Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 1

الٓمٓرۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِۗ وَٱلَّذِيٓ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ ٱلۡحَقُّ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يُؤۡمِنُونَ

ALIF LAM MIM RA[1]. Waxannan ayoyi ne na Littafi (wato Alqur’ani). Wanda kuma aka saukar maka daga Ubangijinka gaskiya ne, sai dai lalle yawancin mutane ba sa yin imani


1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.


Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 2

ٱللَّهُ ٱلَّذِي رَفَعَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ بِغَيۡرِ عَمَدٖ تَرَوۡنَهَاۖ ثُمَّ ٱسۡتَوَىٰ عَلَى ٱلۡعَرۡشِۖ وَسَخَّرَ ٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَۖ كُلّٞ يَجۡرِي لِأَجَلٖ مُّسَمّٗىۚ يُدَبِّرُ ٱلۡأَمۡرَ يُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لَعَلَّكُم بِلِقَآءِ رَبِّكُمۡ تُوقِنُونَ

Allah Wanda Ya xaukaka sammai ba tare da wasu ginshiqai da kuke ganinsu ba; sannan Ya daidaita bisa Al’arshi[1]; Ya kuma hore muku rana da wata; kowannensu yana gudu zuwa wani lokaci qayyadadde. Yana shirya al’amari, Yana bayyana ayoyi don ku sakankance da haxuwarku da Ubangijinku


1- Duba Suratul A’araf aya ta 54, hashiya ta 126.


Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 3

وَهُوَ ٱلَّذِي مَدَّ ٱلۡأَرۡضَ وَجَعَلَ فِيهَا رَوَٰسِيَ وَأَنۡهَٰرٗاۖ وَمِن كُلِّ ٱلثَّمَرَٰتِ جَعَلَ فِيهَا زَوۡجَيۡنِ ٱثۡنَيۡنِۖ يُغۡشِي ٱلَّيۡلَ ٱلنَّهَارَۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ

Shi ne kuma Wanda Ya shimfixa qasa Ya kuma sanya turaku (na duwatsu) a cikinta da qoramu; kuma daga kowaxanne ‘ya’yan itace Ya sanya ma’aura biyu (mace da namiji); dare yana rufe rana. Lalle a game da waxannan abubuwan tabbas akwai ayoyi ga mutanen da suke tunani



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 4

وَفِي ٱلۡأَرۡضِ قِطَعٞ مُّتَجَٰوِرَٰتٞ وَجَنَّـٰتٞ مِّنۡ أَعۡنَٰبٖ وَزَرۡعٞ وَنَخِيلٞ صِنۡوَانٞ وَغَيۡرُ صِنۡوَانٖ يُسۡقَىٰ بِمَآءٖ وَٰحِدٖ وَنُفَضِّلُ بَعۡضَهَا عَلَىٰ بَعۡضٖ فِي ٱلۡأُكُلِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ

A cikin qasa kuma da akwai yankuna masu maqotaka da juna, da gonakai na inabai da shuke-shuke da dabinai masu tushiya xaya da kuma waxanda suke kowane tushiyarsa daban, ana shayar da su da ruwa xaya[1], Muna kuma fifita wasunsu a kan wasu wajen xanxano. Haqiqa a game da wannan da akwai ayoyi ga mutanen da suke da hankali


1- To amma sai su fito mabambanta a kamanni da xanxano da girma, duk kuwa da cewa an shuka su a qasa xaya kuma s`un sha ruwa xaya.


Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 5

۞وَإِن تَعۡجَبۡ فَعَجَبٞ قَوۡلُهُمۡ أَءِذَا كُنَّا تُرَٰبًا أَءِنَّا لَفِي خَلۡقٖ جَدِيدٍۗ أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِرَبِّهِمۡۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ ٱلۡأَغۡلَٰلُ فِيٓ أَعۡنَاقِهِمۡۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Idan kuwa kana mamakin (qaryata ka da suke yi), to ai abin mamaki shi ne faxarsu (cewa): “Yanzu idan muka zama turvaya anya kuwa za a sake halittarmu?” Waxannan su ne waxanda suka kafirce wa Ubangijinsu, waxannan kuma akwai ququmi (da za a sa musu) a wuyoyinsu. Waxannan kuwa su ne ‘yan wuta madawwama a cikinta



