Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 31

وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَوۡلَٰدَكُمۡ خَشۡيَةَ إِمۡلَٰقٖۖ نَّحۡنُ نَرۡزُقُهُمۡ وَإِيَّاكُمۡۚ إِنَّ قَتۡلَهُمۡ كَانَ خِطۡـٔٗا كَبِيرٗا

Kada kuma ku kashe ‘ya’yayenku don tsoron talauci: Mu ne Muke arzuta su har ma da ku. Lalle kashe su kuskure ne babba



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 32

وَلَا تَقۡرَبُواْ ٱلزِّنَىٰٓۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَٰحِشَةٗ وَسَآءَ سَبِيلٗا

Kuma kada ku kusanci zina; lalle ita (zina) ta kasance mugun aiki ne, kuma hanya ce wadda ta munana



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 33

وَلَا تَقۡتُلُواْ ٱلنَّفۡسَ ٱلَّتِي حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۗ وَمَن قُتِلَ مَظۡلُومٗا فَقَدۡ جَعَلۡنَا لِوَلِيِّهِۦ سُلۡطَٰنٗا فَلَا يُسۡرِف فِّي ٱلۡقَتۡلِۖ إِنَّهُۥ كَانَ مَنصُورٗا

Kuma kada ku kashe ran da Allah Ya haramta (kashewa) sai da haqqi. Wanda aka kashe ta hanyar zalunci, to lalle Mun bai wa magajinsa dama (ta ramuwa)[1], to (amma) kada ya wuce gona da iri wajen kisa; lalle shi ya zamanto abin dafa wa baya ne


1- Watau ta hanyar shari’a.


Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 34

وَلَا تَقۡرَبُواْ مَالَ ٱلۡيَتِيمِ إِلَّا بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ أَشُدَّهُۥۚ وَأَوۡفُواْ بِٱلۡعَهۡدِۖ إِنَّ ٱلۡعَهۡدَ كَانَ مَسۡـُٔولٗا

Kuma kada ku kusanci dukiyar maraya sai dai ta (hanya) wadda take mafi kyau[1], har sai ya kawo qarfi. Kuma ku cika alqawari; lalle alqawari ya kasance abin tambaya ne (a lahira)


1- Watau ta hanyar yi masa kasuwanci da ita.


Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 35

وَأَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ إِذَا كِلۡتُمۡ وَزِنُواْ بِٱلۡقِسۡطَاسِ ٱلۡمُسۡتَقِيمِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ وَأَحۡسَنُ تَأۡوِيلٗا

Kuma ku cika mudu idan kuka yi awo, kuma ku auna nauyi da ma’auni na adalci. Wannan (shi ya fi) alheri ya kuma fi kyakkyawan qarshe



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 36

وَلَا تَقۡفُ مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٌۚ إِنَّ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡبَصَرَ وَٱلۡفُؤَادَ كُلُّ أُوْلَـٰٓئِكَ كَانَ عَنۡهُ مَسۡـُٔولٗا

Kada kuma ka dinga bibiyar abin da ba ka da ilimi a kansa. Lalle ji da gani da kuma tunani duk waxannan sun zama abin tambaya ne game da su



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 37

وَلَا تَمۡشِ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَرَحًاۖ إِنَّكَ لَن تَخۡرِقَ ٱلۡأَرۡضَ وَلَن تَبۡلُغَ ٱلۡجِبَالَ طُولٗا

Kada kuma ka yi tafiya a bayan qasa kana mai girman kai; lalle kai ba za ka tsaga qasa ba (don qasaita) kuma ba za ka kai tsawon duwatsu ba



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 38

كُلُّ ذَٰلِكَ كَانَ سَيِّئُهُۥ عِندَ رَبِّكَ مَكۡرُوهٗا

Duk waxancan abubuwa mummunansu a wurin Ubangijinka abin qi ne



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 39

ذَٰلِكَ مِمَّآ أَوۡحَىٰٓ إِلَيۡكَ رَبُّكَ مِنَ ٱلۡحِكۡمَةِۗ وَلَا تَجۡعَلۡ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَتُلۡقَىٰ فِي جَهَنَّمَ مَلُومٗا مَّدۡحُورًا

