Surah: Suratul Baqara

Ayah : 85

ثُمَّ أَنتُمۡ هَـٰٓؤُلَآءِ تَقۡتُلُونَ أَنفُسَكُمۡ وَتُخۡرِجُونَ فَرِيقٗا مِّنكُم مِّن دِيَٰرِهِمۡ تَظَٰهَرُونَ عَلَيۡهِم بِٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِ وَإِن يَأۡتُوكُمۡ أُسَٰرَىٰ تُفَٰدُوهُمۡ وَهُوَ مُحَرَّمٌ عَلَيۡكُمۡ إِخۡرَاجُهُمۡۚ أَفَتُؤۡمِنُونَ بِبَعۡضِ ٱلۡكِتَٰبِ وَتَكۡفُرُونَ بِبَعۡضٖۚ فَمَا جَزَآءُ مَن يَفۡعَلُ ذَٰلِكَ مِنكُمۡ إِلَّا خِزۡيٞ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ يُرَدُّونَ إِلَىٰٓ أَشَدِّ ٱلۡعَذَابِۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ

Sannan sai ga ku, ku xin nan kuna kashe junanku, kuma kuna fitar da wata qungiya daga cikinku daga gidajensu, kuma kuna taimaka wa juna wajen cutar da su ta hanyar laifi da zalunci. Idan kuma sun zo muku suna kamammun yaqi sai ku fanshe su, alhali fitar da su haramun ne a gare ku. Yanzu kwa riqa yin imani da sashen Littafi kuma ku riqa kafircewa da wani sashen? To ba komai ne sakamakon wanda yake aikata haka daga cikinku ba face wani wulaqanci a rayuwar duniya, kuma ranar alqiyama a mayar da su zuwa ga mafi tsananin azaba, kuma Allah ba rafkananne ba ne game da abin da kuke aikatawa



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 184

أَيَّامٗا مَّعۡدُودَٰتٖۚ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوۡ عَلَىٰ سَفَرٖ فَعِدَّةٞ مِّنۡ أَيَّامٍ أُخَرَۚ وَعَلَى ٱلَّذِينَ يُطِيقُونَهُۥ فِدۡيَةٞ طَعَامُ مِسۡكِينٖۖ فَمَن تَطَوَّعَ خَيۡرٗا فَهُوَ خَيۡرٞ لَّهُۥۚ وَأَن تَصُومُواْ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ

Waxansu kwanaki ne qididdigaggu. To duk wanda ya kasance marar lafiya a cikinku ko a kan wata tafiya, to (idan ya sha azumi) sai ya rama a waxansu kwanakin na daban. Kuma waxanda za su yi azumi da wahala su ba da fansa ta ciyar da miskini; to duk wanda ya qara (a kan abincin miskini), to wannan alheri ne gare shi. Amma ku yi azumin shi ne ya fi muku alheri, in har kun kusance kuna sani



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 196

وَأَتِمُّواْ ٱلۡحَجَّ وَٱلۡعُمۡرَةَ لِلَّهِۚ فَإِنۡ أُحۡصِرۡتُمۡ فَمَا ٱسۡتَيۡسَرَ مِنَ ٱلۡهَدۡيِۖ وَلَا تَحۡلِقُواْ رُءُوسَكُمۡ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ ٱلۡهَدۡيُ مَحِلَّهُۥۚ فَمَن كَانَ مِنكُم مَّرِيضًا أَوۡ بِهِۦٓ أَذٗى مِّن رَّأۡسِهِۦ فَفِدۡيَةٞ مِّن صِيَامٍ أَوۡ صَدَقَةٍ أَوۡ نُسُكٖۚ فَإِذَآ أَمِنتُمۡ فَمَن تَمَتَّعَ بِٱلۡعُمۡرَةِ إِلَى ٱلۡحَجِّ فَمَا ٱسۡتَيۡسَرَ مِنَ ٱلۡهَدۡيِۚ فَمَن لَّمۡ يَجِدۡ فَصِيَامُ ثَلَٰثَةِ أَيَّامٖ فِي ٱلۡحَجِّ وَسَبۡعَةٍ إِذَا رَجَعۡتُمۡۗ تِلۡكَ عَشَرَةٞ كَامِلَةٞۗ ذَٰلِكَ لِمَن لَّمۡ يَكُنۡ أَهۡلُهُۥ حَاضِرِي ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Kuma ku cika aikin Hajji da umara domin Allah. To idan an tsare ku, sai ku gabatar da abin da ya sawwaqa na hadaya, kuma kada ku aske kawunanku har sai hadaya ta kai wurin yankanta. To wanda ya kasance a cikinku mara lafiya ko akwai wata cuta a kansa, (idan yayi aski) to sai ya yi fidiya ta (hanyar) yin azumi ko sadaqa ko yanka[1]. Idan kuwa kun amintu, to duk wanda ya yi tamattu’i da yin umara tare da Hajji, to sai ya yanka abin da ya sawwaqa na hadaya; amma wanda bai samu ba, sai ya yi azumin kwana uku a lokacin aikin Hajji, da kuma na kwana bakwai idan kun dawo gida. Waxannan kwana goma ke nan cikakku. Wannan hukuncin yana ga wanda iyalinsa ba sa cikin hurumin Makka ne. Kuma ku kiyaye dokokin Allah, ku sani cewa, lalle Allah Mai tsananin uquba ne