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 6

وَيَسۡتَعۡجِلُونَكَ بِٱلسَّيِّئَةِ قَبۡلَ ٱلۡحَسَنَةِ وَقَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهِمُ ٱلۡمَثُلَٰتُۗ وَإِنَّ رَبَّكَ لَذُو مَغۡفِرَةٖ لِّلنَّاسِ عَلَىٰ ظُلۡمِهِمۡۖ وَإِنَّ رَبَّكَ لَشَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Suna kuma nemanka da gaggauto musu da azaba tun kafin (su nemi) kyakkyawa (wato rahamar Allah), alhali kuwa haqiqa misalai (na waxanda aka halakar) a gabansu sun wuce. Lalle kuma Ubangijinka Ma’abocin gafara ne ga mutane a kan laifuffukansu, kuma lalle Ubangijinka tabbas Mai tsananin azaba ne



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 7

وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡهِ ءَايَةٞ مِّن رَّبِّهِۦٓۗ إِنَّمَآ أَنتَ مُنذِرٞۖ وَلِكُلِّ قَوۡمٍ هَادٍ

Waxanda suka kafirta suna cewa: “Me ya hana a saukar masa da wata aya daga Ubangijinsa?” Lalle kai mai gargaxi ne kawai; kowaxanne mutane kuwa suna da mai shiryawa



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 8

ٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا تَحۡمِلُ كُلُّ أُنثَىٰ وَمَا تَغِيضُ ٱلۡأَرۡحَامُ وَمَا تَزۡدَادُۚ وَكُلُّ شَيۡءٍ عِندَهُۥ بِمِقۡدَارٍ

Allah Yana sane da abin da (mahaifar) kowace mace take xauke da shi da kuma abin da mahaifa take ragewa da wanda take qarawa[1]; kowane abu kuma a wurinsa yana da gwargwado


1- Watau ana nufin lokacin haihuwarta, ko dai ta haihu kafin cikar wata tara, ko ta haihu bayan cikar wa’adin cikinta, ko xan ya zo cikakke da qoshin lafiya, ko kuma da wata nakasa ko rashin lafiya.


Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 9

عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ ٱلۡكَبِيرُ ٱلۡمُتَعَالِ

(Shi) Masanin abin da ke voye da na sarari ne, Mai girma, Mai cikar xaukaka



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 10

سَوَآءٞ مِّنكُم مَّنۡ أَسَرَّ ٱلۡقَوۡلَ وَمَن جَهَرَ بِهِۦ وَمَنۡ هُوَ مُسۡتَخۡفِۭ بِٱلَّيۡلِ وَسَارِبُۢ بِٱلنَّهَارِ

Duka xaya ne (a wurin Allah) wanda ya voye magana daga cikinku da wanda ya bayyana ta da wanda yake vuya da daddare da mai bayyana da rana



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 11

لَهُۥ مُعَقِّبَٰتٞ مِّنۢ بَيۡنِ يَدَيۡهِ وَمِنۡ خَلۡفِهِۦ يَحۡفَظُونَهُۥ مِنۡ أَمۡرِ ٱللَّهِۗ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُغَيِّرُ مَا بِقَوۡمٍ حَتَّىٰ يُغَيِّرُواْ مَا بِأَنفُسِهِمۡۗ وَإِذَآ أَرَادَ ٱللَّهُ بِقَوۡمٖ سُوٓءٗا فَلَا مَرَدَّ لَهُۥۚ وَمَا لَهُم مِّن دُونِهِۦ مِن وَالٍ

(Kowanensu) yana da (mala’iku) masu take masa baya a gabansa da kuma bayansa suna kiyaye shi da umarnin Allah. Lalle Allah ba Ya canja abin da mutane suke ciki har sai sun canja halayensu. Idan kuma Allah Ya yi nufin wata azaba ga mutane, to ba mai juyar da ita, ba su kuwa da wani mai jivintar su wanda ba Shi ba



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 12

هُوَ ٱلَّذِي يُرِيكُمُ ٱلۡبَرۡقَ خَوۡفٗا وَطَمَعٗا وَيُنشِئُ ٱلسَّحَابَ ٱلثِّقَالَ

Shi ne Wanda Yake nuna muku walqiya don tsoratarwa da kuma kwaxaitarwa, Yake kuma haxo hadari mai nauyi (xauke da ruwa)



