وَٱلنَّـٰزِعَٰتِ غَرۡقٗا
Na rantse da (mala’iku) masu cizgar (ran kafiri) mummunar cizga
Share :
وَٱلنَّـٰشِطَٰتِ نَشۡطٗا
Da kuma (mala’iku) masu zare (ran mumini) sassauqar zarewa
وَٱلسَّـٰبِحَٰتِ سَبۡحٗا
Da kuma (mala’iku) masu ninqaya (a sama don sauko da umarni) ninqaya mai tsananin sauri
فَٱلسَّـٰبِقَٰتِ سَبۡقٗا
Sannan da (mala’iku) masu matuqar rigegeniya (don zartar da umarnin Allah)
فَٱلۡمُدَبِّرَٰتِ أَمۡرٗا
Sannan da (mala’iku) masu tsara al’amura
يَوۡمَ تَرۡجُفُ ٱلرَّاجِفَةُ
Ranar da mai girgizawa za ta yi girgiza (watau busar qaho ta farko)
تَتۡبَعُهَا ٱلرَّادِفَةُ
Mai bin ta kuma za ta biyo ta (watau busa ta biyu)
قُلُوبٞ يَوۡمَئِذٖ وَاجِفَةٌ
Wasu zukata a wannan ranar a tsorace suke
أَبۡصَٰرُهَا خَٰشِعَةٞ
Idanuwansu kuma a qasqance suke
يَقُولُونَ أَءِنَّا لَمَرۡدُودُونَ فِي ٱلۡحَافِرَةِ
(A duniya) suna cewa: “Yanzu zai yiwu a dawo da mu a raye (bayan mutuwa)?
أَءِذَا كُنَّا عِظَٰمٗا نَّخِرَةٗ
“Yanzu ko bayan mun zama qasusuwa rududdugaggu?”
قَالُواْ تِلۡكَ إِذٗا كَرَّةٌ خَاسِرَةٞ
Suka ce: “Idan ko ya yiwu, to wannan komawa ce mai cike da asara.”
فَإِنَّمَا هِيَ زَجۡرَةٞ وَٰحِدَةٞ
To lalle ita kawai tsawa ce guda xaya tal!
فَإِذَا هُم بِٱلسَّاهِرَةِ
Sai ga su a bayan qasa[1]
1- Watau kowa da kowa ya fito da rai.
هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ مُوسَىٰٓ
Shin labarin Musa ya zo maka?
إِذۡ نَادَىٰهُ رَبُّهُۥ بِٱلۡوَادِ ٱلۡمُقَدَّسِ طُوًى
Lokacin da Ubangijinsa Ya kirawo shi a kwari mai tsarki, (watau) Xuwa?
ٱذۡهَبۡ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ
(Aka ce da shi): Ka tafi zuwa ga Fir’auna, haqiqa shi ya yi xagawa
فَقُلۡ هَل لَّكَ إِلَىٰٓ أَن تَزَكَّىٰ
Sai ka ce: “Shin zai yiwu gare ka kuwa ka tsarkaka?
وَأَهۡدِيَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخۡشَىٰ
“In kuma shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka, sai ka ji tsoron Sa?
فَأَرَىٰهُ ٱلۡأٓيَةَ ٱلۡكُبۡرَىٰ
Sai ya nuna masa babbar aya[1]
1- Watau ya nuna masa hannun mai haske kamar fitila da kuma sandarsa mai rikixa ta zama macijiya.
فَكَذَّبَ وَعَصَىٰ
Sai ya qaryata ya kuma kangare
ثُمَّ أَدۡبَرَ يَسۡعَىٰ
Sannan ya ba da baya yana ta gaggawa
فَحَشَرَ فَنَادَىٰ
Sai ya tattara (jama’arsa) sai ya yi shela
فَقَالَ أَنَا۠ رَبُّكُمُ ٱلۡأَعۡلَىٰ
Sai ya ce, “Ni ne ubangijinku mafi girma!”
فَأَخَذَهُ ٱللَّهُ نَكَالَ ٱلۡأٓخِرَةِ وَٱلۡأُولَىٰٓ
Saboda haka Allah Ya kama shi da azabar lahira (watau Jahannama) da ta duniya (watau nutse wa a ruwa)
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبۡرَةٗ لِّمَن يَخۡشَىٰٓ
Lalle a game da wannan tabbas akwai izina ga wanda yake tsoron (Allah)
ءَأَنتُمۡ أَشَدُّ خَلۡقًا أَمِ ٱلسَّمَآءُۚ بَنَىٰهَا
Yanzu ku ne halittarku ta fi tsanani ko kuwa sama wadda Shi ne Ya gina ta?
رَفَعَ سَمۡكَهَا فَسَوَّىٰهَا
Ya xaukaka rufinta Ya kuma daidaita ta[1]
1- Watau ya zama babu wata varaka ko tsagewa ko wani aibi tare da ita.
وَأَغۡطَشَ لَيۡلَهَا وَأَخۡرَجَ ضُحَىٰهَا
Ya lulluve darenta da duhu Ya kuma fitar da hasken hantsinta
وَٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ ذَٰلِكَ دَحَىٰهَآ
Qasa kuma bayan haka Ya shimfixa ta