1- Watau ya yi azumi na kwana uku, ko ya ciyar da miskinai shida, kowanne ya ba shi rabin mudu ko ya yanka akuya.


Surah: Suratul Baqara

Ayah : 229

ٱلطَّلَٰقُ مَرَّتَانِۖ فَإِمۡسَاكُۢ بِمَعۡرُوفٍ أَوۡ تَسۡرِيحُۢ بِإِحۡسَٰنٖۗ وَلَا يَحِلُّ لَكُمۡ أَن تَأۡخُذُواْ مِمَّآ ءَاتَيۡتُمُوهُنَّ شَيۡـًٔا إِلَّآ أَن يَخَافَآ أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ ٱللَّهِۖ فَإِنۡ خِفۡتُمۡ أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ ٱللَّهِ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡهِمَا فِيمَا ٱفۡتَدَتۡ بِهِۦۗ تِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِ فَلَا تَعۡتَدُوهَاۚ وَمَن يَتَعَدَّ حُدُودَ ٱللَّهِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Saki sau biyu ne (xaya bayan xaya), don haka ko dai ya riqe ta ta hanyar da aka sani, ko kuma ya sake ta tare da kyautatawa. Kuma bai halatta gare ku ba ku karvi wani abu daga cikin abin da kuka ba su, sai fa idan su (ma’aurata) biyu sun ji tsoron ba za su tsayar da dokokin Allah ba. To idan kuka ji tsoron ba za su tsayar da dokokin Allah ba, to babu laifi a gare su game da abin da ta fanshi kanta da shi[1]. Waxannan iyakokin Allah ne, kada ku qetare su, kuma duk wanda ya qetare iyakokin Allah, to waxannan su ne azzalumai


1- Idan mace ta ga ba za ta iya zama da mijinta ba, to babu laifi ta mayar masa abin da ya kashe, sai su rabu. Wannan shi ne: Khul’u.


Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 91

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَمَاتُواْ وَهُمۡ كُفَّارٞ فَلَن يُقۡبَلَ مِنۡ أَحَدِهِم مِّلۡءُ ٱلۡأَرۡضِ ذَهَبٗا وَلَوِ ٱفۡتَدَىٰ بِهِۦٓۗ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ وَمَا لَهُم مِّن نَّـٰصِرِينَ

Lalle waxanda suka kafirta, kuma suka mutu alhali suna kafirai, to ba za a tava karvar cikin qasa na zinare daga xayansu ba, ko da zai fanshi kansa da shi. Waxannan suna da wata azaba mai raxaxi kuma ba su da wasu mataimaka



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 36

إِنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡ أَنَّ لَهُم مَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا وَمِثۡلَهُۥ مَعَهُۥ لِيَفۡتَدُواْ بِهِۦ مِنۡ عَذَابِ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ مَا تُقُبِّلَ مِنۡهُمۡۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ

Lalle waxanda suka kafirta, in da a ce duk abin da yake ban qasa gaba xaya nasu ne, haxe kuma da wani kamarsa, domin su fanshi kansu da shi daga azabar ranar tashin alqiyama, da ba za a karva daga gare su ba; kuma suna da azaba mai raxaxi



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 54

وَلَوۡ أَنَّ لِكُلِّ نَفۡسٖ ظَلَمَتۡ مَا فِي ٱلۡأَرۡضِ لَٱفۡتَدَتۡ بِهِۦۗ وَأَسَرُّواْ ٱلنَّدَامَةَ لَمَّا رَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَۖ وَقُضِيَ بَيۡنَهُم بِٱلۡقِسۡطِ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ

