Surah: Suratut Tauba

Ayah : 1

بَرَآءَةٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦٓ إِلَى ٱلَّذِينَ عَٰهَدتُّم مِّنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ

Allah da Manzonsa ba ruwansu da waxanda kuka yi alqawari da su daga cikin mushirikai[1]


1- Watau waxanda suka warware alqawarinsu.


Surah: Suratut Tauba

Ayah : 2

فَسِيحُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ أَرۡبَعَةَ أَشۡهُرٖ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّكُمۡ غَيۡرُ مُعۡجِزِي ٱللَّهِ وَأَنَّ ٱللَّهَ مُخۡزِي ٱلۡكَٰفِرِينَ

To sai ku tafi ku wala a bayan qasa tsawon wata huxu, kuma ku sani cewa ku ba za ku gagari Allah ba, kuma lalle Allah Mai wulaqanta kafirai ne



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 3

وَأَذَٰنٞ مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦٓ إِلَى ٱلنَّاسِ يَوۡمَ ٱلۡحَجِّ ٱلۡأَكۡبَرِ أَنَّ ٱللَّهَ بَرِيٓءٞ مِّنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ وَرَسُولُهُۥۚ فَإِن تُبۡتُمۡ فَهُوَ خَيۡرٞ لَّكُمۡۖ وَإِن تَوَلَّيۡتُمۡ فَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّكُمۡ غَيۡرُ مُعۡجِزِي ٱللَّهِۗ وَبَشِّرِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِعَذَابٍ أَلِيمٍ

Kuma sanarwa daga Allah da Manzonsa zuwa ga mutane ranar Babbar Salla cewa, lalle Allah da Manzonsa babu ruwansu da mushrikai[1]. Amma idan kuka tuba, to shi ya fi alheri a gare ku, idan kuma kuka ba da baya, to ku sani lalle ku fa ba za ku gagari Allah ba. Kuma ka yi albishir ga waxanda suka kafirta da azaba mai raxadi


1- A shekara ta tara bayan hijira, Annabi () ya aika Abubakar da Aliyyu () su yi shela a Makka a ranar sallar layya cewa, kada wani mushiriki ya sake zuwa hajji ko ya yi xawafi tsirara.


Surah: Suratut Tauba

Ayah : 4

إِلَّا ٱلَّذِينَ عَٰهَدتُّم مِّنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ ثُمَّ لَمۡ يَنقُصُوكُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَمۡ يُظَٰهِرُواْ عَلَيۡكُمۡ أَحَدٗا فَأَتِمُّوٓاْ إِلَيۡهِمۡ عَهۡدَهُمۡ إِلَىٰ مُدَّتِهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُتَّقِينَ

Sai fa waxannan mushrikan da kuka yi alqawari da su sannan kuma ba su rage muku wani abu ba (daga alqawarin), ba su kuma taimaka wa wani a kanku ba, to sai ku cika musu alqawarinsu har zuwa lokacinsu (da kuka ayyana). Lalle Allah Yana son masu taqawa



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 5

فَإِذَا ٱنسَلَخَ ٱلۡأَشۡهُرُ ٱلۡحُرُمُ فَٱقۡتُلُواْ ٱلۡمُشۡرِكِينَ حَيۡثُ وَجَدتُّمُوهُمۡ وَخُذُوهُمۡ وَٱحۡصُرُوهُمۡ وَٱقۡعُدُواْ لَهُمۡ كُلَّ مَرۡصَدٖۚ فَإِن تَابُواْ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوٰةَ فَخَلُّواْ سَبِيلَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

To idan watanni masu alfarma suka wuce[1] sai ku yaqi mushrikai a duk inda kuka same su, ku kuma kama su ku tsare su ku kuma toshe musu kowace hanya. To amma idan sun tuba sun kuma tsai da salla kuma sun ba da zakka, to sai ku qyale su. Lalle Allah Mai gafara ne Mai jin qai


1- Su ne watanni huxu masu alfarma, watau Zulqi’ida da Zulhijja da Al-Muharram da Rajab.


