لَآ أُقۡسِمُ بِيَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ
Ina rantsuwa da ranar alqiyama
Share :
وَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلنَّفۡسِ ٱللَّوَّامَةِ
Ina kuma rantsuwa da rai mai yawan zargin (kansa)[1]
1- Watau a kan gazawarsa wajen ayyukan alheri ko a kan aikata laifuka.
أَيَحۡسَبُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَلَّن نَّجۡمَعَ عِظَامَهُۥ
Yanzu mutum yana tsammanin ba za Mu tattara qasusuwansa ba?
بَلَىٰ قَٰدِرِينَ عَلَىٰٓ أَن نُّسَوِّيَ بَنَانَهُۥ
E, (Mu) Masu iko ne a kan Mu daidaita gavovin yatsunsa
بَلۡ يُرِيدُ ٱلۡإِنسَٰنُ لِيَفۡجُرَ أَمَامَهُۥ
Ba haka ba ne, mutum yana nufi ne kawai ya gurvata gabansa (da savon Allah)
يَسۡـَٔلُ أَيَّانَ يَوۡمُ ٱلۡقِيَٰمَةِ
Yana tambaya yaushe ne ranar alqiyamar?
فَإِذَا بَرِقَ ٱلۡبَصَرُ
To lokacin da gani ya ruxe
وَخَسَفَ ٱلۡقَمَرُ
Wata kuma ya yi duhu
وَجُمِعَ ٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُ
Aka kuma haxe rana da wata (a mafitarsu)
يَقُولُ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذٍ أَيۡنَ ٱلۡمَفَرُّ
A wannan rana ne mutum zai ce: “Ina wurin gudu?”
كَلَّا لَا وَزَرَ
Faufau, babu mafaka
إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمُسۡتَقَرُّ
Zuwa ga Ubangijinka ne kawai matabbata take a wannan rana
يُنَبَّؤُاْ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذِۭ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ
Za a bai wa mutum labari a wannan rana na abin da ya gabatar da kuma (abin da) ya jinkirtar (na ayyukansa)
بَلِ ٱلۡإِنسَٰنُ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦ بَصِيرَةٞ
A’a, shi dai mutum mai shaida ne a kan kansa
وَلَوۡ أَلۡقَىٰ مَعَاذِيرَهُۥ
Ko da kuwa ya kawo uzururrukansa
لَا تُحَرِّكۡ بِهِۦ لِسَانَكَ لِتَعۡجَلَ بِهِۦٓ
(Allah ya ce da Annabinsa): Kada ka motsa harshenka da shi (Alqur’ani) don gaggauta (karanta) shi
إِنَّ عَلَيۡنَا جَمۡعَهُۥ وَقُرۡءَانَهُۥ
Lalle tattara shi (a zuciyarka) da karanta shi yana kanmu
فَإِذَا قَرَأۡنَٰهُ فَٱتَّبِعۡ قُرۡءَانَهُۥ
Saboda haka idan Muka karanta (maka) shi sai ka bi karatunsa
ثُمَّ إِنَّ عَلَيۡنَا بَيَانَهُۥ
Sannan kuma bayaninsa yana kanmu
كَلَّا بَلۡ تُحِبُّونَ ٱلۡعَاجِلَةَ
Haba, ku dai kawai kuna son duniya ne
وَتَذَرُونَ ٱلۡأٓخِرَةَ
Kuna kuma barin lahira
وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ نَّاضِرَةٌ
Wasu fuskokin a wannan rana a ni’imce suke
إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٞ
Suna masu kallon Ubangijinsu
وَوُجُوهٞ يَوۡمَئِذِۭ بَاسِرَةٞ
Wasu fuskokin kuma a wannan rana a xaxxaure suke
تَظُنُّ أَن يُفۡعَلَ بِهَا فَاقِرَةٞ
Suna tabbatar da cewa, za a saukar musu da wani bala’i
كَلَّآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلتَّرَاقِيَ
Ku saurara, yayin da rai ya iso a karankarama[1]
1- Watau ya zo qasusuwan qirji a lokacin gargarar mutuwa.
وَقِيلَ مَنۡۜ رَاقٖ
Aka kuma ce: “Wane ne mai tawaida[1]?”
1- Watau masu jinya su riqa tambayar junansu cewa, wane ne zai yi masa ruqya ko zai zamu sauqi?
وَظَنَّ أَنَّهُ ٱلۡفِرَاقُ
Ya kuma tabbata cewar (wannan) shi ne rabuwarsa (da duniya)
وَٱلۡتَفَّتِ ٱلسَّاقُ بِٱلسَّاقِ
Kuma tsananin bala’i ya haxu
إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمَسَاقُ
To zuwa Ubangijinka ne (za a) kora ka a wannan ranar