayuwar duniya. Wanda duk kuwa ya tilasta su, to lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai bayan tilastawar da aka yi musu


1- Watau ta hanyar biyan wani kuxi da za a yanka musu idan sun biya sun zama ‘yantattun ‘ya’ya.


Surah: Suratun Nur

Ayah : 34

وَلَقَدۡ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكُمۡ ءَايَٰتٖ مُّبَيِّنَٰتٖ وَمَثَلٗا مِّنَ ٱلَّذِينَ خَلَوۡاْ مِن قَبۡلِكُمۡ وَمَوۡعِظَةٗ لِّلۡمُتَّقِينَ

Haqiqa kuma Mun saukar muku da ayoyi mabayyana da kuma izina daga waxanda suka wuce gabaninku, kuma da gargaxi ga masu taqawa



Surah: Suratun Nur

Ayah : 35

۞ٱللَّهُ نُورُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ مَثَلُ نُورِهِۦ كَمِشۡكَوٰةٖ فِيهَا مِصۡبَاحٌۖ ٱلۡمِصۡبَاحُ فِي زُجَاجَةٍۖ ٱلزُّجَاجَةُ كَأَنَّهَا كَوۡكَبٞ دُرِّيّٞ يُوقَدُ مِن شَجَرَةٖ مُّبَٰرَكَةٖ زَيۡتُونَةٖ لَّا شَرۡقِيَّةٖ وَلَا غَرۡبِيَّةٖ يَكَادُ زَيۡتُهَا يُضِيٓءُ وَلَوۡ لَمۡ تَمۡسَسۡهُ نَارٞۚ نُّورٌ عَلَىٰ نُورٖۚ يَهۡدِي ٱللَّهُ لِنُورِهِۦ مَن يَشَآءُۚ وَيَضۡرِبُ ٱللَّهُ ٱلۡأَمۡثَٰلَ لِلنَّاسِۗ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ

Allah ne hasken sammai da qasa[1]. Misalin haskensa tamkar alkuki ne da fitila take a cikinsa; fitilar kuma tana cikin qarau; qaran kuma tamkar tauraro ne na lu’ulu’u, ana kunna ta da man bishiya mai albarka ta zaitun, ita ba daga mahudar rana take ba kuma ba daga mafaxarta ba, kuma manta kamar zai kama da kansa ko da wuta ba ta tava shi ba. Haske kan haske. Allah Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga haskensa. Kuma Allah yana buga misalai ne ga mutane. Allah kuwa Masanin komai ne


1- Kuma shi ne mai haskaka zukatan muminai mai shiryar da su.


Surah: Suratun Nur

Ayah : 36

فِي بُيُوتٍ أَذِنَ ٱللَّهُ أَن تُرۡفَعَ وَيُذۡكَرَ فِيهَا ٱسۡمُهُۥ يُسَبِّحُ لَهُۥ فِيهَا بِٱلۡغُدُوِّ وَٱلۡأٓصَالِ

(Hasken) yana cikin wasu xakuna (watau masallatai) waxanda Allah Ya yi umarni a xaukaka, a kuma ambaci sunansa a cikinsu. (Wasu mazaje) suna tasbihi gare Shi a cikinsu safe da yamma



Surah: Suratun Nur

Ayah : 37

رِجَالٞ لَّا تُلۡهِيهِمۡ تِجَٰرَةٞ وَلَا بَيۡعٌ عَن ذِكۡرِ ٱللَّهِ وَإِقَامِ ٱلصَّلَوٰةِ وَإِيتَآءِ ٱلزَّكَوٰةِ يَخَافُونَ يَوۡمٗا تَتَقَلَّبُ فِيهِ ٱلۡقُلُوبُ وَٱلۡأَبۡصَٰرُ

Wasu mazaje ne waxanda kasuwanci da saye da sayarwa ba ya shagaltar da su daga ambaton Allah da kuma tsai da salla da ba da zakka, suna jin tsoron ranar da zukata da idanuwa suke raurawa