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 13

وَيُسَبِّحُ ٱلرَّعۡدُ بِحَمۡدِهِۦ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ مِنۡ خِيفَتِهِۦ وَيُرۡسِلُ ٱلصَّوَٰعِقَ فَيُصِيبُ بِهَا مَن يَشَآءُ وَهُمۡ يُجَٰدِلُونَ فِي ٱللَّهِ وَهُوَ شَدِيدُ ٱلۡمِحَالِ

Tsawa tana tsarkake (Shi) tare da gode masa, mala’iku ma (suna tasbihi) saboda tsoron Sa, Yana kuma aiko da tsawawwaki sai Ya sami wanda Ya ga dama da su, kuma su (kafirai) ga su suna jayayya game da (sha’anin) Allah. Shi kuwa Mai tsananin qarfi ne



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 14

لَهُۥ دَعۡوَةُ ٱلۡحَقِّۚ وَٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَسۡتَجِيبُونَ لَهُم بِشَيۡءٍ إِلَّا كَبَٰسِطِ كَفَّيۡهِ إِلَى ٱلۡمَآءِ لِيَبۡلُغَ فَاهُ وَمَا هُوَ بِبَٰلِغِهِۦۚ وَمَا دُعَآءُ ٱلۡكَٰفِرِينَ إِلَّا فِي ضَلَٰلٖ

Gare Shi (Shi kaxai) kira na gaske yake; waxanda kuwa suke bauta wa wasu ba Shi ba, to ba sa amsa musu da komai illa tamkar wanda ya shimfixa tafukansa ga ruwa don ya isa bakinsa, ba kuwa zai isa gare shi ba[1]. Addu’ar kafirai kuma ba a komai take ba illa a cikin vata


1- Watau kamar mai shimfixa hannunsa a kan ruwa yana jiran ya taso ya shiga bakinsa yake yin aikin wofi, hakanan mai bautar wanin Allah shi ma yake yin bautar banza da wofi.


Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 15

وَلِلَّهِۤ يَسۡجُدُۤ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ طَوۡعٗا وَكَرۡهٗا وَظِلَٰلُهُم بِٱلۡغُدُوِّ وَٱلۡأٓصَالِ۩

Waxanda kuma suke sammai da qasa (duka) ga Allah suke sujjada sun so ko sun qi, haka kuma inuwoyinsu, safe da maraice



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 16

قُلۡ مَن رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ قُلِ ٱللَّهُۚ قُلۡ أَفَٱتَّخَذۡتُم مِّن دُونِهِۦٓ أَوۡلِيَآءَ لَا يَمۡلِكُونَ لِأَنفُسِهِمۡ نَفۡعٗا وَلَا ضَرّٗاۚ قُلۡ هَلۡ يَسۡتَوِي ٱلۡأَعۡمَىٰ وَٱلۡبَصِيرُ أَمۡ هَلۡ تَسۡتَوِي ٱلظُّلُمَٰتُ وَٱلنُّورُۗ أَمۡ جَعَلُواْ لِلَّهِ شُرَكَآءَ خَلَقُواْ كَخَلۡقِهِۦ فَتَشَٰبَهَ ٱلۡخَلۡقُ عَلَيۡهِمۡۚ قُلِ ٱللَّهُ خَٰلِقُ كُلِّ شَيۡءٖ وَهُوَ ٱلۡوَٰحِدُ ٱلۡقَهَّـٰرُ

Ka ce (da su): “Wane ne Ubangijin sammai da qasa?” Ka ce: “Allah ne”. Ka ce (da su): “Amma yaya kuka riqi wasu iyayen giji ba Shi ba su zama majivinta (gare ku), ba sa mallakar wani amfani ko cuta ga kansu?” Ka ce: “Shin makaho da mai gani za su yi daidai, ko kuwa shin duhu da haske za su yi daidai? Ko sun sanya wa Allah wasu abokan tarayya ne waxanda suka yi halitta kamar halittarsa, sai halittar ta yi musu kama da juna?” Ka ce: “Allah ne Mahaliccin komai, kuma Shi ne Makaxaici, Mai rinjaye.”