Surah: Suratut Tauba

Ayah : 6

وَإِنۡ أَحَدٞ مِّنَ ٱلۡمُشۡرِكِينَ ٱسۡتَجَارَكَ فَأَجِرۡهُ حَتَّىٰ يَسۡمَعَ كَلَٰمَ ٱللَّهِ ثُمَّ أَبۡلِغۡهُ مَأۡمَنَهُۥۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمۡ قَوۡمٞ لَّا يَعۡلَمُونَ

Kuma idan wani daga mushrikai ya nemi mafaka a wurinka to sai ka ba shi mafaka har ya samu damar jin zancen Allah, sannan ka isar da shi wurin amincewarsa. Wannan kuwa saboda lalle su mutane ne da ba sa sanin (gaskiya)



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 7

كَيۡفَ يَكُونُ لِلۡمُشۡرِكِينَ عَهۡدٌ عِندَ ٱللَّهِ وَعِندَ رَسُولِهِۦٓ إِلَّا ٱلَّذِينَ عَٰهَدتُّمۡ عِندَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۖ فَمَا ٱسۡتَقَٰمُواْ لَكُمۡ فَٱسۡتَقِيمُواْ لَهُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُتَّقِينَ

Ta yaya zai yiwu a samu wani alqawari tsakanin Allah da Manzonsa da kuma mushirikai in ban da waxanda kuka yi alqawari da su a Masallaci mai alfarma? To matuqar sun tsaya muku (bisa gaskiya) sai ku ma ku tsaya musu. Lalle Allah Yana son masu taqawa



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 8

كَيۡفَ وَإِن يَظۡهَرُواْ عَلَيۡكُمۡ لَا يَرۡقُبُواْ فِيكُمۡ إِلّٗا وَلَا ذِمَّةٗۚ يُرۡضُونَكُم بِأَفۡوَٰهِهِمۡ وَتَأۡبَىٰ قُلُوبُهُمۡ وَأَكۡثَرُهُمۡ فَٰسِقُونَ

Ta yaya?! (haka zai faru) alhali idan suka yi nasara a kanku ba za su duba wani kusanci ba balle wani alqawari game da ku? Suna yardar da ku ne da bakunansu, alhali kuwa zukatansu suna qi. Yawancinsu kuma fasiqai ne



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 9

ٱشۡتَرَوۡاْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ ثَمَنٗا قَلِيلٗا فَصَدُّواْ عَن سَبِيلِهِۦٓۚ إِنَّهُمۡ سَآءَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Sun musanya ayoyin Allah da xan kuxi qanqani, sannan suka toshe hanyarsa. Lalle su dai abin da suke aikatawa ya munana



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 10

لَا يَرۡقُبُونَ فِي مُؤۡمِنٍ إِلّٗا وَلَا ذِمَّةٗۚ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُعۡتَدُونَ

Ba sa duban wani kusanci na zumunci da wani mumini ballantana kuma wani alqawari. Waxannan kuma su ne masu qetare iyaka



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 11

فَإِن تَابُواْ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوٰةَ فَإِخۡوَٰنُكُمۡ فِي ٱلدِّينِۗ وَنُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ

To idan sun tuba, suka kuma tsayar da salla kuma suka ba da zakka, to sun zama ‘yan’uwanku a cikin addini. Muna kuwa bayanin ayoyi ne filla-filla ga mutane da suke da sani



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 12

وَإِن نَّكَثُوٓاْ أَيۡمَٰنَهُم مِّنۢ بَعۡدِ عَهۡدِهِمۡ وَطَعَنُواْ فِي دِينِكُمۡ فَقَٰتِلُوٓاْ أَئِمَّةَ ٱلۡكُفۡرِ إِنَّهُمۡ لَآ أَيۡمَٰنَ لَهُمۡ لَعَلَّهُمۡ يَنتَهُونَ