Surah: Suratun Nur

Ayah : 38

لِيَجۡزِيَهُمُ ٱللَّهُ أَحۡسَنَ مَا عَمِلُواْ وَيَزِيدَهُم مِّن فَضۡلِهِۦۗ وَٱللَّهُ يَرۡزُقُ مَن يَشَآءُ بِغَيۡرِ حِسَابٖ

(Suna haka ne) don Allah Ya saka musu da mafi kyan abin da suka aikata, kuma Ya qara musu daga falalarsa. Allah kuwa Yana arzuta wanda Ya ga dama ba da iyaka ba



Surah: Suratun Nur

Ayah : 39

وَٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَعۡمَٰلُهُمۡ كَسَرَابِۭ بِقِيعَةٖ يَحۡسَبُهُ ٱلظَّمۡـَٔانُ مَآءً حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَهُۥ لَمۡ يَجِدۡهُ شَيۡـٔٗا وَوَجَدَ ٱللَّهَ عِندَهُۥ فَوَفَّىٰهُ حِسَابَهُۥۗ وَٱللَّهُ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

Waxanda kuwa suka kafirta ayyukansu kamar kawalwalniya ne a wani faqo wanda mai jin tsananin qishirwa yake zaton ruwa ne, har lokacin da ya zo gare ta ba zai samu komai ba sai ya sami Allah a wurinsa, sai Ya cika masa hisabinsa. Allah kuwa Mai saurin hisabi ne



Surah: Suratun Nur

Ayah : 40

أَوۡ كَظُلُمَٰتٖ فِي بَحۡرٖ لُّجِّيّٖ يَغۡشَىٰهُ مَوۡجٞ مِّن فَوۡقِهِۦ مَوۡجٞ مِّن فَوۡقِهِۦ سَحَابٞۚ ظُلُمَٰتُۢ بَعۡضُهَا فَوۡقَ بَعۡضٍ إِذَآ أَخۡرَجَ يَدَهُۥ لَمۡ يَكَدۡ يَرَىٰهَاۗ وَمَن لَّمۡ يَجۡعَلِ ٱللَّهُ لَهُۥ نُورٗا فَمَا لَهُۥ مِن نُّورٍ

Ko kuma kamar duffai a cikin kogi mai zurfi da raqumin ruwa ya lulluve shi, daga samansa kuma akwai wani raqumin ruwan, daga samansa (kuma) akwai wani hadari. Duffai wasu a kan wasu; idan ya fito da hannunsa ba zai iya ganin sa ba. Wanda kuma Allah bai sanya wa haske ba, to ba shi da wani haske



Surah: Suratun Nur

Ayah : 41

أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ يُسَبِّحُ لَهُۥ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱلطَّيۡرُ صَـٰٓفَّـٰتٖۖ كُلّٞ قَدۡ عَلِمَ صَلَاتَهُۥ وَتَسۡبِيحَهُۥۗ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِمَا يَفۡعَلُونَ

Ba ka gani cewa Allah duk abin da yake sammai da qasa yana tasbihi ne gare Shi, haka tsuntsaye kuma sun buxe fukafukansu sun yi sahu, kowanne xayansu ya san sallarsa da tasbihinsa? Allah kuwa Masanin abin da suke aikatawa ne



Surah: Suratun Nur

Ayah : 42

وَلِلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَإِلَى ٱللَّهِ ٱلۡمَصِيرُ

