Surah: Suratul Hajji

Ayah : 31

حُنَفَآءَ لِلَّهِ غَيۡرَ مُشۡرِكِينَ بِهِۦۚ وَمَن يُشۡرِكۡ بِٱللَّهِ فَكَأَنَّمَا خَرَّ مِنَ ٱلسَّمَآءِ فَتَخۡطَفُهُ ٱلطَّيۡرُ أَوۡ تَهۡوِي بِهِ ٱلرِّيحُ فِي مَكَانٖ سَحِيقٖ

Kuna masu kauce wa varna don Allah, ba masu haxa shi da wasu ba. Duk wanda kuwa ya haxa Allah da wani, to kamar ya faxo ne daga sama, sai tsuntsaye suka fauce shi, (suka yagalgala shi) ko kuma iska ta jefa shi cikin wani wuri mai zurfi (ta rugurguza shi)



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 32

ذَٰلِكَۖ وَمَن يُعَظِّمۡ شَعَـٰٓئِرَ ٱللَّهِ فَإِنَّهَا مِن تَقۡوَى ٱلۡقُلُوبِ

Wannan kuwa (haka yake), duk wanda ya girmama wuraren ibadar (Hajji) na Allah to lalle wannan yana daga taqawar zukata



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 33

لَكُمۡ فِيهَا مَنَٰفِعُ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمّٗى ثُمَّ مَحِلُّهَآ إِلَى ٱلۡبَيۡتِ ٱلۡعَتِيقِ

Kuna da wata moriya game da su (dabbobin)[1] har zuwa wani lokaci qayyadajje (shi ne lokacin yanka su), sannan kuma wurin yankansu zuwa ga Xaki ne ‘yantacce (wato Harami baki xayansa)


1- Watau za su amfana da su wajen hawansu da amfani da gashinsu da nononsu da sauransu.


Surah: Suratul Hajji

Ayah : 34

وَلِكُلِّ أُمَّةٖ جَعَلۡنَا مَنسَكٗا لِّيَذۡكُرُواْ ٱسۡمَ ٱللَّهِ عَلَىٰ مَا رَزَقَهُم مِّنۢ بَهِيمَةِ ٱلۡأَنۡعَٰمِۗ فَإِلَٰهُكُمۡ إِلَٰهٞ وَٰحِدٞ فَلَهُۥٓ أَسۡلِمُواْۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُخۡبِتِينَ

Kowacce al’umma kuma Mun sanya musu (irin) bautar (da za su yi) don su ambaci sunan Allah bisa abin da Ya arzuta su da shi na dabbobin ni’ima. Sannan abin bautarku abin bauta ne guda Xaya, to gare Shi kawai za ku miqa wuya. Kuma ka yi albishir ga masu qasqantar da kai



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 35

ٱلَّذِينَ إِذَا ذُكِرَ ٱللَّهُ وَجِلَتۡ قُلُوبُهُمۡ وَٱلصَّـٰبِرِينَ عَلَىٰ مَآ أَصَابَهُمۡ وَٱلۡمُقِيمِي ٱلصَّلَوٰةِ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ

(Su ne kuwa) waxanda, idan aka ambaci Allah sai zukatansu su raurawa, kuma masu haquri bisa abin da ya same su, kuma masu tsai da salla, kuma masu ciyarwa daga abin da Allah Ya arzuta su (da shi)



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 36

وَٱلۡبُدۡنَ جَعَلۡنَٰهَا لَكُم مِّن شَعَـٰٓئِرِ ٱللَّهِ لَكُمۡ فِيهَا خَيۡرٞۖ فَٱذۡكُرُواْ ٱسۡمَ ٱللَّهِ عَلَيۡهَا صَوَآفَّۖ فَإِذَا وَجَبَتۡ جُنُوبُهَا فَكُلُواْ مِنۡهَا وَأَطۡعِمُواْ ٱلۡقَانِعَ وَٱلۡمُعۡتَرَّۚ كَذَٰلِكَ سَخَّرۡنَٰهَا لَكُمۡ لَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

(Raquma) kuma masu qiba Mun sanya muku su alamomi ne na bautar Allah; kuna da amfani game da su (na rayuwarku). To sai ku ambaci sunan Allah a kansu suna tsaye a kan qafa uku (lokacin soke su). To idan ransu ya fita bayan sun faxi, sai ku ci daga gare su kuma ku ciyar da mai wadatar zuci da kuma mai bara. Kamar haka Muka hore muku su don ku yi godiya