Wannan yana daga cikin abin da Ubangijinka Ya yiwo maka wahayi da shi na hikima. Kada kuma ka sanya wani abin bauta tare da Allah, sai a jefa ka a cikin Jahannama kana abin zargi, korarre (daga rahama)



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 40

أَفَأَصۡفَىٰكُمۡ رَبُّكُم بِٱلۡبَنِينَ وَٱتَّخَذَ مِنَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ إِنَٰثًاۚ إِنَّكُمۡ لَتَقُولُونَ قَوۡلًا عَظِيمٗا

Shin yanzu kuwa Ubangijinku Ya zavar muku ‘ya’ya maza ne (Shi) kuwa Ya xauki (‘ya’ya) mata daga mala’iku? Lalle ku tabbas kuna faxar babbar magana



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 41

وَلَقَدۡ صَرَّفۡنَا فِي هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانِ لِيَذَّكَّرُواْ وَمَا يَزِيدُهُمۡ إِلَّا نُفُورٗا

Haqiqa kuma Mun bayyana (hujjoji) a cikin wannan Alqur’ani don su wa’azantu, (amma) kuma ba abin da yake qara musu sai nesanta (daga gaskiya)



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 42

قُل لَّوۡ كَانَ مَعَهُۥٓ ءَالِهَةٞ كَمَا يَقُولُونَ إِذٗا لَّٱبۡتَغَوۡاْ إِلَىٰ ذِي ٱلۡعَرۡشِ سَبِيلٗا

Ka ce (da su): “Da dai akwai wasu alloli tare da shi (Allah), kamar yadda suke da’awa, to kuwa da sun nemi hanyar (yin hamayya) da Mai Al’arshi (watau Allah)[1].”


1- A wata fassarar: Da su ma sun riqa neman kusanci ne ga Allah ta hanyar yi masa xa’a da bauta masa.


Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 43

سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يَقُولُونَ عُلُوّٗا كَبِيرٗا

Tsarki ya tabbata gare Shi, kuma Ya xaukaka xaukaka mai girma game da abin da suke faxa



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 44

تُسَبِّحُ لَهُ ٱلسَّمَٰوَٰتُ ٱلسَّبۡعُ وَٱلۡأَرۡضُ وَمَن فِيهِنَّۚ وَإِن مِّن شَيۡءٍ إِلَّا يُسَبِّحُ بِحَمۡدِهِۦ وَلَٰكِن لَّا تَفۡقَهُونَ تَسۡبِيحَهُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ حَلِيمًا غَفُورٗا

Sammai bakwai da qasa da abin da yake cikinsu (duka) suna tsarkake Shi. Ba wani abu wanda ba ya tasbihi tare da gode masa, sai dai ba kwa fahimtar tasbihinsu. Lalle Shi Ya kasance Mai yawan haquri ne, Mai yawan gafara



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 45

وَإِذَا قَرَأۡتَ ٱلۡقُرۡءَانَ جَعَلۡنَا بَيۡنَكَ وَبَيۡنَ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ حِجَابٗا مَّسۡتُورٗا

Idan ka karanta Alqur’ani Mukan sanya shamaki mai karewa tsakaninka da waxanda ba sa imani da lahira



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 46

وَجَعَلۡنَا عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ أَكِنَّةً أَن يَفۡقَهُوهُ وَفِيٓ ءَاذَانِهِمۡ وَقۡرٗاۚ وَإِذَا ذَكَرۡتَ رَبَّكَ فِي ٱلۡقُرۡءَانِ وَحۡدَهُۥ وَلَّوۡاْ عَلَىٰٓ أَدۡبَٰرِهِمۡ نُفُورٗا

Kuma Mukan sanya marufi a kan zukatansu don kada su fahimce shi (Alqur’anin); a cikin kunnuwansu kuma (Mukan sanya) wani nauyi. Idan kuma ka ambaci Ubangijinka Shi kaxai a cikin Alqur’ani sai su ba da baya suna masu bazama



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 47

نَّحۡنُ أَعۡلَمُ بِمَا يَسۡتَمِعُونَ بِهِۦٓ إِذۡ يَسۡتَمِعُونَ إِلَيۡكَ وَإِذۡ هُمۡ نَجۡوَىٰٓ إِذۡ يَقُولُ ٱلظَّـٰلِمُونَ إِن تَتَّبِعُونَ إِلَّا رَجُلٗا مَّسۡحُورًا

Mu Muka fi kowa sanin irin yadda suke sauraren sa (Alqur’ani), yayin da suke sauraren ka (kana karanta shi), da kuma sanda suke tattaunawa, yayin da azzalumai suke cewa: “Ai ba wanda kuke bi face wani sihirtaccen mutum.”