Kuma mulkin sammai da qasa na Allah ne; makoma kuma zuwa ga Allah take



Surah: Suratun Nur

Ayah : 43

أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ يُزۡجِي سَحَابٗا ثُمَّ يُؤَلِّفُ بَيۡنَهُۥ ثُمَّ يَجۡعَلُهُۥ رُكَامٗا فَتَرَى ٱلۡوَدۡقَ يَخۡرُجُ مِنۡ خِلَٰلِهِۦ وَيُنَزِّلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مِن جِبَالٖ فِيهَا مِنۢ بَرَدٖ فَيُصِيبُ بِهِۦ مَن يَشَآءُ وَيَصۡرِفُهُۥ عَن مَّن يَشَآءُۖ يَكَادُ سَنَا بَرۡقِهِۦ يَذۡهَبُ بِٱلۡأَبۡصَٰرِ

Shin ba ka gani cewa Allah Yana kora gizagizai sannan Ya harhaxa tsakaninsu sannan Ya mai da su masu hawan juna, sai ka ga ruwan sama yana fitowa ta tsakankaninsa, kuma Yana saukar da wasu kasake (na gizagizai) daga sama waxanda a cikinsu akwai qanqara, sai Ya sami wanda Ya ga dama da ita (qanqarar) Ya kuma kautar da ita daga wanda Ya ga dama. Hasken walqiyarsa yana kusa da ya fauce idanu



Surah: Suratun Nur

Ayah : 44

يُقَلِّبُ ٱللَّهُ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبۡرَةٗ لِّأُوْلِي ٱلۡأَبۡصَٰرِ

Allah Yana jujjuya dare da yini. Lalle game da wannan tabbas akwai izina ga ma’abota hankula



Surah: Suratun Nur

Ayah : 45

وَٱللَّهُ خَلَقَ كُلَّ دَآبَّةٖ مِّن مَّآءٖۖ فَمِنۡهُم مَّن يَمۡشِي عَلَىٰ بَطۡنِهِۦ وَمِنۡهُم مَّن يَمۡشِي عَلَىٰ رِجۡلَيۡنِ وَمِنۡهُم مَّن يَمۡشِي عَلَىٰٓ أَرۡبَعٖۚ يَخۡلُقُ ٱللَّهُ مَا يَشَآءُۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Kuma Allah Ya halicci kowace dabba daga ruwa; sannan daga cikinsu akwai waxanda suke jan ciki, kuma daga cikinsu akwai waxanda suke tafiya a kan qafa biyu, akwai kuma waxanda suke tafiya a kan qafa huxu. Allah Yana halittar abin da Ya ga dama. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai



Surah: Suratun Nur

Ayah : 46

لَّقَدۡ أَنزَلۡنَآ ءَايَٰتٖ مُّبَيِّنَٰتٖۚ وَٱللَّهُ يَهۡدِي مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Haqiqa Mun saukar da ayoyi masu bayyana komai da komai. Allah kuma Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga tafarki madaidaici



Surah: Suratun Nur

Ayah : 47

وَيَقُولُونَ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ وَبِٱلرَّسُولِ وَأَطَعۡنَا ثُمَّ يَتَوَلَّىٰ فَرِيقٞ مِّنۡهُم مِّنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَۚ وَمَآ أُوْلَـٰٓئِكَ بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Kuma suna cewa: “Mun yi imani da Allah da kuma Manzo kuma mun bi,” sannan wata qungiya daga cikinsu takan ba da baya bayan wancan (imanin). Waxannan kuwa ba muminai ba ne



Surah: Suratun Nur

Ayah : 48

وَإِذَا دُعُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ لِيَحۡكُمَ بَيۡنَهُمۡ إِذَا فَرِيقٞ مِّنۡهُم مُّعۡرِضُونَ

Idan kuwa aka yi kiran su zuwa ga Allah da Manzonsa don ya yi hukunci a tsakaninsu sai ka ga wata qungiya daga cikinsu suna bijirewa



