هَلۡ أَتَىٰ عَلَى ٱلۡإِنسَٰنِ حِينٞ مِّنَ ٱلدَّهۡرِ لَمۡ يَكُن شَيۡـٔٗا مَّذۡكُورًا
Haqiqa wani yanki na zamani ya zo wa mutum yayin da bai zama wani abin ambato ba[1]
1- Watau babu shi gaba xaya, babu kuma wanda ya san shi.
إِنَّا خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِن نُّطۡفَةٍ أَمۡشَاجٖ نَّبۡتَلِيهِ فَجَعَلۡنَٰهُ سَمِيعَۢا بَصِيرًا
Lalle Mun halicci mutum daga maniyyi gamin-gambiza[1] don Mu jarrabe shi, sai Muka sanya shi mai ji mai gani
1- Watau tsakanin na namiji da na mace.
إِنَّا هَدَيۡنَٰهُ ٱلسَّبِيلَ إِمَّا شَاكِرٗا وَإِمَّا كَفُورًا
Lalle Mun bayyana masa hanya, ko dai (ya zama) mai godewa ko kuma mai butulcewa
إِنَّآ أَعۡتَدۡنَا لِلۡكَٰفِرِينَ سَلَٰسِلَاْ وَأَغۡلَٰلٗا وَسَعِيرًا
Lalle Mun tanadar wa kafirai sarqoqi da ququmai da wutar Sa’ira
إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ يَشۡرَبُونَ مِن كَأۡسٖ كَانَ مِزَاجُهَا كَافُورًا
Lalle mutane nagari suna sha daga wani kofin (giya) da mahaxinta ya kasance kafur ne[1]
1- Watau mai daxin qamshi.
عَيۡنٗا يَشۡرَبُ بِهَا عِبَادُ ٱللَّهِ يُفَجِّرُونَهَا تَفۡجِيرٗا
Wani marmaro ne da bayin Allah suke sha daga gare shi suna vuvvugo shi vuvvugowa ta haqiqa
يُوفُونَ بِٱلنَّذۡرِ وَيَخَافُونَ يَوۡمٗا كَانَ شَرُّهُۥ مُسۡتَطِيرٗا
Suna cika alqawari na bakance suna kuma tsoron ranar da sharrinta ya kasance mai bazuwa ne
وَيُطۡعِمُونَ ٱلطَّعَامَ عَلَىٰ حُبِّهِۦ مِسۡكِينٗا وَيَتِيمٗا وَأَسِيرًا
Suna kuma ciyar da abinci tare da suna son sa ga miskini da maraya da kuma ribataccen yaqi
إِنَّمَا نُطۡعِمُكُمۡ لِوَجۡهِ ٱللَّهِ لَا نُرِيدُ مِنكُمۡ جَزَآءٗ وَلَا شُكُورًا
(Suna cewa): “Mu kawai muna ciyar da ku ne saboda Allah, ba ma nufin sakamako ko godiya daga wurinka
إِنَّا نَخَافُ مِن رَّبِّنَا يَوۡمًا عَبُوسٗا قَمۡطَرِيرٗا
“Lalle mu muna jin tsoron rana mai sa xaure fuska, matsananciya daga Ubangijinmu
فَوَقَىٰهُمُ ٱللَّهُ شَرَّ ذَٰلِكَ ٱلۡيَوۡمِ وَلَقَّىٰهُمۡ نَضۡرَةٗ وَسُرُورٗا
Sai Allah Ya kare su (daga) sharrin wannan ranar Ya kuma ba su haske (a fuskokinsu) da kuma farin ciki
وَجَزَىٰهُم بِمَا صَبَرُواْ جَنَّةٗ وَحَرِيرٗا
Ya kuma saka musu da Aljanna da alharini saboda haqurin da suka yi
مُّتَّكِـِٔينَ فِيهَا عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِۖ لَا يَرَوۡنَ فِيهَا شَمۡسٗا وَلَا زَمۡهَرِيرٗا
Suna masu kishingixa a cikinta a kan gadaje; ba sa ganin rana ko jin tsananin sanyi a cikinta
وَدَانِيَةً عَلَيۡهِمۡ ظِلَٰلُهَا وَذُلِّلَتۡ قُطُوفُهَا تَذۡلِيلٗا
Inuwoyinta kuma suna kusa da su, an kuma hore musu ‘ya’yan itatuwanta matuqar horewa
وَيُطَافُ عَلَيۡهِم بِـَٔانِيَةٖ مِّن فِضَّةٖ وَأَكۡوَابٖ كَانَتۡ قَوَارِيرَا۠