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 48

ٱنظُرۡ كَيۡفَ ضَرَبُواْ لَكَ ٱلۡأَمۡثَالَ فَضَلُّواْ فَلَا يَسۡتَطِيعُونَ سَبِيلٗا

Duba ka ga yadda suka yi ta ba ka sifofi (iri-iri)[1], sai suka vace, ba ko za su sami damar (gane) hanya ba


1- Watau ko su ce masa mawaqi ko mai sihiri ko boka ko mai tavin hankali.


Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 49

وَقَالُوٓاْ أَءِذَا كُنَّا عِظَٰمٗا وَرُفَٰتًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ خَلۡقٗا جَدِيدٗا

Kuma suka ce: “Yanzu kuwa idan muka zama qasusuwa kuma rududdugaggu, anya kuwa za a tashe mu a sabuwar halitta?”



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 50

۞قُلۡ كُونُواْ حِجَارَةً أَوۡ حَدِيدًا

Ka ce (da su): “Ku zama dutse ko qarfe!



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 51

أَوۡ خَلۡقٗا مِّمَّا يَكۡبُرُ فِي صُدُورِكُمۡۚ فَسَيَقُولُونَ مَن يُعِيدُنَاۖ قُلِ ٱلَّذِي فَطَرَكُمۡ أَوَّلَ مَرَّةٖۚ فَسَيُنۡغِضُونَ إِلَيۡكَ رُءُوسَهُمۡ وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هُوَۖ قُلۡ عَسَىٰٓ أَن يَكُونَ قَرِيبٗا

“Ko kuma duk wata halitta da take da girma a ranku (lalle za a tashe ku).” Sannan za su ce: “To wane ne zai dawo da mu?” Ka ce (da su): “Wanda ya halicce ku tun farko.” Sannan za su girgiza maka kawunansu su kuma ce: “To yaushe ne shi (wannan al’amari zai kasance)?” Ka ce (da su): “Mai yiwuwa ne ya faru ba da daxewa ba



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 52

يَوۡمَ يَدۡعُوكُمۡ فَتَسۡتَجِيبُونَ بِحَمۡدِهِۦ وَتَظُنُّونَ إِن لَّبِثۡتُمۡ إِلَّا قَلِيلٗا

“Ranar da zai kira ku sai ku amsa tare da gode masa kuma ku riqa tsammanin ba ku zauna (a bayan qasa ba) sai xan lokaci qanqani.”



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 53

وَقُل لِّعِبَادِي يَقُولُواْ ٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُۚ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ يَنزَغُ بَيۡنَهُمۡۚ إِنَّ ٱلشَّيۡطَٰنَ كَانَ لِلۡإِنسَٰنِ عَدُوّٗا مُّبِينٗا

Ka kuma ce da bayina su faxi (magana) wadda ita ce ta fi kyau. Lalle Shaixan yana vata tsakaninsu. Lalle Shaixan ya tabbata maqiyi ne mai bayyana (qiyayya) ga mutum



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 54

رَّبُّكُمۡ أَعۡلَمُ بِكُمۡۖ إِن يَشَأۡ يَرۡحَمۡكُمۡ أَوۡ إِن يَشَأۡ يُعَذِّبۡكُمۡۚ وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ عَلَيۡهِمۡ وَكِيلٗا

Ubangijinku (Shi) Ya fi sanin ku; in Ya ga dama sai Ya ji qan ku ko kuma in Ya ga dama sai Ya azabtar da ku. Ba Mu kuwa aiko ka ba don ka zama wakili a kansu



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 55

وَرَبُّكَ أَعۡلَمُ بِمَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَلَقَدۡ فَضَّلۡنَا بَعۡضَ ٱلنَّبِيِّـۧنَ عَلَىٰ بَعۡضٖۖ وَءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ زَبُورٗا

