وَلَيۡسَتِ ٱلتَّوۡبَةُ لِلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلسَّيِّـَٔاتِ حَتَّىٰٓ إِذَا حَضَرَ أَحَدَهُمُ ٱلۡمَوۡتُ قَالَ إِنِّي تُبۡتُ ٱلۡـَٰٔنَ وَلَا ٱلَّذِينَ يَمُوتُونَ وَهُمۡ كُفَّارٌۚ أُوْلَـٰٓئِكَ أَعۡتَدۡنَا لَهُمۡ عَذَابًا أَلِيمٗا
Kuma ba a karvar tuba daga waxanda suke aikata munanan ayyuka har sai lokacin da mutuwa ta zo wa xayansu, sai ya ce: “Ni kam na tuba yanzu;” kuma ba a karvar tuban waxanda suke mutuwa alhalin suna kafirai. Waxannan Mun yi musu tanadin azaba mai raxaxi
مَّن يَشۡفَعۡ شَفَٰعَةً حَسَنَةٗ يَكُن لَّهُۥ نَصِيبٞ مِّنۡهَاۖ وَمَن يَشۡفَعۡ شَفَٰعَةٗ سَيِّئَةٗ يَكُن لَّهُۥ كِفۡلٞ مِّنۡهَاۗ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ مُّقِيتٗا
Duk wanda ya yi (ma wani) kyakkyawar alfarma, zai samu rabonsa na lada daga gare ta; kuma duk wanda ya yi wa wani mummunar alfarma, zai samu rabonsa na zunubi daga gare ta. Kuma Allah Ya kasance Mai kiyaye komai ne[1]
1- Watau zai yi wa kowa sakamako gwargwadon aikinsa mai kyau ko mummuna.
لَّيۡسَ بِأَمَانِيِّكُمۡ وَلَآ أَمَانِيِّ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِۗ مَن يَعۡمَلۡ سُوٓءٗا يُجۡزَ بِهِۦ وَلَا يَجِدۡ لَهُۥ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلِيّٗا وَلَا نَصِيرٗا
(Al’amarin) ba wai ya dangaci burace-buracenku ba ne, ba kuma burace-buracen Ma’abota Littafi ba ne. Duk wanda ya aikata mummunan aiki, to za a saka masa da shi, kuma ba zai sami wani masoyi ko mai taimako ba Allah ba
مَن جَآءَ بِٱلۡحَسَنَةِ فَلَهُۥ عَشۡرُ أَمۡثَالِهَاۖ وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَلَا يُجۡزَىٰٓ إِلَّا مِثۡلَهَا وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Wanda ya zo da kyakkyawan aiki xaya, to yana da ninkin ladansa goma; wanda kuwa ya zo da mummuna xaya, to ba za a saka masa ba sai daidai da shi, ba kuma za a zalunce su ba
وَٱلَّذِينَ كَسَبُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ جَزَآءُ سَيِّئَةِۭ بِمِثۡلِهَا وَتَرۡهَقُهُمۡ ذِلَّةٞۖ مَّا لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِنۡ عَاصِمٖۖ كَأَنَّمَآ أُغۡشِيَتۡ وُجُوهُهُمۡ قِطَعٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِ مُظۡلِمًاۚ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ
Waxanda kuma suka yi mummunan aiki, to sakamakon mummunan aiki irinsa ne, kuma qasqanci zai lulluve su; ba su da wani mai kare su daga (azabar) Allah; kamar dai an lulluve fuskokinsu ne da wani yanki na dare mai duhu qirin. Waxannan su ne ‘yan wuta; su kuma masu dawwama ne a cikinta
وَٱلَّذِينَ يَنقُضُونَ عَهۡدَ ٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ مِيثَٰقِهِۦ وَيَقۡطَعُونَ مَآ أَمَرَ ٱللَّهُ بِهِۦٓ أَن يُوصَلَ وَيُفۡسِدُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمُ ٱللَّعۡنَةُ وَلَهُمۡ سُوٓءُ ٱلدَّارِ
Waxanda kuma suke warware alqawarin Allah bayan sun qulla shi, suke kuma yanke abin da Allah Ya yi umarni a sadar da shi, kuma suke varna a bayan qasa, waxannan la’ana ta tabbata a gare su kuma suna da (sakamakon) mummunan gida (shi ne Jahannama)
فَأَصَابَهُمۡ سَيِّـَٔاتُ مَا عَمِلُواْ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Sai (sakamakon) mummunan abin da suka aikata ya same su, kuma abin da suke yi wa izgili ya rutsa da su
وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَكُبَّتۡ وُجُوهُهُمۡ فِي ٱلنَّارِ هَلۡ تُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Waxanda kuwa suka zo da mummunan (aiki), to an kifar da fuskokinsu cikin wuta, to ba za a saka muku ba sai da irin abin da kuka zamanto kuna aikatawa