Da a ce kowane rai da ya yi zalunci ya mallaki duk abin da yake bayan qasa, to lalle da ya fanshi kansa da shi. Suka kuwa voye nadama a lokacin da suka ga azaba; an kuma yi hukunci tsakaninsu na adalci; ba kuma za a zalunce su ba



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 18

لِلَّذِينَ ٱسۡتَجَابُواْ لِرَبِّهِمُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ وَٱلَّذِينَ لَمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَهُۥ لَوۡ أَنَّ لَهُم مَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا وَمِثۡلَهُۥ مَعَهُۥ لَٱفۡتَدَوۡاْ بِهِۦٓۚ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ سُوٓءُ ٱلۡحِسَابِ وَمَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمِهَادُ

Waxanda suka amsa (kiran) Ubangijinsu suna da kyakkyawar (makoma). Waxanda kuwa ba su amsa ba, da a ce duk abin da ke qasa gaba xaya tare kuma da wani kwatankwacinsa duka nasu ne, to da lalle sun fanshi kansu da shi (ranar alqiyama). Waxannan suna da mummunan hisabi, kuma Jahannama ce makomarsu, kuma tir da wannan shimfixa



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 107

وَفَدَيۡنَٰهُ بِذِبۡحٍ عَظِيمٖ

Muka kuma fanshe shi da abin yankawa mai girma



Surah: Suratuz Zumar

Ayah : 47

وَلَوۡ أَنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُواْ مَا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا وَمِثۡلَهُۥ مَعَهُۥ لَٱفۡتَدَوۡاْ بِهِۦ مِن سُوٓءِ ٱلۡعَذَابِ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ وَبَدَا لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مَا لَمۡ يَكُونُواْ يَحۡتَسِبُونَ

Da a ce waxanda suka yi zalunci za su mallaki abin da yake bayan qasa baki xaya har da wani kamarsa a tare da shi, to da sun fanshi kansu da shi saboda munin azabar ranar lahira. Abin da kuma ba su kasance suna tsammani daga Allah ba ya bayyana a gare su



Surah: Suratu Muhammad

Ayah : 4

فَإِذَا لَقِيتُمُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فَضَرۡبَ ٱلرِّقَابِ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَثۡخَنتُمُوهُمۡ فَشُدُّواْ ٱلۡوَثَاقَ فَإِمَّا مَنَّۢا بَعۡدُ وَإِمَّا فِدَآءً حَتَّىٰ تَضَعَ ٱلۡحَرۡبُ أَوۡزَارَهَاۚ ذَٰلِكَۖ وَلَوۡ يَشَآءُ ٱللَّهُ لَٱنتَصَرَ مِنۡهُمۡ وَلَٰكِن لِّيَبۡلُوَاْ بَعۡضَكُم بِبَعۡضٖۗ وَٱلَّذِينَ قُتِلُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَلَن يُضِلَّ أَعۡمَٰلَهُمۡ

To idan kuka haxu da waxanda suka kafirta sai ku sare wuyoyinsu har lokacin da kuka yi musu jina-jina, sai ku tsananta xauri[1]; to bayan nan ko dai yafewa su tafi bayan (kun ribace su), ko kuma karvar fansa har sai yaqi ya lafa. Wannan abu haka yake, da kuma Allah Ya ga dama da Ya yi nasara a kansu (ko da ba yaqi), sai dai kuma (Ya yi haka ne) don Ya jarrabi shashinku da shashi. Waxanda kuwa aka kashe su a hanyar Allah, to ba zai tava lalata ayyukansa ba


1- Watau Musulmi su kama su a matsayin ribatattun yaqi.


Surah: Suratul Hadid

Ayah : 15

فَٱلۡيَوۡمَ لَا يُؤۡخَذُ مِنكُمۡ فِدۡيَةٞ وَلَا مِنَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْۚ مَأۡوَىٰكُمُ ٱلنَّارُۖ هِيَ مَوۡلَىٰكُمۡۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

“To a yau ba za a karvi wata fansa ba daga gare ku da kuma daga waxanda suka kafirta. Makomarku wuta; ita ce ta kamace ku, makoma kuwa ta munana.”



Surah: Suratul Ma’arij

Ayah : 11

يُبَصَّرُونَهُمۡۚ يَوَدُّ ٱلۡمُجۡرِمُ لَوۡ يَفۡتَدِي مِنۡ عَذَابِ يَوۡمِئِذِۭ بِبَنِيهِ

(Alhali kuma) ana nuna musu junansu. Mai laifi ya riqa burin ina ma zai fanshi kansa daga azabar wannan rana da ‘ya’yansa