Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 31

وَلَوۡ أَنَّ قُرۡءَانٗا سُيِّرَتۡ بِهِ ٱلۡجِبَالُ أَوۡ قُطِّعَتۡ بِهِ ٱلۡأَرۡضُ أَوۡ كُلِّمَ بِهِ ٱلۡمَوۡتَىٰۗ بَل لِّلَّهِ ٱلۡأَمۡرُ جَمِيعًاۗ أَفَلَمۡ يَاْيۡـَٔسِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَن لَّوۡ يَشَآءُ ٱللَّهُ لَهَدَى ٱلنَّاسَ جَمِيعٗاۗ وَلَا يَزَالُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ تُصِيبُهُم بِمَا صَنَعُواْ قَارِعَةٌ أَوۡ تَحُلُّ قَرِيبٗا مِّن دَارِهِمۡ حَتَّىٰ يَأۡتِيَ وَعۡدُ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُخۡلِفُ ٱلۡمِيعَادَ

Da a ce akwai wani abin karantawa da za a gusar da duwatsu da shi, ko kuma a keta qasa da shi, ko kuma a yi magana da matattu da shi, (to da wannan Alqur’anin ne). Bari dai, dukkanin al’amari gaba xaya na Allah ne. Shin waxanda suka yi imani ba su san da cewa da Allah Ya ga dama da Ya shiryi mutane gaba xaya ba? Kafirai kuwa azaba ba za ta daina samun su ba saboda abin da suka aikata, ko kuwa ta faxo kusa da gidajensu har sai alqawarin Allah ya zo. Lalle Allah ba Ya sava alqawari



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 32

وَلَقَدِ ٱسۡتُهۡزِئَ بِرُسُلٖ مِّن قَبۡلِكَ فَأَمۡلَيۡتُ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ ثُمَّ أَخَذۡتُهُمۡۖ فَكَيۡفَ كَانَ عِقَابِ

Haqiqa an yi wa manzannin da suka gabace ka izgili, sai Na yi wa waxanda suka kafirta talala, sannan Na damqe su. To yaya uqubata ta kasance (a gare su)?



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 33

أَفَمَنۡ هُوَ قَآئِمٌ عَلَىٰ كُلِّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡۗ وَجَعَلُواْ لِلَّهِ شُرَكَآءَ قُلۡ سَمُّوهُمۡۚ أَمۡ تُنَبِّـُٔونَهُۥ بِمَا لَا يَعۡلَمُ فِي ٱلۡأَرۡضِ أَم بِظَٰهِرٖ مِّنَ ٱلۡقَوۡلِۗ بَلۡ زُيِّنَ لِلَّذِينَ كَفَرُواْ مَكۡرُهُمۡ وَصُدُّواْ عَنِ ٱلسَّبِيلِۗ وَمَن يُضۡلِلِ ٱللَّهُ فَمَا لَهُۥ مِنۡ هَادٖ

Yanzu wanda Yake tsaye a kan kula da kowane rai game da abin da ya aikata, (zai zama daidai da wanda ba haka ba?) Sun kuma sanya wa Allah abokan tarayya. Ka ce: (da su) “Ku faxa min sunayensu. Ko kuwa kuna ba Shi labarin abin da bai sani ba ne a bayan qasa, ko kuma dai kun riqe wata vatacciyar magana ce?” Bari dai; an dai qawata wa kafirai makircinsu ne kawai, aka kuma toshe musu hanyar (Allah). Wanda kuwa Allah Ya vatar to ba shi da wani mai shiryarwa



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 34

لَّهُمۡ عَذَابٞ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَلَعَذَابُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَشَقُّۖ وَمَا لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن وَاقٖ

Suna da wata azaba a rayuwar duniya; kuma lalle azabar lahira ita ta fi tsanani; ba su kuwa da wani mai kare su daga (azabar) Allah



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 35

۞مَّثَلُ ٱلۡجَنَّةِ ٱلَّتِي وُعِدَ ٱلۡمُتَّقُونَۖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ أُكُلُهَا دَآئِمٞ وَظِلُّهَاۚ تِلۡكَ عُقۡبَى ٱلَّذِينَ ٱتَّقَواْۚ وَّعُقۡبَى ٱلۡكَٰفِرِينَ ٱلنَّارُ

Misalin Aljannar nan da aka yi wa masu taqawa alqawari da ita; qoramu ne suke gudana ta qarqashinta; abincinta kuma mai dawwama ne da kuma inuwarta. Wannan shi ne makomar waxanda suka kiyaye dokokin Allah; makomar kafirai kuma ita ce wuta



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 36

وَٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَفۡرَحُونَ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَۖ وَمِنَ ٱلۡأَحۡزَابِ مَن يُنكِرُ بَعۡضَهُۥۚ قُلۡ إِنَّمَآ أُمِرۡتُ أَنۡ أَعۡبُدَ ٱللَّهَ وَلَآ أُشۡرِكَ بِهِۦٓۚ إِلَيۡهِ أَدۡعُواْ وَإِلَيۡهِ مَـَٔابِ

Waxanda kuwa Muka bai wa littafi (muminansu) suna farin ciki da abin da aka saukar maka; akwai kuma wasu daga qungiyoyi waxanda suke musun wani sashi nasa. Ka ce: “Ni dai an umarce ni ne kawai da in bauta wa Allah, kada kuma in tara wani abu da Shi. Kuma zuwa gare Shi kawai nake kira, wurinsa ne kawai kuma makomata.”



