ٱقۡتَرَبَتِ ٱلسَّاعَةُ وَٱنشَقَّ ٱلۡقَمَرُ
Alqiyama ta kusanto, wata kuma ya tsage[1]
1- Watau a zamanin Manzon Allah () wanda mushirikan Quraishawa suka gani da idonsu, bayan sun nemi ya nuna musu mu’ujiza.
وَإِن يَرَوۡاْ ءَايَةٗ يُعۡرِضُواْ وَيَقُولُواْ سِحۡرٞ مُّسۡتَمِرّٞ
Idan kuma suka ga wata aya sai su kau da kai kuma su ce: “Wannan sihiri ne qaqqarfa.”
وَكَذَّبُواْ وَٱتَّبَعُوٓاْ أَهۡوَآءَهُمۡۚ وَكُلُّ أَمۡرٖ مُّسۡتَقِرّٞ
Suka kuma qaryata, suka bi soye-soyen zukatansu. Kowane al’amari kuwa (na alheri ko na sharri) mai tabbata ne
وَلَقَدۡ جَآءَهُم مِّنَ ٱلۡأَنۢبَآءِ مَا فِيهِ مُزۡدَجَرٌ
Haqiqa kuma wasu labarai waxanda tsawatarwa take cikinsu sun zo musu
حِكۡمَةُۢ بَٰلِغَةٞۖ فَمَا تُغۡنِ ٱلنُّذُرُ
Hikima ce mai kaiwa matuqa, sai dai kuma gargaxin ba ya amfanarwa
فَتَوَلَّ عَنۡهُمۡۘ يَوۡمَ يَدۡعُ ٱلدَّاعِ إِلَىٰ شَيۡءٖ نُّكُرٍ
Saboda haka ka rabu da su. A ranar da mai kira[1] zai yi kira zuwa ga wani abu na qi a rai[2]
1- Shi ne Mala’ika Israfilu () mai busa a qaho.
2- Watau lokacin fitowa daga qaburbura.
خُشَّعًا أَبۡصَٰرُهُمۡ يَخۡرُجُونَ مِنَ ٱلۡأَجۡدَاثِ كَأَنَّهُمۡ جَرَادٞ مُّنتَشِرٞ
Idanuwansu suna a qasqance suna fitowa daga qaburbura, kai ka ce su farin xango ne masu bazuwa
مُّهۡطِعِينَ إِلَى ٱلدَّاعِۖ يَقُولُ ٱلۡكَٰفِرُونَ هَٰذَا يَوۡمٌ عَسِرٞ
Suna gaggawa zuwa ga mai kiran; kafirai za su riqa cewa: “Wannan rana ce mai tsanani.”
۞كَذَّبَتۡ قَبۡلَهُمۡ قَوۡمُ نُوحٖ فَكَذَّبُواْ عَبۡدَنَا وَقَالُواْ مَجۡنُونٞ وَٱزۡدُجِرَ
Mutanen Nuhu sun qaryata kafin su (Quraishawa), sai suka qaryata Bawanmu suka kuma ce, mahaukaci ne, aka kuma kyare (shi)
فَدَعَا رَبَّهُۥٓ أَنِّي مَغۡلُوبٞ فَٱنتَصِرۡ
Sai ya roqi Ubangijinsa (cewa): “Lalle an fi qarfina, sai Ka taimaka.”
فَفَتَحۡنَآ أَبۡوَٰبَ ٱلسَّمَآءِ بِمَآءٖ مُّنۡهَمِرٖ
Sai Muka buxe qofofin sama da ruwa mai kwararowa
وَفَجَّرۡنَا ٱلۡأَرۡضَ عُيُونٗا فَٱلۡتَقَى ٱلۡمَآءُ عَلَىٰٓ أَمۡرٖ قَدۡ قُدِرَ
Muka kuma vuvvugar da idanuwan ruwa daga qasa, sai ruwayen suka haxu a bisa al’amarin da aka riga aka qaddara
وَحَمَلۡنَٰهُ عَلَىٰ ذَاتِ أَلۡوَٰحٖ وَدُسُرٖ
Muka kuma xauke shi a kan (jirgin ruwa) mai alluna da qusoshi
تَجۡرِي بِأَعۡيُنِنَا جَزَآءٗ لِّمَن كَانَ كُفِرَ
Yana gudu a kan idonmu, don ya zama sakayya ga wanda aka kafirce wa (watau Nuhu)
وَلَقَد تَّرَكۡنَٰهَآ ءَايَةٗ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ
Haqiqa kuma Mun bar (abin da ya faru) ya zama aya, to ko akwai mai wa’azantuwa?
فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ
To qaqa azabata da gargaxina suka kasance?
وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ
Haqiqa kuma Mun sauqaqe Alqur’ani don tunasarwa da hadda, to ko akwai mai wa’azantuwa?
كَذَّبَتۡ عَادٞ فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ
Adawa sun qaryata (Annabinsu), to qaqa azabata da gargaxina suka kasance?
إِنَّآ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ رِيحٗا صَرۡصَرٗا فِي يَوۡمِ نَحۡسٖ مُّسۡتَمِرّٖ
Lalle Mu Mun aiko musu da iska mai qarfi a ranar shu’umci mai zarcewa
تَنزِعُ ٱلنَّاسَ كَأَنَّهُمۡ أَعۡجَازُ نَخۡلٖ مُّنقَعِرٖ
Tana tumvuko mutane[1] ta kayar su, kai ka ce su kututturan dabinai ne da aka tuttunvuke
1- Watau daga doron qasa ta yi sama da su sannan ta kifo da su ta kawunansu su faxo qasa a mace.
فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ
To qaqa azabata da gargaxina suka kasance?
وَلَقَدۡ يَسَّرۡنَا ٱلۡقُرۡءَانَ لِلذِّكۡرِ فَهَلۡ مِن مُّدَّكِرٖ
Kuma haqiqa Mun sauqaqe Alqur’ani don tunatarwa, to ko akwai mai wa’azantuwa?
كَذَّبَتۡ ثَمُودُ بِٱلنُّذُرِ
Samudawa sun qaryata gargaxi
فَقَالُوٓاْ أَبَشَرٗا مِّنَّا وَٰحِدٗا نَّتَّبِعُهُۥٓ إِنَّآ إِذٗا لَّفِي ضَلَٰلٖ وَسُعُرٍ
Sannan suka ce: “Yanzu mutum xaya daga cikinmu ne za mu bi? To lalle idan mun yi haka, mun tabbata cikin vata da hauka
أَءُلۡقِيَ ٱلذِّكۡرُ عَلَيۡهِ مِنۢ بَيۡنِنَا بَلۡ هُوَ كَذَّابٌ أَشِرٞ
“Yanzu (zai yiwu) a saukar masa da wahayi a tsakaninmu? A’a, shi dai maqaryaci ne mai tsananin girman kai.”
سَيَعۡلَمُونَ غَدٗا مَّنِ ٱلۡكَذَّابُ ٱلۡأَشِرُ
A gobe lalle za su san wane ne maqaryacin mai girman kai
إِنَّا مُرۡسِلُواْ ٱلنَّاقَةِ فِتۡنَةٗ لَّهُمۡ فَٱرۡتَقِبۡهُمۡ وَٱصۡطَبِرۡ
Lalle Mu Masu aiko taguwa ne don ta zama fitina a gare su, saboda haka ka saurara musu, kuma ka jure
وَنَبِّئۡهُمۡ أَنَّ ٱلۡمَآءَ قِسۡمَةُۢ بَيۡنَهُمۡۖ كُلُّ شِرۡبٖ مُّحۡتَضَرٞ
Kuma ka ba su labarin cewa ruwan sha an raba ne tsakaninsu (da ita taguwar); kowane akwai ranar shansa
فَنَادَوۡاْ صَاحِبَهُمۡ فَتَعَاطَىٰ فَعَقَرَ
Sai suka kirawo (shaqiyin) abokin nasu sai ya xauki (abin sara) sai ya sare ta
فَكَيۡفَ كَانَ عَذَابِي وَنُذُرِ
To qaqa azabata da gargaxina suka kasance?