Idan kuma suka warware rantsuwarsu bayan xaukar alqawarinsu, suka kuma soki addininku, to sai ku yaqi shugabannin kafirci, don kuwa ba su da alqawari, ko yin haka zai sa su daina



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 13

أَلَا تُقَٰتِلُونَ قَوۡمٗا نَّكَثُوٓاْ أَيۡمَٰنَهُمۡ وَهَمُّواْ بِإِخۡرَاجِ ٱلرَّسُولِ وَهُم بَدَءُوكُمۡ أَوَّلَ مَرَّةٍۚ أَتَخۡشَوۡنَهُمۡۚ فَٱللَّهُ أَحَقُّ أَن تَخۡشَوۡهُ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Yanzu ba za ku yaqi mutanen da suka warware alqawarinsu ba, kuma (tun farko) sun yi nufin fitar da Manzo (daga Makka), su ne kuma suka fara far muku da yaqi? Yanzu kwa riqa tsoron su? To Allah ne Ya fi cancantar ku ji tsoron Sa idan kun kasance muminai



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 14

قَٰتِلُوهُمۡ يُعَذِّبۡهُمُ ٱللَّهُ بِأَيۡدِيكُمۡ وَيُخۡزِهِمۡ وَيَنصُرۡكُمۡ عَلَيۡهِمۡ وَيَشۡفِ صُدُورَ قَوۡمٖ مُّؤۡمِنِينَ

Ku yaqe su, Allah zai azabtar da su ta hannayenku, Ya kuma kunyatar da su, kuma Ya taimake ku a kansu, Ya kuma warkar da zukatan muminai



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 15

وَيُذۡهِبۡ غَيۡظَ قُلُوبِهِمۡۗ وَيَتُوبُ ٱللَّهُ عَلَىٰ مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ

Ya kuma tafiyar da vacin ransu. Allah kuma Ya karvi tuban duk wanda Ya ga dama. Allah kuwa Masani ne, Mai hikima



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 16

أَمۡ حَسِبۡتُمۡ أَن تُتۡرَكُواْ وَلَمَّا يَعۡلَمِ ٱللَّهُ ٱلَّذِينَ جَٰهَدُواْ مِنكُمۡ وَلَمۡ يَتَّخِذُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَا رَسُولِهِۦ وَلَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَلِيجَةٗۚ وَٱللَّهُ خَبِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ

Ko kuwa kuna tsammanin za a qyale ku ne (sakaka) alhali kuwa har yanzu Allah bai tantance waxanda suka yi jihadi ba a cikinku, ba su kuma riqi wasu masoya ba banda Allah da Manzonsa da muminai? Allah Mai cikakken sanin abin da kuke aikatawa ne



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 17

مَا كَانَ لِلۡمُشۡرِكِينَ أَن يَعۡمُرُواْ مَسَٰجِدَ ٱللَّهِ شَٰهِدِينَ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِم بِٱلۡكُفۡرِۚ أُوْلَـٰٓئِكَ حَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ وَفِي ٱلنَّارِ هُمۡ خَٰلِدُونَ

Ba zai tava yiwuwa mushrikai su raya masallatan Allah ba, alhalin kuwa suna masu iqirarin kafirci ga kawunansu. Waxannan ayyukansu sun vaci kuma a cikin wuta za su dawwama



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 18

إِنَّمَا يَعۡمُرُ مَسَٰجِدَ ٱللَّهِ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَأَقَامَ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَى ٱلزَّكَوٰةَ وَلَمۡ يَخۡشَ إِلَّا ٱللَّهَۖ فَعَسَىٰٓ أُوْلَـٰٓئِكَ أَن يَكُونُواْ مِنَ ٱلۡمُهۡتَدِينَ

Lalle mai raya masallatan Allah shi ne kawai wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira ya kuma tsayar da salla, kuma ya ba da zakka, bai kuma ji tsoron wani ba sai Allah. To waxannan tabbas suna cikin shiryayyu



