يسٓ
YA SIN[1]
1- Duba Suratul Baqara aya ta 1, hashiya ta 8.
وَٱلۡقُرۡءَانِ ٱلۡحَكِيمِ
Na rantse da Alqur’ani mai hikima
إِنَّكَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Lalle kai (Manzon Allah) tabbas kana daga cikin manzanni
عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
(Kana) a kan tafarki madaidaici
تَنزِيلَ ٱلۡعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ
(Alqur’ani) saukarwar (Allah) Mabuwayi Mai jin qai ne
لِتُنذِرَ قَوۡمٗا مَّآ أُنذِرَ ءَابَآؤُهُمۡ فَهُمۡ غَٰفِلُونَ
Don ka gargaxi mutanen da ba a yi wa iyayensu gargaxi ba[1], don haka kuwa suna cikin gafala
1- Su ne al’ummar Larabawa waxanda wani annabi bai zo musu ba.
لَقَدۡ حَقَّ ٱلۡقَوۡلُ عَلَىٰٓ أَكۡثَرِهِمۡ فَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ
Haqiqa hukuncin Allah (na azaba) ya wajaba a kan mafiya yawansu, don ba za su yi imani ba
إِنَّا جَعَلۡنَا فِيٓ أَعۡنَٰقِهِمۡ أَغۡلَٰلٗا فَهِيَ إِلَى ٱلۡأَذۡقَانِ فَهُم مُّقۡمَحُونَ
Lalle Mun sanya ququmai a wuyoyinsu har zuwa havovinsu, don haka kawunansu a xage suke
وَجَعَلۡنَا مِنۢ بَيۡنِ أَيۡدِيهِمۡ سَدّٗا وَمِنۡ خَلۡفِهِمۡ سَدّٗا فَأَغۡشَيۡنَٰهُمۡ فَهُمۡ لَا يُبۡصِرُونَ
Muka kuma sanya wani shamaki a gabansu da kuma shamaki a bayansu, sai Muka lulluve musu (idanuwa), don haka ba sa gani
وَسَوَآءٌ عَلَيۡهِمۡ ءَأَنذَرۡتَهُمۡ أَمۡ لَمۡ تُنذِرۡهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ
Kuma duk xaya ne a wurinsu ko ka yi musu gargaxi ko ba ka yi musu gargaxi ba, ba za su yi imani ba
إِنَّمَا تُنذِرُ مَنِ ٱتَّبَعَ ٱلذِّكۡرَ وَخَشِيَ ٱلرَّحۡمَٰنَ بِٱلۡغَيۡبِۖ فَبَشِّرۡهُ بِمَغۡفِرَةٖ وَأَجۡرٖ كَرِيمٍ
Kana yin gargaxi ne kawai ga wanda ya bi umarnin Alqur’ani, ya kuma ji tsoron Allah ba tare da ya gan Shi ba; sai ka yi masa albishir da samun gafara da lada na karamci
إِنَّا نَحۡنُ نُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰ وَنَكۡتُبُ مَا قَدَّمُواْ وَءَاثَٰرَهُمۡۚ وَكُلَّ شَيۡءٍ أَحۡصَيۡنَٰهُ فِيٓ إِمَامٖ مُّبِينٖ
Lalle Mu ne za Mu raya matattu, Muke kuma rubuta irin abubuwan da suka gabatar (a rayuwarsu) da kuma abin da suka bari a bayansu (bayan mutuwa). Kowane abu kuma Mun qididdige shi a cikin Lauhul-Mahafuzu
وَٱضۡرِبۡ لَهُم مَّثَلًا أَصۡحَٰبَ ٱلۡقَرۡيَةِ إِذۡ جَآءَهَا ٱلۡمُرۡسَلُونَ
Kuma ka ba su misali da mutanen wata alqarya lokacin da manzannin suka zo mata
إِذۡ أَرۡسَلۡنَآ إِلَيۡهِمُ ٱثۡنَيۡنِ فَكَذَّبُوهُمَا فَعَزَّزۡنَا بِثَالِثٖ فَقَالُوٓاْ إِنَّآ إِلَيۡكُم مُّرۡسَلُونَ
A yayin da Muka aika musu (manzanni) biyu sai suka qaryata su, sannan Muka qarfafe su da na uku, sai suka ce: “Lalle mu manzanni ne zuwa gare ku.”
قَالُواْ مَآ أَنتُمۡ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُنَا وَمَآ أَنزَلَ ٱلرَّحۡمَٰنُ مِن شَيۡءٍ إِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا تَكۡذِبُونَ
Suka ce: “Ku ai ba kowa ba ne face mutane kamarmu, kuma (Allah) Mai rahama bai saukar da komai ba, ku dai ba abin da kuke yi sai qarya.”