مَن جَآءَ بِٱلۡحَسَنَةِ فَلَهُۥ خَيۡرٞ مِّنۡهَاۖ وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَلَا يُجۡزَى ٱلَّذِينَ عَمِلُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ إِلَّا مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ
Duk wanda ya zo da kyakkyawan aiki, to yana da (lada) fiye da aikinsa; wanda kuma ya zo da mummunan aiki, to ba za a saka wa waxanda suka aikata munanan ayyuka ba face daidai da abin da suka kasance suna aikatawa
ثُمَّ كَانَ عَٰقِبَةَ ٱلَّذِينَ أَسَـٰٓـُٔواْ ٱلسُّوٓأَىٰٓ أَن كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ وَكَانُواْ بِهَا يَسۡتَهۡزِءُونَ
Sannan kuma qarshen waxanda suka munana (ayyukansu) ya kasance mummunan (sakamako), don sun qaryata ayoyin Allah, kuma sun kasance suna yin izgili gare su
مَن كَانَ يُرِيدُ ٱلۡعِزَّةَ فَلِلَّهِ ٱلۡعِزَّةُ جَمِيعًاۚ إِلَيۡهِ يَصۡعَدُ ٱلۡكَلِمُ ٱلطَّيِّبُ وَٱلۡعَمَلُ ٱلصَّـٰلِحُ يَرۡفَعُهُۥۚ وَٱلَّذِينَ يَمۡكُرُونَ ٱلسَّيِّـَٔاتِ لَهُمۡ عَذَابٞ شَدِيدٞۖ وَمَكۡرُ أُوْلَـٰٓئِكَ هُوَ يَبُورُ
Wanda ya zamanto yana nufin xaukaka, to xaukaka gaba xayanta ta Allah ce. Daxaxan kalmomi[1] zuwa wurinsa suke hawa, kyakkyawan aiki kuwa shi yake xaukaka shi. Waxanda kuwa suke shirya makirci suna da (sakamakon) azaba mai tsanani, kuma makircin waxannan shi ne yake lalacewa
1- Watau kamar kalmar shahada da karatun Alqur’ani da ambaton Allah.
هَٰذَاۚ وَإِنَّ لِلطَّـٰغِينَ لَشَرَّ مَـَٔابٖ
Wannan (shi ne sakamakon masu taqawa). Kuma lalle masu xagawa tabbas suna da mummunar makoma
مَنۡ عَمِلَ سَيِّئَةٗ فَلَا يُجۡزَىٰٓ إِلَّا مِثۡلَهَاۖ وَمَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَأُوْلَـٰٓئِكَ يَدۡخُلُونَ ٱلۡجَنَّةَ يُرۡزَقُونَ فِيهَا بِغَيۡرِ حِسَابٖ
“Wanda ya aikata wani mummunan aiki, to ba za a saka masa ba sai da kwatankwacinsa, wanda kuwa ya aikata wani kyakkyawan aiki, namiji ne ko mace alhali shi yana mumini, to waxannan za su shiga Aljanna, a riqa arzuta su a cikinta ba tare da lissafi ba
يَوۡمَ لَا يَنفَعُ ٱلظَّـٰلِمِينَ مَعۡذِرَتُهُمۡۖ وَلَهُمُ ٱللَّعۡنَةُ وَلَهُمۡ سُوٓءُ ٱلدَّارِ
Ranar da hanzarin azzulamai ba zai amfane su ba; la’ana kuma ta tabbata a kansu, suna kuma da mummunan gida
وَجَزَـٰٓؤُاْ سَيِّئَةٖ سَيِّئَةٞ مِّثۡلُهَاۖ فَمَنۡ عَفَا وَأَصۡلَحَ فَأَجۡرُهُۥ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Kuma sakamakon mummunan (abu) shi ne mayar da mummuna kamarsa; to wanda ya yi afuwa ya kuma kyautata, to ladansa yana wurin Allah. Lalle Shi ba Ya son azzalumai
وَبَدَا لَهُمۡ سَيِّـَٔاتُ مَا عَمِلُواْ وَحَاقَ بِهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ
Kuma irin munanan ayyukan da suka aikata suka bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance suna yi wa izgili ya saukar musu
وَيُعَذِّبَ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتِ وَٱلۡمُشۡرِكِينَ وَٱلۡمُشۡرِكَٰتِ ٱلظَّآنِّينَ بِٱللَّهِ ظَنَّ ٱلسَّوۡءِۚ عَلَيۡهِمۡ دَآئِرَةُ ٱلسَّوۡءِۖ وَغَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡ وَلَعَنَهُمۡ وَأَعَدَّ لَهُمۡ جَهَنَّمَۖ وَسَآءَتۡ مَصِيرٗا
Ya kuma azabtar da munafukai maza da mata, da mushirikai maza da mata, masu munana zato ga Allah. Mummunar azaba ta koma a kansu; kuma Allah Ya yi fushi da su, Ya kuma la’ance su, Ya kuma tanadar musu Jahannama; makoma kuwa ta munana