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 17

أَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَسَالَتۡ أَوۡدِيَةُۢ بِقَدَرِهَا فَٱحۡتَمَلَ ٱلسَّيۡلُ زَبَدٗا رَّابِيٗاۖ وَمِمَّا يُوقِدُونَ عَلَيۡهِ فِي ٱلنَّارِ ٱبۡتِغَآءَ حِلۡيَةٍ أَوۡ مَتَٰعٖ زَبَدٞ مِّثۡلُهُۥۚ كَذَٰلِكَ يَضۡرِبُ ٱللَّهُ ٱلۡحَقَّ وَٱلۡبَٰطِلَۚ فَأَمَّا ٱلزَّبَدُ فَيَذۡهَبُ جُفَآءٗۖ وَأَمَّا مَا يَنفَعُ ٱلنَّاسَ فَيَمۡكُثُ فِي ٱلۡأَرۡضِۚ كَذَٰلِكَ يَضۡرِبُ ٱللَّهُ ٱلۡأَمۡثَالَ

Ya saukar da ruwa daga sama, sai magudanai suka kwarara daidai gwargwadon abin da za su iya xauka, sai (shi ruwan) mai kwarara ya xauko kumfa a samansa. Akwai kuma wata kumfar kamarta daga abin da kuke narkawa a wuta don samun abin ado ko kuwa (qera) abin jin daxi. Kamar haka ne Allah Yake ba da misalin gaskiya da varna. To amma kumfar sai ta tafi ta bi iska; amma kuma abin da zai amfani mutane sai ya zauna a qasa. Kamar haka ne Allah Yake ba da misali



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 18

لِلَّذِينَ ٱسۡتَجَابُواْ لِرَبِّهِمُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ وَٱلَّذِينَ لَمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَهُۥ لَوۡ أَنَّ لَهُم مَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا وَمِثۡلَهُۥ مَعَهُۥ لَٱفۡتَدَوۡاْ بِهِۦٓۚ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ سُوٓءُ ٱلۡحِسَابِ وَمَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمِهَادُ

Waxanda suka amsa (kiran) Ubangijinsu suna da kyakkyawar (makoma). Waxanda kuwa ba su amsa ba, da a ce duk abin da ke qasa gaba xaya tare kuma da wani kwatankwacinsa duka nasu ne, to da lalle sun fanshi kansu da shi (ranar alqiyama). Waxannan suna da mummunan hisabi, kuma Jahannama ce makomarsu, kuma tir da wannan shimfixa



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 19

۞أَفَمَن يَعۡلَمُ أَنَّمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ ٱلۡحَقُّ كَمَنۡ هُوَ أَعۡمَىٰٓۚ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Yanzu wanda ya san cewa abin da aka saukar maka daga Ubangijinka gaskiya ne (zai zama) kamar wanda yake shi makaho ne? Lalle ma’abota hankali ne kaxai ke wa’azantuwa



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 20

ٱلَّذِينَ يُوفُونَ بِعَهۡدِ ٱللَّهِ وَلَا يَنقُضُونَ ٱلۡمِيثَٰقَ

(Su ne) waxanda suke cika alqawarin Allah kuma ba sa warware alqawarin



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 21

وَٱلَّذِينَ يَصِلُونَ مَآ أَمَرَ ٱللَّهُ بِهِۦٓ أَن يُوصَلَ وَيَخۡشَوۡنَ رَبَّهُمۡ وَيَخَافُونَ سُوٓءَ ٱلۡحِسَابِ

Waxanda kuma suke sadar da abin da Allah Ya yi umarni a sadar da shi (na zumunci), suke kuma tsoron Ubangijinsu, kuma suke tsoron mummunan hisabi



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 22

وَٱلَّذِينَ صَبَرُواْ ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ رَبِّهِمۡ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنفَقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ سِرّٗا وَعَلَانِيَةٗ وَيَدۡرَءُونَ بِٱلۡحَسَنَةِ ٱلسَّيِّئَةَ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عُقۡبَى ٱلدَّارِ

Waxanda kuma suka yi haquri don neman yardar Ubangijnsu, suka kuma tsai da salla, kuma suka ciyar daga abin da Muka arzuta su da shi a voye da sarari, suke kuma ingije mummunan aiki da kyakkyawa, waxannan suna da (kyakkyawar) makoma ta gidan (Aljanna)



