Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 114

يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَيَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَيَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَيُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ مِنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ

Suna yin imani da Allah da ranar qarshe, kuma suna umarni da kyakkyawan aiki, kuma suna hana mummuna, kuma suna hanzari wajen ayyukan alheri, waxannan kuwa suna cikin salihan bayi



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 115

وَمَا يَفۡعَلُواْ مِنۡ خَيۡرٖ فَلَن يُكۡفَرُوهُۗ وَٱللَّهُ عَلِيمُۢ بِٱلۡمُتَّقِينَ

Kuma duk abin da suka aikata na alheri, to ba za a hana musu ladansa ba. Kuma Allah Yana sane da masu taqawa



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 56

وَلَا تُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ بَعۡدَ إِصۡلَٰحِهَا وَٱدۡعُوهُ خَوۡفٗا وَطَمَعًاۚ إِنَّ رَحۡمَتَ ٱللَّهِ قَرِيبٞ مِّنَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kuma kada ku yi varna a bayan qasa bayan gyara ta, kuma ku bauta masa kuna masu tsoro da kwaxayi. Lalle rahamar Allah a kusa take da masu kyautatawa



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 26

۞لِّلَّذِينَ أَحۡسَنُواْ ٱلۡحُسۡنَىٰ وَزِيَادَةٞۖ وَلَا يَرۡهَقُ وُجُوهَهُمۡ قَتَرٞ وَلَا ذِلَّةٌۚ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Waxanda suka kyautata aiki suna da sakamako mafi kyau (watau Aljanna) da kuma qari[1]. Wani qunci da qasqanci kuma ba za su same su ba. Waxannan su ne ‘yan Aljanna; su masu dawwama ne a cikinta


1- Watau shi ne ganin Fuskar Allah () bayan shigarsu Aljanna. Duba Muslim #181.


Surah: Suratu Yusuf 

Ayah : 56

وَكَذَٰلِكَ مَكَّنَّا لِيُوسُفَ فِي ٱلۡأَرۡضِ يَتَبَوَّأُ مِنۡهَا حَيۡثُ يَشَآءُۚ نُصِيبُ بِرَحۡمَتِنَا مَن نَّشَآءُۖ وَلَا نُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kamar haka ne Muka kafa Yusufu a bayan qasa; yana zama a cikinta inda ya ga dama. Muna bayar da rahamarmu ga wanda Muka ga dama, ba kuwa za Mu tozarta ladan masu kyautatawa ba



Surah: Suratun Nahl

Ayah : 128

إِنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَواْ وَّٱلَّذِينَ هُم مُّحۡسِنُونَ

Lalle Allah Yana tare da waxanda suka yi taqawa da kuma waxanda suke masu kyautatawa ne



Surah: Suratul Mu’uminun

Ayah : 61

أُوْلَـٰٓئِكَ يُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِ وَهُمۡ لَهَا سَٰبِقُونَ

Waxannan su ne suke gaggawa ga ayyukan alheri, suna kuma masu rige-rige gare su