وَزَكَرِيَّا وَيَحۡيَىٰ وَعِيسَىٰ وَإِلۡيَاسَۖ كُلّٞ مِّنَ ٱلصَّـٰلِحِينَ
Da Zakariyya da Yahaya da Isa da Iliyasu; kowanne daga cikinsu yana cikin salihan bayi
Share :
وَإِنَّ إِلۡيَاسَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ
Kuma lalle Ilyasu tabbas yana daga cikin manzanni
إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِۦٓ أَلَا تَتَّقُونَ
Lokacin da ya ce da mutanensa: “Yanzu ba za ku kiyaye dokokin (Allah) ba?
أَتَدۡعُونَ بَعۡلٗا وَتَذَرُونَ أَحۡسَنَ ٱلۡخَٰلِقِينَ
“Yanzu kwa riqa bauta wa (gunkin) Ba’alu ku riqa barin Mafi iya kyautata halitta?
ٱللَّهَ رَبَّكُمۡ وَرَبَّ ءَابَآئِكُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ
“(Wato) Allah Ubangijinku kuma Ubangijin iyayenku na farko?”
فَكَذَّبُوهُ فَإِنَّهُمۡ لَمُحۡضَرُونَ
Sai suka qaryata shi, to don haka, lalle za a halarto da su (wuta)
إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ
Sai dai bayin Allah waxanda aka tsarkake
وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ
Muka kuma bar (kyakkyawan yabo) a gare shi ga ‘yan baya
سَلَٰمٌ عَلَىٰٓ إِلۡ يَاسِينَ
Aminci ya tabbata ga Ilyasu
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Lalle Mu kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa
إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Lalle shi yana daga bayinmu muminai