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 23

جَنَّـٰتُ عَدۡنٖ يَدۡخُلُونَهَا وَمَن صَلَحَ مِنۡ ءَابَآئِهِمۡ وَأَزۡوَٰجِهِمۡ وَذُرِّيَّـٰتِهِمۡۖ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَدۡخُلُونَ عَلَيۡهِم مِّن كُلِّ بَابٖ

Gidajen Aljanna na dawwama, za su shiga su da waxanda suka kyautata (aiki) daga iyayensu da matansu da kuma zuriyarsu; mala’iku kuma za su riqa shigowa wurinsu ta kowace qofa



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 24

سَلَٰمٌ عَلَيۡكُم بِمَا صَبَرۡتُمۡۚ فَنِعۡمَ عُقۡبَى ٱلدَّارِ

(Suna ce musu): “Aminci ya tabbata a gare ku saboda haqurin da kuka yi. To madalla da gida na qarshe (watau Aljanna)”



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 25

وَٱلَّذِينَ يَنقُضُونَ عَهۡدَ ٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ مِيثَٰقِهِۦ وَيَقۡطَعُونَ مَآ أَمَرَ ٱللَّهُ بِهِۦٓ أَن يُوصَلَ وَيُفۡسِدُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمُ ٱللَّعۡنَةُ وَلَهُمۡ سُوٓءُ ٱلدَّارِ

Waxanda kuma suke warware alqawarin Allah bayan sun qulla shi, suke kuma yanke abin da Allah Ya yi umarni a sadar da shi, kuma suke varna a bayan qasa, waxannan la’ana ta tabbata a gare su kuma suna da (sakamakon) mummunan gida (shi ne Jahannama)



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 26

ٱللَّهُ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ وَفَرِحُواْ بِٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا فِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِلَّا مَتَٰعٞ

Allah ne Yake shimfixa arziki ga wanda Ya ga dama, Yake kuma quntatawa (ga wanda Ya ga dama. (Kafirai) kuma sun yi farin ciki da rayuwar duniya, rayuwar duniya kuwa ba komai ba ce illa xan jin daxi kaxan dangane da na lahira



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 27

وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡهِ ءَايَةٞ مِّن رَّبِّهِۦۚ قُلۡ إِنَّ ٱللَّهَ يُضِلُّ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِيٓ إِلَيۡهِ مَنۡ أَنَابَ

Waxanda suka kafirta kuma suna cewa: “Me ya hana a saukar masa da aya daga Ubangijinsa?” Ka ce: “Lalle Allah Yana vatar da wanda Ya ga dama, Yana kuma shiryar da wanda ya koma gare Shi



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 28

ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَتَطۡمَئِنُّ قُلُوبُهُم بِذِكۡرِ ٱللَّهِۗ أَلَا بِذِكۡرِ ٱللَّهِ تَطۡمَئِنُّ ٱلۡقُلُوبُ

“(Su ne) waxanda suka yi imani, zukatansu kuma suna nutsuwa da ambaton Allah. Ku saurara, da ambaton Allah ne zukata suke nutsuwa



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 29

ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ طُوبَىٰ لَهُمۡ وَحُسۡنُ مَـَٔابٖ

“Waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari, to farin ciki ya tabbata a gare su da kuma kyakkyawar makoma.”



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 30

كَذَٰلِكَ أَرۡسَلۡنَٰكَ فِيٓ أُمَّةٖ قَدۡ خَلَتۡ مِن قَبۡلِهَآ أُمَمٞ لِّتَتۡلُوَاْ عَلَيۡهِمُ ٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ وَهُمۡ يَكۡفُرُونَ بِٱلرَّحۡمَٰنِۚ قُلۡ هُوَ رَبِّي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ عَلَيۡهِ تَوَكَّلۡتُ وَإِلَيۡهِ مَتَابِ

Kamar haka Muka aiko ka cikin al’umma wadda tuni wasu al’ummun sun wuce kafinta, don ka karanta musu abin da Muka yi maka wahayinsa, alhali kuwa su suna kafirce wa Arrahamanu[1]. Ka ce: “Shi ne Ubangijina, babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, gare Shi kawai na dogara, kuma gare Shi kawai tubata take.”


1- Kafiran Quraishawa suna qyamar su siffanta Allah da suna Arrahman, watau Mai rahma, kamar yadda ya zo a cikin Suratul Furqan aya ta 60.