Surah: Suratul Baqara

Ayah : 109

وَدَّ كَثِيرٞ مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ لَوۡ يَرُدُّونَكُم مِّنۢ بَعۡدِ إِيمَٰنِكُمۡ كُفَّارًا حَسَدٗا مِّنۡ عِندِ أَنفُسِهِم مِّنۢ بَعۡدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمُ ٱلۡحَقُّۖ فَٱعۡفُواْ وَٱصۡفَحُواْ حَتَّىٰ يَأۡتِيَ ٱللَّهُ بِأَمۡرِهِۦٓۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

Da yawa daga cikin ma’abota littafi sun yi burin ina ma a ce su mayar da ku kafirai bayan imaninku, saboda hassada daga zukatansu, bayan kuma gaskiya ta bayyana a gare su. Don haka ku yi afuwa ku kawar da kai har sai Allah Ya zo da al’amarinsa. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 178

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡقِصَاصُ فِي ٱلۡقَتۡلَىۖ ٱلۡحُرُّ بِٱلۡحُرِّ وَٱلۡعَبۡدُ بِٱلۡعَبۡدِ وَٱلۡأُنثَىٰ بِٱلۡأُنثَىٰۚ فَمَنۡ عُفِيَ لَهُۥ مِنۡ أَخِيهِ شَيۡءٞ فَٱتِّبَاعُۢ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَأَدَآءٌ إِلَيۡهِ بِإِحۡسَٰنٖۗ ذَٰلِكَ تَخۡفِيفٞ مِّن رَّبِّكُمۡ وَرَحۡمَةٞۗ فَمَنِ ٱعۡتَدَىٰ بَعۡدَ ذَٰلِكَ فَلَهُۥ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, an wajabta muku qisasi dangane da waxanda aka kashe; xa da xa, bawa da bawa, mace da mace[1]. To duk wanda aka yafe masa qisasin xan uwansa, to sai ya bibiye shi ta hanyar da ta dace, shi kuma ya biya diyyar ta hanyar kyautatawa. Wannan (abin da aka ambata), sauqi ne da rahama daga wajen Ubangijinku. Don haka duk wanda ya qetare iyaka bayan haka, to yana da azaba mai raxaxi


1- Haka hukuncin yake yayin da namiji xa ya kashe ‘ya mace, ko mace ta kashe xa namiji. Amma idan magadan wanda aka kashe suka yafe, to babu zancen qisasi, sai a biya diyya kawai.


Surah: Suratul Baqara

Ayah : 237

وَإِن طَلَّقۡتُمُوهُنَّ مِن قَبۡلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ وَقَدۡ فَرَضۡتُمۡ لَهُنَّ فَرِيضَةٗ فَنِصۡفُ مَا فَرَضۡتُمۡ إِلَّآ أَن يَعۡفُونَ أَوۡ يَعۡفُوَاْ ٱلَّذِي بِيَدِهِۦ عُقۡدَةُ ٱلنِّكَاحِۚ وَأَن تَعۡفُوٓاْ أَقۡرَبُ لِلتَّقۡوَىٰۚ وَلَا تَنسَوُاْ ٱلۡفَضۡلَ بَيۡنَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٌ

Idan kuwa kun sake su ne tun kafin ku sadu da su, alhalin kuma kun yanka musu sadaki, to sai (ku bayar) da rabin abin da kuka yanka, sai fa in su matan sun yi afuwa ko kuma wanda a hannunsa igiyar aure take ya yi afuwa[1]; kuma ku yi afuwa shi ya fi kusa ga taqawa. Kuma kada ku manta da kyautatawar da take tsakaninku. Lalle Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne


1- Wanda igiyar aure take hannusa, shi ne mijin. Yana iya yafe wa, ya bar mata duk sadakin baki xaya.


Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 134

ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ فِي ٱلسَّرَّآءِ وَٱلضَّرَّآءِ وَٱلۡكَٰظِمِينَ ٱلۡغَيۡظَ وَٱلۡعَافِينَ عَنِ ٱلنَّاسِۗ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

(Su ne) waxanda suke ciyarwa a cikin halin yalwa da halin qunci, kuma masu voye fushi kuma masu yin afuwa ga mutane. Allah kuwa Yana son masu kyautatawa



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 159

فَبِمَا رَحۡمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ لِنتَ لَهُمۡۖ وَلَوۡ كُنتَ فَظًّا غَلِيظَ ٱلۡقَلۡبِ لَٱنفَضُّواْ مِنۡ حَوۡلِكَۖ فَٱعۡفُ عَنۡهُمۡ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُمۡ وَشَاوِرۡهُمۡ فِي ٱلۡأَمۡرِۖ فَإِذَا عَزَمۡتَ فَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُتَوَكِّلِينَ

To saboda rahama ta musamman daga Allah, sai ka zamo mai tausasawa gare su; in da kuwa ka kasance mai kaushin mu’amala, mai qeqasasshiyar zuciya ne, to da sun watse sun bar ka. To ka yi musu afuwa, kuma ka nema musu gafara, kuma ka nemi shawararsu cikin duk lamura; amma idan ka riga ka qulla niyya, to ka dogara ga Allah. Lalle Allah Yana son masu dogara a gare Shi



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 149

إِن تُبۡدُواْ خَيۡرًا أَوۡ تُخۡفُوهُ أَوۡ تَعۡفُواْ عَن سُوٓءٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَفُوّٗا قَدِيرًا

Idan har kuka bayyana wani alheri ko kuka voye shi ko kuma kuka yi afuwa game da wata cutarwa, to lalle Allah Ya kasance Mai yawan afuwa ne, Mai cikakken iko



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 13

فَبِمَا نَقۡضِهِم مِّيثَٰقَهُمۡ لَعَنَّـٰهُمۡ وَجَعَلۡنَا قُلُوبَهُمۡ قَٰسِيَةٗۖ يُحَرِّفُونَ ٱلۡكَلِمَ عَن مَّوَاضِعِهِۦ وَنَسُواْ حَظّٗا مِّمَّا ذُكِّرُواْ بِهِۦۚ وَلَا تَزَالُ تَطَّلِعُ عَلَىٰ خَآئِنَةٖ مِّنۡهُمۡ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنۡهُمۡۖ فَٱعۡفُ عَنۡهُمۡ وَٱصۡفَحۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Saboda yadda suke warware alqawarin da aka yi da su, sai Muka la’ance su, kuma Muka sanya zukatansu suka zamo qeqasassu; suna jirkita magana daga wurinta, kuma sun bar wani rabo na abin da aka yi musu wa’azi da shi. Kuma ba za ka gushe ba kana ganin ha’inci daga gare su, sai ‘yan kaxan daga cikinsu. To sai ka yi musu afuwa, kuma ka kawar da kai, lalle Allah Yana son masu kyautatawa



Surah: Suratu Yusuf 

Ayah : 92

قَالَ لَا تَثۡرِيبَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡيَوۡمَۖ يَغۡفِرُ ٱللَّهُ لَكُمۡۖ وَهُوَ أَرۡحَمُ ٱلرَّـٰحِمِينَ

Ya ce: “A yau babu wani zargi a kanku; Allah zai yafe muku, Shi ne Mafificin masu rahama



Surah: Suratul Hijr

Ayah : 85

وَمَا خَلَقۡنَا ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ وَمَا بَيۡنَهُمَآ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۗ وَإِنَّ ٱلسَّاعَةَ لَأٓتِيَةٞۖ فَٱصۡفَحِ ٱلصَّفۡحَ ٱلۡجَمِيلَ

Ba Mu kuma halicci sammai da qasa ba sai da gaskiya. Kuma lalle alqiyama tabbas mai zuwa ce, sai ka yi afuwa kyakkyawar afuwa[1]


1- Watau afuwar da babu cutarwa a cikinta sai dai kyautatawa ga wanda ya munana.


