Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 1

وَيۡلٞ لِّلۡمُطَفِّفِينَ

Tsananin azaba ya tabbata ga masu tauye ma’auni



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 2

ٱلَّذِينَ إِذَا ٱكۡتَالُواْ عَلَى ٱلنَّاسِ يَسۡتَوۡفُونَ

Waxanda idan suka auna daga wajen mutane suna cikawa fal



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 3

وَإِذَا كَالُوهُمۡ أَو وَّزَنُوهُمۡ يُخۡسِرُونَ

Idan kuwa su za su aunar, da mudu ne ko da sikeli, to sai su tauye



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 4

أَلَا يَظُنُّ أُوْلَـٰٓئِكَ أَنَّهُم مَّبۡعُوثُونَ

Yanzu waxannan ba sa zaton cewa su lalle za a tashe su?



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 5

لِيَوۡمٍ عَظِيمٖ

A wata rana mai girma?



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 6

يَوۡمَ يَقُومُ ٱلنَّاسُ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Ranar da mutane za su tsaya gaban Ubangijin talikai?



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 7

كَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلۡفُجَّارِ لَفِي سِجِّينٖ

Tabbas, lalle littafin fajirai yana cikin Sijjinu



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 8

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا سِجِّينٞ

Me kuma ya sanar da kai me ake ce wa Sijjinu?



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 9

كِتَٰبٞ مَّرۡقُومٞ

Littafi ne rubutacce[1]


1- Watau wanda ya qunshi cikakkun ayyukan fajirai cif-cif ba daxi babu ragi.


Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 10

وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ

Tsananin azaba a wannan ranar ya tabbata ga masu qaryatawa



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 11

ٱلَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوۡمِ ٱلدِّينِ

Waxanda suke qaryata ranar sakamako



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 12

وَمَا يُكَذِّبُ بِهِۦٓ إِلَّا كُلُّ مُعۡتَدٍ أَثِيمٍ

Babu kuwa mai qaryata ta sai duk wani mai shisshigi mai yawan savo



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 13

إِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِ ءَايَٰتُنَا قَالَ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ

Idan ana karanta masa ayoyinmu sai ya ce: “Wannan tatsuniyoyi ne na mutanen farko.”



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 14

كَلَّاۖ بَلۡۜ رَانَ عَلَىٰ قُلُوبِهِم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ

A’a, abin ai ba haka ba ne; abin da suke aikatawa ne ya yi tsatsa a zukatansu



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 15

كَلَّآ إِنَّهُمۡ عَن رَّبِّهِمۡ يَوۡمَئِذٖ لَّمَحۡجُوبُونَ

Tabbas! Lalle su haqiqa ababan kangewa ne daga (ganin) Ubangijinsu[1] a wannan rana


1- Watau kafirai ba za su ga Allah ba a ranar alqiyama, kamar yadda suka kasa ganin gaskiya a nan duniya.


Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 16

ثُمَّ إِنَّهُمۡ لَصَالُواْ ٱلۡجَحِيمِ

Sannan kuma lalle su tabbas masu shiga wutar Jahimu ne



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 17

ثُمَّ يُقَالُ هَٰذَا ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ

Sannan za a ce: “Wannan ne abin da kuka kasance kuna qaryata shi.”



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 18

كَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلۡأَبۡرَارِ لَفِي عِلِّيِّينَ

Tabbas! Lalle littafin mutanen kirki haqiqa yana cikin Illiyyuna



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 19

وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا عِلِّيُّونَ

Me ya sanar da kai mene ne Iliyyuna?



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 20

كِتَٰبٞ مَّرۡقُومٞ

Wani littafi ne rubutacce[1]


1- Watau wanda aka tanada domin rubuta kyawawan ayyukan muminai cif-cif.


Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 21

يَشۡهَدُهُ ٱلۡمُقَرَّبُونَ

(Mala’iku) makusanta suke halartar sa



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 22

إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ لَفِي نَعِيمٍ

Lalle masu biyayya tabbas suna cikin ni’ima



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 23

عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ

A kan gadaje suna kallo



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 24

تَعۡرِفُ فِي وُجُوهِهِمۡ نَضۡرَةَ ٱلنَّعِيمِ

Za ka gane hasken ni’ima a fuskokinsu[1]


1- Watau fuskokinsu suna sheqi da annuri.


Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 25

يُسۡقَوۡنَ مِن رَّحِيقٖ مَّخۡتُومٍ

Ana shayar da su giyar da aka rufe (bakin mazubinta)



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 26

خِتَٰمُهُۥ مِسۡكٞۚ وَفِي ذَٰلِكَ فَلۡيَتَنَافَسِ ٱلۡمُتَنَٰفِسُونَ

(Har) qarshensa (qamshin) almiski ne. To game da wannan kuwa lalle masu gasa su yi gasa



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 27

وَمِزَاجُهُۥ مِن تَسۡنِيمٍ

Mahaxinsa kuma daga ruwan tasnimu yake



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 28

عَيۡنٗا يَشۡرَبُ بِهَا ٱلۡمُقَرَّبُونَ

Wani idon ruwa wanda bayi makusanta ne suke sha daga gare shi



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 29

إِنَّ ٱلَّذِينَ أَجۡرَمُواْ كَانُواْ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يَضۡحَكُونَ

Lalle waxanda suka yi manyan laifuka[1] sun kasance suna yi wa waxanda suka yi imani dariya (a duniya)


1- Watau kafirai.


Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 30

وَإِذَا مَرُّواْ بِهِمۡ يَتَغَامَزُونَ

Kuma idan suka wuce ta wajensu sai su riqa zunxen su