Ana kuma kai-kawo a tsakaninsu da qorai na azurfa da kofuna waxanda suka kasance na qarau
قَوَارِيرَاْ مِن فِضَّةٖ قَدَّرُوهَا تَقۡدِيرٗا
Qarau xin na azurfa ne, sun auna su, aunawa daidai da buqata
وَيُسۡقَوۡنَ فِيهَا كَأۡسٗا كَانَ مِزَاجُهَا زَنجَبِيلًا
Ana kuma shayar da su wata giya a cikinta, wadda mahaxinta ya kasance citta mai yatsu ce
عَيۡنٗا فِيهَا تُسَمَّىٰ سَلۡسَبِيلٗا
Wani marmaro ne a cikinta da ake kiran sa Salsabilu
۞وَيَطُوفُ عَلَيۡهِمۡ وِلۡدَٰنٞ مُّخَلَّدُونَ إِذَا رَأَيۡتَهُمۡ حَسِبۡتَهُمۡ لُؤۡلُؤٗا مَّنثُورٗا
Samari hadimai dawwamammu (da ba sa tsufa) kuma suna kai-kawo tsakaninsu, idan ka gan su sai ka yi tsammanin su wani lu’ulu’u ne da aka baza
وَإِذَا رَأَيۡتَ ثَمَّ رَأَيۡتَ نَعِيمٗا وَمُلۡكٗا كَبِيرًا
Idan kuma ka yi kallo a can, za ka ga ni’ima da kuma mulki qasaitacce
عَٰلِيَهُمۡ ثِيَابُ سُندُسٍ خُضۡرٞ وَإِسۡتَبۡرَقٞۖ وَحُلُّوٓاْ أَسَاوِرَ مِن فِضَّةٖ وَسَقَىٰهُمۡ رَبُّهُمۡ شَرَابٗا طَهُورًا
Suna sanye da korayen tufafin alharini marar kauri da na alharini mai kauri; aka kuma yi musu ado da warawarai na azurfa, Ubangijinsu kuma Ya shayar da su abin sha mai tsarki
إِنَّ هَٰذَا كَانَ لَكُمۡ جَزَآءٗ وَكَانَ سَعۡيُكُم مَّشۡكُورًا
Lalle wannan ya kasance sakamako ne a gare ku, kuma aikinku ya kasance abin godewa
إِنَّا نَحۡنُ نَزَّلۡنَا عَلَيۡكَ ٱلۡقُرۡءَانَ تَنزِيلٗا
Lalle Mu Muka saukar maka da Alqur’ani daki-daki
فَٱصۡبِرۡ لِحُكۡمِ رَبِّكَ وَلَا تُطِعۡ مِنۡهُمۡ ءَاثِمًا أَوۡ كَفُورٗا
Saboda haka ka yi haquri da hukuncin Ubangijinka kada kuwa ka bi mai yawan savo ko mai yawan kafircewa daga cikinsu
وَٱذۡكُرِ ٱسۡمَ رَبِّكَ بُكۡرَةٗ وَأَصِيلٗا
Ka kuma ambaci sunan Ubangijinka safe da yamma
وَمِنَ ٱلَّيۡلِ فَٱسۡجُدۡ لَهُۥ وَسَبِّحۡهُ لَيۡلٗا طَوِيلًا
Da daddare kuma sai ka yi sujjada a gare Shi, ka kuma yi nafiloli saboda Shi a tsawon dare
إِنَّ هَـٰٓؤُلَآءِ يُحِبُّونَ ٱلۡعَاجِلَةَ وَيَذَرُونَ وَرَآءَهُمۡ يَوۡمٗا ثَقِيلٗا
Lalle waxannan suna son mai gaggawar qarewa (watau duniya), suna kuma watsi da rana mai nauyi[1] a bayansu
1- Watau ranar alqiyama mai cike da wahalhalu da musibu iri-iri.
نَّحۡنُ خَلَقۡنَٰهُمۡ وَشَدَدۡنَآ أَسۡرَهُمۡۖ وَإِذَا شِئۡنَا بَدَّلۡنَآ أَمۡثَٰلَهُمۡ تَبۡدِيلًا
Mu Muka halicce su Muka kuma qarfafa gavovinsu; idan kuwa Muka ga dama sai Mu musanya irinsu (kyakkyawar) musanyawa
إِنَّ هَٰذِهِۦ تَذۡكِرَةٞۖ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ سَبِيلٗا
Lalle wannan wa’azi ne; saboda haka wanda ya ga dama sai ya riqi hanya zuwa ga Ubangijinsa
وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا حَكِيمٗا
Kuma ba ganin damarku ba ce sai abin da Allah ya ga dama. Lalle Allah Ya kasance Masani, Mai hikima