Ubangijinka kuma (Shi ne) Mafi sanin abin da yake cikin sammai da qasa. Haqiqa kuma Mun fifita wasu annabawa a kan wasu; Muka kuma bai wa Dawuda (littafin) Zabura



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 56

قُلِ ٱدۡعُواْ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُم مِّن دُونِهِۦ فَلَا يَمۡلِكُونَ كَشۡفَ ٱلضُّرِّ عَنكُمۡ وَلَا تَحۡوِيلًا

Ka ce (da su): “Ku kirawo waxanda kuka riya (cewa su ne iyayen gijinku) ba Shi ba, to ba su da ikon yaye muku cuta ko juyar da ita.”



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 57

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ يَبۡتَغُونَ إِلَىٰ رَبِّهِمُ ٱلۡوَسِيلَةَ أَيُّهُمۡ أَقۡرَبُ وَيَرۡجُونَ رَحۡمَتَهُۥ وَيَخَافُونَ عَذَابَهُۥٓۚ إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ كَانَ مَحۡذُورٗا

Waxancan da suke bauta wa[1], su ma suna neman hanya ne zuwa ga Ubangijinsu, a cikinsu wa zai fi kusanci? Suna kuma qaunar rahamarsa, kuma suna tsoron azabarsa. Lalle azabar Ubangijinka ta kasance abar tsoro ce


1- Watau kamar mala’iku ko annabawa ko salihan bayi.


Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 58

وَإِن مِّن قَرۡيَةٍ إِلَّا نَحۡنُ مُهۡلِكُوهَا قَبۡلَ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ أَوۡ مُعَذِّبُوهَا عَذَابٗا شَدِيدٗاۚ كَانَ ذَٰلِكَ فِي ٱلۡكِتَٰبِ مَسۡطُورٗا

Kuma ba wata alqarya[1] sai Mu ne masu halaka ta tun kafin ranar alqiyama, ko kuma Masu azabtar da ita azaba mai tsanani. Wannan ya tabbata a rubuce cikin Littafi[2]


1- Watau waxanda za su qaryata manzannin Allah, su riqa aikata manyan laifuka.


2- Watau litttafin Lauhul Mahfuzu.


Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 59

وَمَا مَنَعَنَآ أَن نُّرۡسِلَ بِٱلۡأٓيَٰتِ إِلَّآ أَن كَذَّبَ بِهَا ٱلۡأَوَّلُونَۚ وَءَاتَيۡنَا ثَمُودَ ٱلنَّاقَةَ مُبۡصِرَةٗ فَظَلَمُواْ بِهَاۚ وَمَا نُرۡسِلُ بِٱلۡأٓيَٰتِ إِلَّا تَخۡوِيفٗا

Kuma ba abin da ya hana Mu aiko da ayoyi sai don (al’ummu) na farko sun qaryata su; Muka kuma bai wa Samudawa taguwa (don ta zama aya) bayyananniya, sai suka butulce mata. Ba Ma kuwa aiko da ayoyi sai don tsoratarwa



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 60

وَإِذۡ قُلۡنَا لَكَ إِنَّ رَبَّكَ أَحَاطَ بِٱلنَّاسِۚ وَمَا جَعَلۡنَا ٱلرُّءۡيَا ٱلَّتِيٓ أَرَيۡنَٰكَ إِلَّا فِتۡنَةٗ لِّلنَّاسِ وَٱلشَّجَرَةَ ٱلۡمَلۡعُونَةَ فِي ٱلۡقُرۡءَانِۚ وَنُخَوِّفُهُمۡ فَمَا يَزِيدُهُمۡ إِلَّا طُغۡيَٰنٗا كَبِيرٗا

(Ka tuna) kuma lokacin da Muka ce da kai: “Lalle Ubangijinka Ya kewaye mutane (da ikonsa).” Ba Mu kuwa sanya abin da Muka nuna maka ido-da-ido ba (lokacin Mi’iraji) sai don jarraba ga mutane, da kuma la’ananniyar bishiyar nan (da aka ambata) a cikin Alqur’ani. Muna kuwa tsoratar da su ne, amma ba abin da yake qara musu sai xagawa mai girma