Surah: Suratun Nur

Ayah : 49

وَإِن يَكُن لَّهُمُ ٱلۡحَقُّ يَأۡتُوٓاْ إِلَيۡهِ مُذۡعِنِينَ

Idan kuwa su ne masu gaskiya sai su zo wurinsa suna masu miqa wuya



Surah: Suratun Nur

Ayah : 50

أَفِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ أَمِ ٱرۡتَابُوٓاْ أَمۡ يَخَافُونَ أَن يَحِيفَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡ وَرَسُولُهُۥۚ بَلۡ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Shin cuta ce a cikin zukatansu, ko kuwa suna tababa ne, ko kuma suna tsoron Allah da Manzonsa su zalunce su ne? A’a, waxannan su ne azzalumai



Surah: Suratun Nur

Ayah : 51

إِنَّمَا كَانَ قَوۡلَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ إِذَا دُعُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ لِيَحۡكُمَ بَيۡنَهُمۡ أَن يَقُولُواْ سَمِعۡنَا وَأَطَعۡنَاۚ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

Muminai ba su da wata magana idan aka kira su zuwa ga Allah da Manzonsa don ya yi hukunci a tsakaninsu sai faxar: “Mun ji kuma mun bi.” Waxannan kuwa su ne masu babban rabo



Surah: Suratun Nur

Ayah : 52

وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَيَخۡشَ ٱللَّهَ وَيَتَّقۡهِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَآئِزُونَ

Duk kuwa wanda ya bi Allah da Manzonsa kuma yake tsoron Allah kuma yake kiyaye dokokinsa, to waxannan su ne masu rabauta



Surah: Suratun Nur

Ayah : 53

۞وَأَقۡسَمُواْ بِٱللَّهِ جَهۡدَ أَيۡمَٰنِهِمۡ لَئِنۡ أَمَرۡتَهُمۡ لَيَخۡرُجُنَّۖ قُل لَّا تُقۡسِمُواْۖ طَاعَةٞ مَّعۡرُوفَةٌۚ إِنَّ ٱللَّهَ خَبِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ

Suka kuma rantse da Allah iya iyawarsu cewa lalle idan ka umarce su (da fita) tabbas za su fita. Ka ce (da su): “Ku daina rantse-rantse; biyayya (taku ta qarya) sananniya ce. Lalle Allah Masanin abin da kuke aikatawa ne.”



Surah: Suratun Nur

Ayah : 54

قُلۡ أَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَۖ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا عَلَيۡهِ مَا حُمِّلَ وَعَلَيۡكُم مَّا حُمِّلۡتُمۡۖ وَإِن تُطِيعُوهُ تَهۡتَدُواْۚ وَمَا عَلَى ٱلرَّسُولِ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ

Ka ce (da su): “Ku bi Allah kuma ku bi Manzo; sannan idan kuka ba da baya, to lalle nauyin abin da aka xora masa ne kawai a kansa; kuma nauyin da aka xora muku yana kanku, idan kuwa kuka bi shi za ku shiriya. Ba kuwa abin da yake kan Manzo sai isar da aike mabayyani



Surah: Suratun Nur

Ayah : 55

وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنكُمۡ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَيَسۡتَخۡلِفَنَّهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ كَمَا ٱسۡتَخۡلَفَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ وَلَيُمَكِّنَنَّ لَهُمۡ دِينَهُمُ ٱلَّذِي ٱرۡتَضَىٰ لَهُمۡ وَلَيُبَدِّلَنَّهُم مِّنۢ بَعۡدِ خَوۡفِهِمۡ أَمۡنٗاۚ يَعۡبُدُونَنِي لَا يُشۡرِكُونَ بِي شَيۡـٔٗاۚ وَمَن كَفَرَ بَعۡدَ ذَٰلِكَ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ

Allah kuwa Ya yi wa waxanda suka yi imani daga cikinku suka kuma yi aiki na gari alqawarin lalle zai sanya su halifofi a bayan qasa kamar yadda Ya sanya waxanda suke gabaninsu halifofi, kuma lalle zai tabbatar musu da addininsu wanda Ya yardar musu, tabbas kuma zai dawo musu da zaman lafiya bayan zamantowarsu cikin tsoro. Su bauta mini, ba sa yin shirkar komai da Ni. Wanda kuwa ya kafirta bayan wannan, to waxannan su ne fasiqai