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 37

وَكَذَٰلِكَ أَنزَلۡنَٰهُ حُكۡمًا عَرَبِيّٗاۚ وَلَئِنِ ٱتَّبَعۡتَ أَهۡوَآءَهُم بَعۡدَ مَا جَآءَكَ مِنَ ٱلۡعِلۡمِ مَا لَكَ مِنَ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا وَاقٖ

Kamar haka Muka saukar da shi (Alqur’ani), ya zama hukunci, da harshen Larabci. Lalle kuma idan ka bi son ransu bayan abin da ya zo maka na ilimi, to ba ka da wani majivinci ko mai kariya daga (azabar) Allah



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 38

وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلٗا مِّن قَبۡلِكَ وَجَعَلۡنَا لَهُمۡ أَزۡوَٰجٗا وَذُرِّيَّةٗۚ وَمَا كَانَ لِرَسُولٍ أَن يَأۡتِيَ بِـَٔايَةٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۗ لِكُلِّ أَجَلٖ كِتَابٞ

Haqiqa kuma Mun aiko manzanni a gabaninka, Muka kuma ba su matan aure da zurriya. Bai kuma kamata ba ga wani annabi ya zo da wata aya (da za a neme shi da ya kawo ta) sai da izinin Allah. Kuma kowane lokaci yana nan a rubuce



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 39

يَمۡحُواْ ٱللَّهُ مَا يَشَآءُ وَيُثۡبِتُۖ وَعِندَهُۥٓ أُمُّ ٱلۡكِتَٰبِ

Allah Yana shafe abin da ya ga dama, Yana kuma tabbatar (da abin da ya ga dama); kuma a wurinsa asalin littafi yake[1]


1- Watau Lauhul Mahfuzu, littafin da Allah ya rubuta komai a cikinsa.


Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 40

وَإِن مَّا نُرِيَنَّكَ بَعۡضَ ٱلَّذِي نَعِدُهُمۡ أَوۡ نَتَوَفَّيَنَّكَ فَإِنَّمَا عَلَيۡكَ ٱلۡبَلَٰغُ وَعَلَيۡنَا ٱلۡحِسَابُ

Ko dai Mu nuna maka irin sashin abin da Muke yi musu gargaxi da aukuwarsa, ko kuma Mu karvi ranka (kafin lokacin), abin da yake kanka kawai shi ne isar da aike, Mu kuma hisabi yana a kanmu



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 41

أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّا نَأۡتِي ٱلۡأَرۡضَ نَنقُصُهَا مِنۡ أَطۡرَافِهَاۚ وَٱللَّهُ يَحۡكُمُ لَا مُعَقِّبَ لِحُكۡمِهِۦۚ وَهُوَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

Yanzu ba sa ganin cewa Muna zaike wa qasa Muna ta cinye iyakokinta[1]? Allah ne Mai yin hukunci, babu kuma mai yin gyara ga hukuncinsa. Shi ne kuma Mai saurin yin hisabi


1- Watau Musulmi suna ta samun nasara a kansu, suna ta cinye garuruwansu da yaqi.


Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 42

وَقَدۡ مَكَرَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ فَلِلَّهِ ٱلۡمَكۡرُ جَمِيعٗاۖ يَعۡلَمُ مَا تَكۡسِبُ كُلُّ نَفۡسٖۗ وَسَيَعۡلَمُ ٱلۡكُفَّـٰرُ لِمَنۡ عُقۡبَى ٱلدَّارِ

Haqiqa kuma waxanda suke gabaninsu sun qulla makirci, (sakamakon) qulle-qulle dukkaninsa ga Allah yake; Yana sane da abin da kowane rai yake aikatawa. Ba da daxewa ba kuma kafirai za su san wane ne mai kyakkyawan gidan (qarshe)



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 43

وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَسۡتَ مُرۡسَلٗاۚ قُلۡ كَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدَۢا بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡ وَمَنۡ عِندَهُۥ عِلۡمُ ٱلۡكِتَٰبِ

Kafirai kuma suna cewa: “Kai ba manzo ba ne.” Ka ce (da su): “Allah Ya isa shaida tsakanina da ku, da kuma wanda yake da ilimin Littafi[1].”


1- Watau malaman Ahlulkitabi waxanda suka musulunta suka shaida da manzancinsa, suka yi imani da shi.