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 37

لَن يَنَالَ ٱللَّهَ لُحُومُهَا وَلَا دِمَآؤُهَا وَلَٰكِن يَنَالُهُ ٱلتَّقۡوَىٰ مِنكُمۡۚ كَذَٰلِكَ سَخَّرَهَا لَكُمۡ لِتُكَبِّرُواْ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا هَدَىٰكُمۡۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Namansu da jininsu ba sa zuwa wajen Allah, sai dai taqawarku ce za ta isa gare Shi. Kamar haka Ya hore muku su don ku girmama Allah bisa shiryarwar da Ya yi muku (da addininsa). Kuma ka yi albishir ga masu kyautatawa



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 38

۞إِنَّ ٱللَّهَ يُدَٰفِعُ عَنِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُحِبُّ كُلَّ خَوَّانٖ كَفُورٍ

Haqiqa Allah Yana bayar da kariya ga waxanda suka yi imani. Lalle Allah ba Ya son duk mai ha’inci, butulu



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 39

أُذِنَ لِلَّذِينَ يُقَٰتَلُونَ بِأَنَّهُمۡ ظُلِمُواْۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ نَصۡرِهِمۡ لَقَدِيرٌ

An yi izini (na yin yaqi) ga waxanda ake yaqa[1] don ko lalle an zalunce su. Lalle kuma Allah Mai iko ne bisa taimakon su


1- Watau sahabban Annabi () waxanda kafirai a lokacin suke yaqar su.


Surah: Suratul Hajji

Ayah : 40

ٱلَّذِينَ أُخۡرِجُواْ مِن دِيَٰرِهِم بِغَيۡرِ حَقٍّ إِلَّآ أَن يَقُولُواْ رَبُّنَا ٱللَّهُۗ وَلَوۡلَا دَفۡعُ ٱللَّهِ ٱلنَّاسَ بَعۡضَهُم بِبَعۡضٖ لَّهُدِّمَتۡ صَوَٰمِعُ وَبِيَعٞ وَصَلَوَٰتٞ وَمَسَٰجِدُ يُذۡكَرُ فِيهَا ٱسۡمُ ٱللَّهِ كَثِيرٗاۗ وَلَيَنصُرَنَّ ٱللَّهُ مَن يَنصُرُهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَقَوِيٌّ عَزِيزٌ

(Su ne) waxanda aka fitar da su daga gidajensu ba da wani laifi ba, sai don kawai sun ce: “Allah ne Ubangijinmu”. Kuma ba don kariyar Allah ga wasu mutane ta hanyar wasu ba, to da lalle an rusa wuraren bauta (na Nasara da suka qaurace wa ‘yan’uwansu), da coci-coci da wuraren bautar Yahudawa da masallatai (na Musulmi) waxanda ake ambaton sunan Allah da yawa a cikinsu. Kuma tabbas Allah zai taimaki mai taimakon Sa. Lalle Allah Mai qarfi ne, Mabuwayi



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 41

ٱلَّذِينَ إِن مَّكَّنَّـٰهُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ أَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَمَرُواْ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَنَهَوۡاْ عَنِ ٱلۡمُنكَرِۗ وَلِلَّهِ عَٰقِبَةُ ٱلۡأُمُورِ

(Su ne) waxanda, idan Muka kafa su a bayan qasa sai su tsai da salla su kuma ba da zakka kuma su yi umarni da aikin alheri su kuma yi hani daga mummunan aiki. Qarshen al’amura kuwa na Allah ne



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 42

وَإِن يُكَذِّبُوكَ فَقَدۡ كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ وَعَادٞ وَثَمُودُ

Idan kuwa suka qaryata ka, to haqiqa mutanen Nuhu da Adawa da Samudawa sun qaryata (manzanni) kafin su



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 43

وَقَوۡمُ إِبۡرَٰهِيمَ وَقَوۡمُ لُوطٖ

Da mutanen Ibrahimu da mutanen Luxu (su ma sun qaryata)



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 44

وَأَصۡحَٰبُ مَدۡيَنَۖ وَكُذِّبَ مُوسَىٰۖ فَأَمۡلَيۡتُ لِلۡكَٰفِرِينَ ثُمَّ أَخَذۡتُهُمۡۖ فَكَيۡفَ كَانَ نَكِيرِ

Da ma mutanen Madyana (su ma sun qaryata); an kuma qaryata Musa, sai Na jinkirta wa kafurai, sannan Na kama su (da azabata); to qaqa (qarshen) kashedina (a gare su) ya kasance?