Surah: Suratun Nur

Ayah : 56

وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ

Kuma ku tsai da salla ku kuma ba da zakka kuma ku bi Manzo don a ji qan ku



Surah: Suratun Nur

Ayah : 57

لَا تَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مُعۡجِزِينَ فِي ٱلۡأَرۡضِۚ وَمَأۡوَىٰهُمُ ٱلنَّارُۖ وَلَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

Kada kuma ka tsammaci waxanda suka kafirta za su gagara a bayan qasa, kuma makomarsu wuta ce; makoma kuwa ta munana



Surah: Suratun Nur

Ayah : 58

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لِيَسۡتَـٔۡذِنكُمُ ٱلَّذِينَ مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡ وَٱلَّذِينَ لَمۡ يَبۡلُغُواْ ٱلۡحُلُمَ مِنكُمۡ ثَلَٰثَ مَرَّـٰتٖۚ مِّن قَبۡلِ صَلَوٰةِ ٱلۡفَجۡرِ وَحِينَ تَضَعُونَ ثِيَابَكُم مِّنَ ٱلظَّهِيرَةِ وَمِنۢ بَعۡدِ صَلَوٰةِ ٱلۡعِشَآءِۚ ثَلَٰثُ عَوۡرَٰتٖ لَّكُمۡۚ لَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ وَلَا عَلَيۡهِمۡ جُنَاحُۢ بَعۡدَهُنَّۚ طَوَّـٰفُونَ عَلَيۡكُم بَعۡضُكُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمُ ٱلۡأٓيَٰتِۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, bayinku da kuma waxanda ba su isa mafarki ba a cikinku (watau waxanda ba su balaga ba) su nemi izininku sau uku. Kafin sallar Asuba da sanda kuke tuve tufafinku a lokacin garjin rana da kuma bayan sallar Lisha. Lokatai ne guda uku na tsiraicinku[1]. Babu laifi a kanku ko a kansu bayansu (waxannan lokatai). Masu shige da fice ne a gare ku sashinku bisa sashi. Kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyi. Allah kuma Masani ne, Mai hikima


1- Watau lokacin da suke sanya tufafin barci ko na shan iska a gida.


Surah: Suratun Nur

Ayah : 59

وَإِذَا بَلَغَ ٱلۡأَطۡفَٰلُ مِنكُمُ ٱلۡحُلُمَ فَلۡيَسۡتَـٔۡذِنُواْ كَمَا ٱسۡتَـٔۡذَنَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمۡ ءَايَٰتِهِۦۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

Idan kuma yara daga cikinku suka isa mafarki (watau suka balaga) sai su nemi izini kamar yadda waxanda suke gabaninsu suka riqa neman izini. Kamar haka Allah Yake bayyana muku ayoyinsa. Allah kuwa Masani ne, Mai hikima



Surah: Suratun Nur

Ayah : 60

وَٱلۡقَوَٰعِدُ مِنَ ٱلنِّسَآءِ ٱلَّـٰتِي لَا يَرۡجُونَ نِكَاحٗا فَلَيۡسَ عَلَيۡهِنَّ جُنَاحٌ أَن يَضَعۡنَ ثِيَابَهُنَّ غَيۡرَ مُتَبَرِّجَٰتِۭ بِزِينَةٖۖ وَأَن يَسۡتَعۡفِفۡنَ خَيۡرٞ لَّهُنَّۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٞ

Tsofaffin mata kuwa waxanda ba sa tsammanin yin aure to babu laifi a kansu su sauke lulluvinsu, amma ba masu fitar da adonsu ba; amma kuma su yi lulluvi shi ya fi zama alheri a gare su. Allah kuwa Mai ji ne, Masani