قَالُواْ رَبُّنَا يَعۡلَمُ إِنَّآ إِلَيۡكُمۡ لَمُرۡسَلُونَ
Suka ce: “Ubangijinmu Yana sane da cewa mu lalle tabbas manzanni ne zuwa gare ku
وَمَا عَلَيۡنَآ إِلَّا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ
“Kuma babu wani abu a kanmu sai isar da aike bayyananne.”
قَالُوٓاْ إِنَّا تَطَيَّرۡنَا بِكُمۡۖ لَئِن لَّمۡ تَنتَهُواْ لَنَرۡجُمَنَّكُمۡ وَلَيَمَسَّنَّكُم مِّنَّا عَذَابٌ أَلِيمٞ
Suka ce: “Mu dai lalle mun camfa ku, tabbas idan ba ku bari ba to za mu jefe ku, kuma tabbas za ku gamu da azaba mai raxaxi daga gare mu.”
قَالُواْ طَـٰٓئِرُكُم مَّعَكُمۡ أَئِن ذُكِّرۡتُمۚ بَلۡ أَنتُمۡ قَوۡمٞ مُّسۡرِفُونَ
Suka ce: “Camfinku ya qare a kanku. Yanzu don an yi muku gargaxi ne (za ku faxi haka?) A’a, ku dai mutane ne mavarnata.”
وَجَآءَ مِنۡ أَقۡصَا ٱلۡمَدِينَةِ رَجُلٞ يَسۡعَىٰ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱتَّبِعُواْ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Wani mutum kuma ya zo daga can qarshen gari yana sauri ya ce: “Ya ku mutanena, ku bi waxannan manzannin
ٱتَّبِعُواْ مَن لَّا يَسۡـَٔلُكُمۡ أَجۡرٗا وَهُم مُّهۡتَدُونَ
“Ku bi waxanda ba sa tambayar ku wani lada, ga su kuma shiryayyu
وَمَالِيَ لَآ أَعۡبُدُ ٱلَّذِي فَطَرَنِي وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ
“Ni kuma me zai hana ni in bauta wa wanda Ya halicce ni, kuma gare Shi ne za a komar da ku?
ءَأَتَّخِذُ مِن دُونِهِۦٓ ءَالِهَةً إِن يُرِدۡنِ ٱلرَّحۡمَٰنُ بِضُرّٖ لَّا تُغۡنِ عَنِّي شَفَٰعَتُهُمۡ شَيۡـٔٗا وَلَا يُنقِذُونِ
“Yanzu na riqi wasu ababen bauta ba Shi ba, alhali kuwa idan (Allah) Mai rahama Ya nufe ni da wata cuta, cetonsu ba zai amfana min komai ba, kuma ba za su iya tsamo ni ba?
إِنِّيٓ إِذٗا لَّفِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٍ
“Lalle ni idan na yi haka to tabbas na zama cikin vata mabayyani
إِنِّيٓ ءَامَنتُ بِرَبِّكُمۡ فَٱسۡمَعُونِ
“Lalle ni na yi imani da Ubangijinku, sai ku saurare ni.”
قِيلَ ٱدۡخُلِ ٱلۡجَنَّةَۖ قَالَ يَٰلَيۡتَ قَوۡمِي يَعۡلَمُونَ
Aka ce (da shi): “Shiga Aljanna.” Ya ce: “Kaicon mutanena, ina ma da suna sane?
بِمَا غَفَرَ لِي رَبِّي وَجَعَلَنِي مِنَ ٱلۡمُكۡرَمِينَ
“Da gafarar da Ubangijina Ya yi min, Ya kuma sanya ni cikin waxanda aka karrama?”
۞وَمَآ أَنزَلۡنَا عَلَىٰ قَوۡمِهِۦ مِنۢ بَعۡدِهِۦ مِن جُندٖ مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَمَا كُنَّا مُنزِلِينَ
Ba Mu kuma saukar da wata runduna (ta mala’iku) a kan mutanensa daga sama ba a bayansa, ba Mu kuma saba saukarwa ba
إِن كَانَتۡ إِلَّا صَيۡحَةٗ وَٰحِدَةٗ فَإِذَا هُمۡ خَٰمِدُونَ
Ba abin da ya kasance sai tsawa guda xaya, sai ga su matattu
يَٰحَسۡرَةً عَلَى ٱلۡعِبَادِۚ مَا يَأۡتِيهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Nadama ta tabbata ga bayi (masu qaryatawa), ba wani manzo da zai zo musu sai sun zamanto suna yi masa izgili