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 45

فَكَأَيِّن مِّن قَرۡيَةٍ أَهۡلَكۡنَٰهَا وَهِيَ ظَالِمَةٞ فَهِيَ خَاوِيَةٌ عَلَىٰ عُرُوشِهَا وَبِئۡرٖ مُّعَطَّلَةٖ وَقَصۡرٖ مَّشِيدٍ

Sannan alqarya nawa muka hallaka su alhalin suna azzalumai, sai ga su suna rugurguje a kan rufinsu sun zama kufai, da kuma rijiyoyin da aka watsar da amfani da su, da manya-manyan gine-gine da aka xaukaka su?



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 46

أَفَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَتَكُونَ لَهُمۡ قُلُوبٞ يَعۡقِلُونَ بِهَآ أَوۡ ءَاذَانٞ يَسۡمَعُونَ بِهَاۖ فَإِنَّهَا لَا تَعۡمَى ٱلۡأَبۡصَٰرُ وَلَٰكِن تَعۡمَى ٱلۡقُلُوبُ ٱلَّتِي فِي ٱلصُّدُورِ

Yanzu ba za su yi tafiya a bayan qasa ba don su samu zukata da za su riqa tunani da su, ko kuwa kunnuwa da za su riqa ji da su? To lalle yadda lamarin yake ba idanduna ba ne suke makancewa sai dai zukatan da suke cikin qiraza su ne suke makancewa



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 47

وَيَسۡتَعۡجِلُونَكَ بِٱلۡعَذَابِ وَلَن يُخۡلِفَ ٱللَّهُ وَعۡدَهُۥۚ وَإِنَّ يَوۡمًا عِندَ رَبِّكَ كَأَلۡفِ سَنَةٖ مِّمَّا تَعُدُّونَ

Kuma suna neman ka da gaggauto musu da azaba, Allah kuwa ba Ya sava alqawarinsa. Lalle kuma yini xaya a wurin Ubangijinka kamar shekara dubu ne daga irin waxanda kuke qirgawa



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 48

وَكَأَيِّن مِّن قَرۡيَةٍ أَمۡلَيۡتُ لَهَا وَهِيَ ظَالِمَةٞ ثُمَّ أَخَذۡتُهَا وَإِلَيَّ ٱلۡمَصِيرُ

Kuma alqaryu nawa ne Na saurara musu, alhali kuwa suna kafirai, sannan (daga baya) Na kama su? Makoma kuma zuwa gare Ni ne



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 49

قُلۡ يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ إِنَّمَآ أَنَا۠ لَكُمۡ نَذِيرٞ مُّبِينٞ

Ka ce: “Ya ku mutane, ni dai kawai mai gargarxi ne a gare ku mai bayyana (gargaxi).”



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 50

فَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَرِزۡقٞ كَرِيمٞ

To waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari, suna da gafara da kuma arziki mai girma



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 51

وَٱلَّذِينَ سَعَوۡاْ فِيٓ ءَايَٰتِنَا مُعَٰجِزِينَ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَحِيمِ

Waxanda kuwa suka yi iya qoqarinsu game da vata ayoyinmu suna ganin za su gagare Mu, to waxannan su ne ma’abota (wutar) Jahima



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 52

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا مِن قَبۡلِكَ مِن رَّسُولٖ وَلَا نَبِيٍّ إِلَّآ إِذَا تَمَنَّىٰٓ أَلۡقَى ٱلشَّيۡطَٰنُ فِيٓ أُمۡنِيَّتِهِۦ فَيَنسَخُ ٱللَّهُ مَا يُلۡقِي ٱلشَّيۡطَٰنُ ثُمَّ يُحۡكِمُ ٱللَّهُ ءَايَٰتِهِۦۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

Kuma babu wani manzo ko wani annabi[1] da Muka aiko a gabaninka face idan ya yi karatu sai Shaixan ya jefa (ruxu da wasiwasi) cikin karatunsa; sannan Allah Yakan vata abin da shi Shaixan yake jefawa, sannan Allah Ya tabbatar da ayoyinsa. Allah kuwa Masani ne Mai hikima


1- Manzo, shi ne wanda Allah () ya aika shi zuwa ga kafirai ‘yan jahiliyya. Annabi kuwa shi ne wanda ya aika shi zuwa ga mutanen da ba ‘yan jahiliyya ba, amma suna da buqatar a jaddada musu addininsu.


