وَٱلذَّـٰرِيَٰتِ ذَرۡوٗا
Na rantse da iskoki masu ta da qura
Share :
فَٱلۡحَٰمِلَٰتِ وِقۡرٗا
Sannan da (giragizai) waxanda suke xauke da nauyin ruwa
فَٱلۡجَٰرِيَٰتِ يُسۡرٗا
Da jiragen ruwa masu gudu a sauqaqe
فَٱلۡمُقَسِّمَٰتِ أَمۡرًا
Da kuma mala’iku masu raba abubuwa
إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَصَادِقٞ
Lalle abin da ake yi muku alqawarinsa tabbas gaskiya ne
وَإِنَّ ٱلدِّينَ لَوَٰقِعٞ
Kuma lalle sakamako tabbas mai afkuwa ne
وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلۡحُبُكِ
Na rantse da sama ma’abociyar hanyoyi
إِنَّكُمۡ لَفِي قَوۡلٖ مُّخۡتَلِفٖ
Lalle ku (mutanen Makka) tabbas kuna cikin magana mai sassavawa
يُؤۡفَكُ عَنۡهُ مَنۡ أُفِكَ
Ana karkatar da wanda aka karkatar daga gare shi (Annabi ko Alqur’ani)
قُتِلَ ٱلۡخَرَّـٰصُونَ
An la’anci maqaryata[1]
1- Watau game da Annabi () da kuma Alqur’ani.
ٱلَّذِينَ هُمۡ فِي غَمۡرَةٖ سَاهُونَ
Waxanda suke rafkanannu a cikin jahilci
يَسۡـَٔلُونَ أَيَّانَ يَوۡمُ ٱلدِّينِ
Suna tambayar yaushe ne ranar sakamako?
يَوۡمَ هُمۡ عَلَى ٱلنَّارِ يُفۡتَنُونَ
A ranar da su za a azabtar da su kan wuta
ذُوقُواْ فِتۡنَتَكُمۡ هَٰذَا ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تَسۡتَعۡجِلُونَ
(A ce da su): “Ku xanxani azabarku, wannan shi ne abin da kuka kasance kuna neman gaggautowarsa.”
إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّـٰتٖ وَعُيُونٍ
Lalle masu taqawa suna cikin gidajen Aljanna da idanuwan (ruwa)
ءَاخِذِينَ مَآ ءَاتَىٰهُمۡ رَبُّهُمۡۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَبۡلَ ذَٰلِكَ مُحۡسِنِينَ
Suna masu kwasar abin da Ubangijinsu Ya ba su. Lalle su sun zamanto kafin wannan (ranar) masu kyautata ayyuka ne
كَانُواْ قَلِيلٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِ مَا يَهۡجَعُونَ
Sun kasance kaxan ne na dare suke bacci[1]
1- Watau sun kasance masu yawaita sallar dare.
وَبِٱلۡأَسۡحَارِ هُمۡ يَسۡتَغۡفِرُونَ
A gefin asuba kuma su suna neman gafara
وَفِيٓ أَمۡوَٰلِهِمۡ حَقّٞ لِّلسَّآئِلِ وَٱلۡمَحۡرُومِ
A cikin dukiyoyinsu kuma akwai wani haqqi na mai bara da mai kamewa daga yin ta
وَفِي ٱلۡأَرۡضِ ءَايَٰتٞ لِّلۡمُوقِنِينَ
A cikin qasa kuma akwai ayoyi ga masu sakankancewa
وَفِيٓ أَنفُسِكُمۡۚ أَفَلَا تُبۡصِرُونَ
Da kuma cikin kawunanku. Yanzu ba kwa lura ba?
وَفِي ٱلسَّمَآءِ رِزۡقُكُمۡ وَمَا تُوعَدُونَ
A cikin sammai kuma akwai arzikinku da kuma abin da aka yi muku alkawarinsa
فَوَرَبِّ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ إِنَّهُۥ لَحَقّٞ مِّثۡلَ مَآ أَنَّكُمۡ تَنطِقُونَ
To na rantse da Ubangijin sammai da qasa, lalle shi (abin da ake yi muku gargaxinsa) tabbas gaskiya ne kamar dai yadda kuke yin magana
هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ضَيۡفِ إِبۡرَٰهِيمَ ٱلۡمُكۡرَمِينَ
Shin labarin baqin Ibrahimu masu girma[1] ya zo maka?
1- Su ne mala’iku da Allah ya aiko.
إِذۡ دَخَلُواْ عَلَيۡهِ فَقَالُواْ سَلَٰمٗاۖ قَالَ سَلَٰمٞ قَوۡمٞ مُّنكَرُونَ
Lokacin da suka shiga wurinsa sai suka ce: “Muna maka sallama;” ya ce: “Aminci ya tabbata gare ku, (ku) mutane ne da ba sanannu ba.”
فَرَاغَ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ فَجَآءَ بِعِجۡلٖ سَمِينٖ
Sai ya saxaxa da sauri zuwa ga iyalinsa, sai ya zo da wani xan maraqi mai mai
فَقَرَّبَهُۥٓ إِلَيۡهِمۡ قَالَ أَلَا تَأۡكُلُونَ
Sai ya kusanta shi gare su, ya ce: “Yanzu ba za ku ci ba?”
فَأَوۡجَسَ مِنۡهُمۡ خِيفَةٗۖ قَالُواْ لَا تَخَفۡۖ وَبَشَّرُوهُ بِغُلَٰمٍ عَلِيمٖ
(Da suka qi ci) sai ya tsorata da su, suka ce: “Kada ka tsorata;” suka kuma yi masa albishir da samun yaro mai ilimi[1]
1- Watau Annabi Ishaq ().
فَأَقۡبَلَتِ ٱمۡرَأَتُهُۥ فِي صَرَّةٖ فَصَكَّتۡ وَجۡهَهَا وَقَالَتۡ عَجُوزٌ عَقِيمٞ
Sannan sai matarsa ta gabato su cikin wata qara, sai ta mari fuskarta ta ce: “Yanzu tsohuwa bakarara (ita ce za ta haihu?)”
قَالُواْ كَذَٰلِكِ قَالَ رَبُّكِۖ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡحَكِيمُ ٱلۡعَلِيمُ
Suka ce, “Kamar haka Ubangijinki Ya ce, lalle Shi Mai hikima ne, Masani.”