وَٱلصَّـٰٓفَّـٰتِ صَفّٗا
Ina rantsuwa da mala’iku masu yin sahu-sahu
Share :
فَٱلزَّـٰجِرَٰتِ زَجۡرٗا
Sannan da masu yi wa girgije tsawa
فَٱلتَّـٰلِيَٰتِ ذِكۡرًا
Da masu karanta maganar Allah
إِنَّ إِلَٰهَكُمۡ لَوَٰحِدٞ
Lalle Ubangiijnku tabbas Xaya ne
رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا وَرَبُّ ٱلۡمَشَٰرِقِ
Ubangijin sammai da qasa da abin da yake tsakaninsu, kuma Ubangijin wuraren hudowar rana
إِنَّا زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنۡيَا بِزِينَةٍ ٱلۡكَوَاكِبِ
Lalle Mun qawata sama ta kusa da ado na taurari
وَحِفۡظٗا مِّن كُلِّ شَيۡطَٰنٖ مَّارِدٖ
Da kuma tsaro daga dukkan wani shaixan mai tsaurin kai
لَّا يَسَّمَّعُونَ إِلَى ٱلۡمَلَإِ ٱلۡأَعۡلَىٰ وَيُقۡذَفُونَ مِن كُلِّ جَانِبٖ
Ba kuma za su iya jiyowa ba (daga asirin) mala’iku na sama, sai a yi ta jifan su ta kowane vangare
دُحُورٗاۖ وَلَهُمۡ عَذَابٞ وَاصِبٌ
Don kora; suna kuma da wata azaba dawwamamma
إِلَّا مَنۡ خَطِفَ ٱلۡخَطۡفَةَ فَأَتۡبَعَهُۥ شِهَابٞ ثَاقِبٞ
Sai dai wanda ya yi fautowar jin, to sai wani tauraro mai haske da quna ya biyo shi
فَٱسۡتَفۡتِهِمۡ أَهُمۡ أَشَدُّ خَلۡقًا أَم مَّنۡ خَلَقۡنَآۚ إِنَّا خَلَقۡنَٰهُم مِّن طِينٖ لَّازِبِۭ
Ka tambaye su cewa, yanzu su suka fi qarfin halitta ko kuwa waxanda a da Muka halitta? Lalle Mu Mun halicce su daga wani tavo mai danqo
بَلۡ عَجِبۡتَ وَيَسۡخَرُونَ
A’a, kai dai ka yi mamakin (ikon Allah da qaryatawarsu) ne, su kuma suna yin izgili
وَإِذَا ذُكِّرُواْ لَا يَذۡكُرُونَ
Idan kuma aka yi musu wa’azi ba sa wa’azantuwa
وَإِذَا رَأَوۡاْ ءَايَةٗ يَسۡتَسۡخِرُونَ
Idan kuma suka ga wata aya sai su tsananta ba’a
وَقَالُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ مُّبِينٌ
Su kuma ce: “Wannan ba wani abu ba ne in ban da sihiri mabayyani
أَءِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابٗا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ
“Yanzu idan muka mutu muka zama qasa da qasusuwa shin da gaske za a tashe mu?
أَوَءَابَآؤُنَا ٱلۡأَوَّلُونَ
“Haka ma da iyayenmu na farko?”
قُلۡ نَعَمۡ وَأَنتُمۡ دَٰخِرُونَ
Ka ce: “Na’am, (za a tashe ku) kuna kuwa qasqantattu.”
فَإِنَّمَا هِيَ زَجۡرَةٞ وَٰحِدَةٞ فَإِذَا هُمۡ يَنظُرُونَ
To (wannan) ba wani abu ba ne sai kawai tsawa guda xaya, sai ga su suna sauraron (abin da zai faru)
وَقَالُواْ يَٰوَيۡلَنَا هَٰذَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ
Sai su ce: “Kaitonmu!” (Sai a ce da su): “Wannan ita ce ranar sakamako
هَٰذَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِ ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ
“Wannan ita ce ranar hukunci wadda kuka kasance kuna qaryatawa.”
۞ٱحۡشُرُواْ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ وَأَزۡوَٰجَهُمۡ وَمَا كَانُواْ يَعۡبُدُونَ
(Za a ce da mala’iku): “Ku tattaro waxanda suka yi zalunci su da abokan haxinsu (shaixanu) da kuma abin da suka kasance suna bauta wa
مِن دُونِ ٱللَّهِ فَٱهۡدُوهُمۡ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡجَحِيمِ
Waxanda ba Allah ba, sai ku nuna musu hanyar zuwa wutar Jahima
وَقِفُوهُمۡۖ إِنَّهُم مَّسۡـُٔولُونَ
“Kuma ku tsayar da su; don lalle za a tambaye su
مَا لَكُمۡ لَا تَنَاصَرُونَ
“Cewa: ‘Me ya sa ba kwa taimakon juna ne?’”
بَلۡ هُمُ ٱلۡيَوۡمَ مُسۡتَسۡلِمُونَ
Ba haka ba ne, su dai a yau masu miqa wuya ne
وَأَقۡبَلَ بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖ يَتَسَآءَلُونَ
Shashinsu kuma ya fuskanci shashi suna tambayar juna
قَالُوٓاْ إِنَّكُمۡ كُنتُمۡ تَأۡتُونَنَا عَنِ ٱلۡيَمِينِ
Suka ce: “Lalle kun kasance kuna zo mana ta damanmu[1] (don mu amince muku).”
1- Watau ta hanyar yaudara da daxin baki.
قَالُواْ بَل لَّمۡ تَكُونُواْ مُؤۡمِنِينَ
Suka ce: “A’a, ba ku dai kasance muminai ba ne
وَمَا كَانَ لَنَا عَلَيۡكُم مِّن سُلۡطَٰنِۭۖ بَلۡ كُنتُمۡ قَوۡمٗا طَٰغِينَ
“Kuma mu ba mu da wani iko a kanku; ku dai kawai kun kasance mutane ne masu xagawa