Surah: Suratul Hajji

Ayah : 53

لِّيَجۡعَلَ مَا يُلۡقِي ٱلشَّيۡطَٰنُ فِتۡنَةٗ لِّلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ وَٱلۡقَاسِيَةِ قُلُوبُهُمۡۗ وَإِنَّ ٱلظَّـٰلِمِينَ لَفِي شِقَاقِۭ بَعِيدٖ

(Yakan yi haka ne) don Ya sanya abin da Shaixan yake jefawa ya zama fitina ga waxanda suke da cuta a cikin zukatansu, da kuma masu qeqasassun zukata. Lalle kuma azzalumai tabbas suna cikin savani mai nisa



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 54

وَلِيَعۡلَمَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡعِلۡمَ أَنَّهُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَيُؤۡمِنُواْ بِهِۦ فَتُخۡبِتَ لَهُۥ قُلُوبُهُمۡۗ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهَادِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Don kuma waxanda aka bai wa ilimi su san cewa shi (Alqur’ani) gaskiya ne daga Ubangijinka yake, sai su yi imani da shi sai zukatansu su nutsu da shi. Kuma lalle Allah tabbas Mai shiryar da waxanda suka yi imani ne zuwa ga tafarki madaidaici



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 55

وَلَا يَزَالُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فِي مِرۡيَةٖ مِّنۡهُ حَتَّىٰ تَأۡتِيَهُمُ ٱلسَّاعَةُ بَغۡتَةً أَوۡ يَأۡتِيَهُمۡ عَذَابُ يَوۡمٍ عَقِيمٍ

Waxanda kuwa suka kafirce ba za su daina kokwanton sa ba (watau Alqur’ani) har sai alqiyama ta zo musu ba zato ba tsammani, ko kuma azabar rana bakarara[1] ta zo musu


1- Watau ranar da kafirai ba za su samu wata rahama ko wani alheri ba.


Surah: Suratul Hajji

Ayah : 56

ٱلۡمُلۡكُ يَوۡمَئِذٖ لِّلَّهِ يَحۡكُمُ بَيۡنَهُمۡۚ فَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فِي جَنَّـٰتِ ٱلنَّعِيمِ

Mulki a wannan ranar na Allah ne, zai yi hukunci a tsakaninsu. To waxanda suka yi imani suka kuma yi kyawawan ayyuka, suna cikin gidajen Aljanna na ni’ima



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 57

وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا فَأُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٞ مُّهِينٞ

Waxanda kuwa suka kafirta suka kuma qaryata ayoyinmu, to waxannan suna da azaba mai wulaqantawa



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 58

وَٱلَّذِينَ هَاجَرُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ثُمَّ قُتِلُوٓاْ أَوۡ مَاتُواْ لَيَرۡزُقَنَّهُمُ ٱللَّهُ رِزۡقًا حَسَنٗاۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَهُوَ خَيۡرُ ٱلرَّـٰزِقِينَ

Waxanda kuwa suka yi hijira saboda Allah sannan aka kashe su ko kuma suka mutu, to lalle Allah tabbas zai arzuta su da kyakkyawan arziki. Kuma lalle Allah tabbas Shi ne Fiyayyen masu arzutawa



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 59

لَيُدۡخِلَنَّهُم مُّدۡخَلٗا يَرۡضَوۡنَهُۥۚ وَإِنَّ ٱللَّهَ لَعَلِيمٌ حَلِيمٞ

Lalle tabbas Zai shigar da su wata mashiga da za su yarda da ita. Kuma lalle Allah tabbas Masani ne, Mai hakuri



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 60

۞ذَٰلِكَۖ وَمَنۡ عَاقَبَ بِمِثۡلِ مَا عُوقِبَ بِهِۦ ثُمَّ بُغِيَ عَلَيۡهِ لَيَنصُرَنَّهُ ٱللَّهُۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَعَفُوٌّ غَفُورٞ

Wannan (abu da aka ambata haka yake), duk wanda ya yi uquba da irin abin da aka yi masa uquba da shi, sannan aka daxa yi masa ta’addanci, to lalle Allah tabbas zai taimake shi. Lalle Allah tabbas Mai afuwa ne, Mai gafara