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 19

۞أَجَعَلۡتُمۡ سِقَايَةَ ٱلۡحَآجِّ وَعِمَارَةَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ كَمَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَجَٰهَدَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۚ لَا يَسۡتَوُۥنَ عِندَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Yanzu kwa mayar da shayar da alhazai da raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira ya kuma yi jihadi saboda Allah? Ai ba za su zama xaya ba a wurin Allah. Allah kuma ba Ya shiryar da mutane azzalumai



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 20

ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَهَاجَرُواْ وَجَٰهَدُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡ أَعۡظَمُ دَرَجَةً عِندَ ٱللَّهِۚ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَآئِزُونَ

Waxanda suka yi imani kuma suka yi hijira suka yi jihadi saboda Allah da dukiyoyinsu da kawunansu su suka fi girman daraja a wurin Allah kuma waxannan su ne marabauta



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 21

يُبَشِّرُهُمۡ رَبُّهُم بِرَحۡمَةٖ مِّنۡهُ وَرِضۡوَٰنٖ وَجَنَّـٰتٖ لَّهُمۡ فِيهَا نَعِيمٞ مُّقِيمٌ

Ubangijinsu Yana yi musu albishir da rahama da yarda daga gare Shi, kana da gidajen Aljanna (waxanda) a cikinsu suke da ni’imomi masu xorewa



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 22

خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ عِندَهُۥٓ أَجۡرٌ عَظِيمٞ

Su madawwama ne a cikinsu har abada. Lalle lada mai girma yana wurin Allah



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 23

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّخِذُوٓاْ ءَابَآءَكُمۡ وَإِخۡوَٰنَكُمۡ أَوۡلِيَآءَ إِنِ ٱسۡتَحَبُّواْ ٱلۡكُفۡرَ عَلَى ٱلۡإِيمَٰنِۚ وَمَن يَتَوَلَّهُم مِّنكُمۡ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku xauki iyayenku da ‘yan’uwanku masoya muddin dai sun fifita kafirci a kan imani. Duk kuwa waxanda suka xauke su (masoya) daga cikinku to waxannan su ne azzalumai



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 24

قُلۡ إِن كَانَ ءَابَآؤُكُمۡ وَأَبۡنَآؤُكُمۡ وَإِخۡوَٰنُكُمۡ وَأَزۡوَٰجُكُمۡ وَعَشِيرَتُكُمۡ وَأَمۡوَٰلٌ ٱقۡتَرَفۡتُمُوهَا وَتِجَٰرَةٞ تَخۡشَوۡنَ كَسَادَهَا وَمَسَٰكِنُ تَرۡضَوۡنَهَآ أَحَبَّ إِلَيۡكُم مِّنَ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَجِهَادٖ فِي سَبِيلِهِۦ فَتَرَبَّصُواْ حَتَّىٰ يَأۡتِيَ ٱللَّهُ بِأَمۡرِهِۦۗ وَٱللَّهُ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلۡفَٰسِقِينَ

Ka ce: “Idan iyayenku da ‘ya’yanku da matanku da danginku da dukiyoyin da kuka tara da kasuwanci da kuke tsoron gurguncewarsa da kuma gidajen da kuke sha’awa; idan har su kuka fi so fiye da Allah da Manzonsa da kuma jihadi saboda Shi, to sai ku saurara har Allah Ya zo da al’amarinsa. Allah kuwa ba Ya shiryar da mutane fasiqai.”



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 25

لَقَدۡ نَصَرَكُمُ ٱللَّهُ فِي مَوَاطِنَ كَثِيرَةٖ وَيَوۡمَ حُنَيۡنٍ إِذۡ أَعۡجَبَتۡكُمۡ كَثۡرَتُكُمۡ فَلَمۡ تُغۡنِ عَنكُمۡ شَيۡـٔٗا وَضَاقَتۡ عَلَيۡكُمُ ٱلۡأَرۡضُ بِمَا رَحُبَتۡ ثُمَّ وَلَّيۡتُم مُّدۡبِرِينَ