Surah: Suratun Nur

Ayah : 22

وَلَا يَأۡتَلِ أُوْلُواْ ٱلۡفَضۡلِ مِنكُمۡ وَٱلسَّعَةِ أَن يُؤۡتُوٓاْ أُوْلِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينَ وَٱلۡمُهَٰجِرِينَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ وَلۡيَعۡفُواْ وَلۡيَصۡفَحُوٓاْۗ أَلَا تُحِبُّونَ أَن يَغۡفِرَ ٱللَّهُ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٌ

Kuma kada masu hali da wadata daga cikinku su rantse a kan qin ba da (abin hannunsu) ga makusanta da miskinai da masu hijira saboda Allah. Su kuma yi afuwa su yafe. Shin ku ba kwa so ne Allah Ya gafarta muku? Allah kuwa Mai gafara ne, Mai jin qai[1]


1- Ayar tana magana ne a kan Abubakar () lokacin da ya yi rantsuwa ba zai ci gaba da taimaka wa xan innarsa Misxahu xan Usasa ba domin ya zama cikin masu kwaza qagen da aka yi wa Nana A’isha (RAH)..


Surah: Suratus Shura

Ayah : 37

وَٱلَّذِينَ يَجۡتَنِبُونَ كَبَـٰٓئِرَ ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡفَوَٰحِشَ وَإِذَا مَا غَضِبُواْ هُمۡ يَغۡفِرُونَ

Waxanda kuma suke nesantar manyan zunubai da munanansu, idan kuma sun yi fushi sukan yafe



Surah: Suratus Shura

Ayah : 40

وَجَزَـٰٓؤُاْ سَيِّئَةٖ سَيِّئَةٞ مِّثۡلُهَاۖ فَمَنۡ عَفَا وَأَصۡلَحَ فَأَجۡرُهُۥ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Kuma sakamakon mummunan (abu) shi ne mayar da mummuna kamarsa; to wanda ya yi afuwa ya kuma kyautata, to ladansa yana wurin Allah. Lalle Shi ba Ya son azzalumai



Surah: Suratus Shura

Ayah : 43

وَلَمَن صَبَرَ وَغَفَرَ إِنَّ ذَٰلِكَ لَمِنۡ عَزۡمِ ٱلۡأُمُورِ

Tabbas kuma wanda ya yi haquri ya yafe, to tabbas wannan yana daga muhimman al’amura[1]


1- Watau haqurinsa zai zame masa alheri, har ma da al’ummarsa gaba xaya.


Surah: Suratuz Zukhruf 

Ayah : 89

فَٱصۡفَحۡ عَنۡهُمۡ وَقُلۡ سَلَٰمٞۚ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ

To ka kawar musu kai, kuma ka ce: “Na kuvuta (daga haqqinku). Don haka ba da daxewa ba za ku sani.”



Surah: Suratul Jasiya

Ayah : 14

قُل لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ يَغۡفِرُواْ لِلَّذِينَ لَا يَرۡجُونَ أَيَّامَ ٱللَّهِ لِيَجۡزِيَ قَوۡمَۢا بِمَا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ

Ka ce da waxanda suka yi imani su yi gafara ga waxanda ba su damu da ni’imomi ko musibu na Allah ba[1], don Ya saka wa mutane game da irin abin da suka kasance suna aikatawa


1- Watau domin Allah zai saka wa bayinsa muminai masu haquri.


Surah: Suratut Taghabun

Ayah : 14

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّ مِنۡ أَزۡوَٰجِكُمۡ وَأَوۡلَٰدِكُمۡ عَدُوّٗا لَّكُمۡ فَٱحۡذَرُوهُمۡۚ وَإِن تَعۡفُواْ وَتَصۡفَحُواْ وَتَغۡفِرُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ

Ya ku waxanda suka yi imani, lalle wasu daga matanku da ‘ya’yanku maqiyanku ne[1], sai ku yi hattara da su. Idan kuma kuka yafe kuka kau da kai, to lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai


1- Watau waxanda suke qoqarin hana su xa’ar Allah ko su jefa su cikin savon Allah.