سَأَلَ سَآئِلُۢ بِعَذَابٖ وَاقِعٖ
Mai tambaya ya yi tambaya game da wata azaba mai aukuwa[1]
1- Watau wadda Annabi () yake musu kashedi da ita idan sun qi imani. Duba Suratul Anfal, aya ta 32. Mai tambayar kuwa shi ne Nadhru xan Haris.
Share :
لِّلۡكَٰفِرِينَ لَيۡسَ لَهُۥ دَافِعٞ
Ga kafirai (wadda) ba ta da wani mai kaxe ta
مِّنَ ٱللَّهِ ذِي ٱلۡمَعَارِجِ
Daga Allah Mai matattakalai
تَعۡرُجُ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ وَٱلرُّوحُ إِلَيۡهِ فِي يَوۡمٖ كَانَ مِقۡدَارُهُۥ خَمۡسِينَ أَلۡفَ سَنَةٖ
Mala’iku tare da Jibrilu suna hawa zuwa gare Shi a cikin wata rana (wadda) gwargwadonta yake daidai da shekara dubu hamsin
فَٱصۡبِرۡ صَبۡرٗا جَمِيلًا
Sai ka yi haquri kyakkyawan haquri
إِنَّهُمۡ يَرَوۡنَهُۥ بَعِيدٗا
Lalle su suna ganin ta mai nisa ce
وَنَرَىٰهُ قَرِيبٗا
Mu kuma Muna ganin ta kusa-kusa
يَوۡمَ تَكُونُ ٱلسَّمَآءُ كَٱلۡمُهۡلِ
A ranar da sama za ta kasance kamar narkakkiyar dalma
وَتَكُونُ ٱلۡجِبَالُ كَٱلۡعِهۡنِ
Duwatsu kuma su zama kamar kaxaxxiyar auduga (ta gashin tumaki)
وَلَا يَسۡـَٔلُ حَمِيمٌ حَمِيمٗا
Kuma aboki ba ya tambayar aboki
يُبَصَّرُونَهُمۡۚ يَوَدُّ ٱلۡمُجۡرِمُ لَوۡ يَفۡتَدِي مِنۡ عَذَابِ يَوۡمِئِذِۭ بِبَنِيهِ
(Alhali kuma) ana nuna musu junansu. Mai laifi ya riqa burin ina ma zai fanshi kansa daga azabar wannan rana da ‘ya’yansa
وَصَٰحِبَتِهِۦ وَأَخِيهِ
Da matarsa da xan’uwansa
وَفَصِيلَتِهِ ٱلَّتِي تُـٔۡوِيهِ
Da danginsa waxanda suke kare shi
وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا ثُمَّ يُنجِيهِ
Da ma duk wanda yake a bayan qasa baki xaya, sannan (fansar) ta tserar da shi
كَلَّآۖ إِنَّهَا لَظَىٰ
Faufau! Lalle ita (wutar) Laza ce
نَزَّاعَةٗ لِّلشَّوَىٰ
Mai xaxxaye fatar kai
تَدۡعُواْ مَنۡ أَدۡبَرَ وَتَوَلَّىٰ
Tana kiran wanda ya juya ya ba da baya
وَجَمَعَ فَأَوۡعَىٰٓ
Ya kuma tara (dukiya) sai ya voye (ta)
۞إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ خُلِقَ هَلُوعًا
Lalle mutum an halicce shi mai rashin nutsuwa ne
إِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ جَزُوعٗا
(Watau) idan sharri ya same shi ya zama mai raki
وَإِذَا مَسَّهُ ٱلۡخَيۡرُ مَنُوعًا
Idan kuma alheri ya same shi ya zama mai maqo
إِلَّا ٱلۡمُصَلِّينَ
Sai dai masallata
ٱلَّذِينَ هُمۡ عَلَىٰ صَلَاتِهِمۡ دَآئِمُونَ
Waxanda suke masu dawwama a kan sallarsu
وَٱلَّذِينَ فِيٓ أَمۡوَٰلِهِمۡ حَقّٞ مَّعۡلُومٞ
Waxanda kuma suke akwai haqqi sananne a cikin dukiyoyinsu
لِّلسَّآئِلِ وَٱلۡمَحۡرُومِ
Ga mai roqo da wanda ake hana wa (saboda ba ya roqo)
وَٱلَّذِينَ يُصَدِّقُونَ بِيَوۡمِ ٱلدِّينِ
Waxanda kuma suke gaskata ranar sakamako
وَٱلَّذِينَ هُم مِّنۡ عَذَابِ رَبِّهِم مُّشۡفِقُونَ
Waxanda kuma suke tsoron azabar Ubangijinsu
إِنَّ عَذَابَ رَبِّهِمۡ غَيۡرُ مَأۡمُونٖ
Lalle azabar Ubangijinsu ba abar amincewa ba ce
وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِفُرُوجِهِمۡ حَٰفِظُونَ
Waxanda kuma suke kiyaye al’aurarsu (daga yin zina)
إِلَّا عَلَىٰٓ أَزۡوَٰجِهِمۡ أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُمۡ فَإِنَّهُمۡ غَيۡرُ مَلُومِينَ
Sai a wajan matayensu ko kuma qwarqarorinsu; to su a nan ba ababen zargi ba ne