Lalle haqiqa Allah Ya taimake ku a wurare da yawa, da kuma ranar (yaqin) Hunaini lokacin da yawanku ya ruxe ku sai (yawan naku) bai amfana muku komai ba, qasa kuma ta yi muku qunci duk da yalwarta, sannan kuka juya kuna masu ba da baya



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 26

ثُمَّ أَنزَلَ ٱللَّهُ سَكِينَتَهُۥ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ وَعَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَأَنزَلَ جُنُودٗا لَّمۡ تَرَوۡهَا وَعَذَّبَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۚ وَذَٰلِكَ جَزَآءُ ٱلۡكَٰفِرِينَ

Sannan Allah Ya sauqar wa da Manzonsa da kuma muminai nutsuwarsa, Ya kuma saukar da wasu rundunoni da ba kwa gani, Ya kuma azabtar da waxanda suka kafirta. Wannan kuwa shi ne sakamakon kafirai



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 27

ثُمَّ يَتُوبُ ٱللَّهُ مِنۢ بَعۡدِ ذَٰلِكَ عَلَىٰ مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Sannan bayan wannan Allah zai karvi tuban wanda Ya ga dama. Allah kuwa Mai gafara ne, Mai rahama



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 28

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّمَا ٱلۡمُشۡرِكُونَ نَجَسٞ فَلَا يَقۡرَبُواْ ٱلۡمَسۡجِدَ ٱلۡحَرَامَ بَعۡدَ عَامِهِمۡ هَٰذَاۚ وَإِنۡ خِفۡتُمۡ عَيۡلَةٗ فَسَوۡفَ يُغۡنِيكُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦٓ إِن شَآءَۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, lalle mushrikai najasa ne kawai, saboda haka kada su kusanci Masallaci mai alfarma bayan wannan shekarar tasu. Idan kuma kuna tsoron talauci ne to Allah zai wadata ku daga falalarsa idan Ya ga dama. Lalle Allah Masani ne, Mai hikima



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 29

قَٰتِلُواْ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَلَا بِٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَلَا يُحَرِّمُونَ مَا حَرَّمَ ٱللَّهُ وَرَسُولُهُۥ وَلَا يَدِينُونَ دِينَ ٱلۡحَقِّ مِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ حَتَّىٰ يُعۡطُواْ ٱلۡجِزۡيَةَ عَن يَدٖ وَهُمۡ صَٰغِرُونَ

Ku yaqi waxanda ba sa yin imani da Allah da ranar lahira, ba kuma sa haramta abin da Allah da Manzonsa suka haramta, kuma ba sa yin addini na gaskiya, daga waxanda aka bai wa littafi har sai (sun yarda) za su ba da jizya[1] da hannunsu a qasqance


1- Jizya, ita ce dukiyar da ake karva daga hannun Yahudu da Nasara waxanda ake zaune da su lafiya a qasar Musulmi, domin xauke mu shiga rundunar Musulmi, sannan a ba su kariya daga abokan gaba. Ba a karvar zakka daga hannunsu, wannan haqqi ne da ya shafi Musulmi kaxai.


Surah: Suratut Tauba

Ayah : 30

وَقَالَتِ ٱلۡيَهُودُ عُزَيۡرٌ ٱبۡنُ ٱللَّهِ وَقَالَتِ ٱلنَّصَٰرَى ٱلۡمَسِيحُ ٱبۡنُ ٱللَّهِۖ ذَٰلِكَ قَوۡلُهُم بِأَفۡوَٰهِهِمۡۖ يُضَٰهِـُٔونَ قَوۡلَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قَبۡلُۚ قَٰتَلَهُمُ ٱللَّهُۖ أَنَّىٰ يُؤۡفَكُونَ

Yahudawa sun ce: “Uzairu xan Allah ne.” Nasara kuma suka ce: “Almasihu xan Allah ne.” Wannan faxarsu ce kawai da bakunansu; suna kwaikwayon faxar kafiran da suka gabace su ne. Allah Ya tsine musu. Ta qaqa ake kautar da su daga gaskiya?