يَوۡمَ تُبَدَّلُ ٱلۡأَرۡضُ غَيۡرَ ٱلۡأَرۡضِ وَٱلسَّمَٰوَٰتُۖ وَبَرَزُواْ لِلَّهِ ٱلۡوَٰحِدِ ٱلۡقَهَّارِ
(Ka tuna) ranar da za a sake qasa ba (wannan) qasar ba, da kuma sammai (ba waxannan samman ba. Halittu) kuma suka fito (daga cikin qasa) a gaban Allah Makaxaici, Mai rinjaye
وَيَوۡمَ نُسَيِّرُ ٱلۡجِبَالَ وَتَرَى ٱلۡأَرۡضَ بَارِزَةٗ وَحَشَرۡنَٰهُمۡ فَلَمۡ نُغَادِرۡ مِنۡهُمۡ أَحَدٗا
Kuma ka tuna ranar da za Mu tafiyar da duwatsu kuma ka ga qasa a baje (ba tudu ba rafi), Mu kuma tattara su (gaba xaya), ba Mu bar xaya daga cikinsu ba
إِنَّا نَحۡنُ نَرِثُ ٱلۡأَرۡضَ وَمَنۡ عَلَيۡهَا وَإِلَيۡنَا يُرۡجَعُونَ
Lalle Mu ne za Mu gaje qasa da wanda yake bayanta kuma gare Mu ne za a komar da su
وَيَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡجِبَالِ فَقُلۡ يَنسِفُهَا رَبِّي نَسۡفٗا
Suna kuma tambayar ka game da duwatsu, to ka ce (da su): “Ubangijina zai niqe su tilis
فَيَذَرُهَا قَاعٗا صَفۡصَفٗا
“Sannan Ya bar ta (wato qasar) fili fetal
لَّا تَرَىٰ فِيهَا عِوَجٗا وَلَآ أَمۡتٗا
“Ba za ka ga wani kwari ko tudu a kanta ba.”
أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱللَّهَ سَخَّرَ لَكُم مَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَٱلۡفُلۡكَ تَجۡرِي فِي ٱلۡبَحۡرِ بِأَمۡرِهِۦ وَيُمۡسِكُ ٱلسَّمَآءَ أَن تَقَعَ عَلَى ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِٱلنَّاسِ لَرَءُوفٞ رَّحِيمٞ
Shin ba ka ga cewa Allah Ya hore muku abin da yake cikin qasa, da kuma jiragen ruwa da suke gudu a cikin kogi da umarninsa, kuma Yake riqe sama don kada ta faxo a kan qasa, sai da izininsa? Lalle Allah Mai tausayi ne, Mai rahama ga mutane
وَتَرَى ٱلۡجِبَالَ تَحۡسَبُهَا جَامِدَةٗ وَهِيَ تَمُرُّ مَرَّ ٱلسَّحَابِۚ صُنۡعَ ٱللَّهِ ٱلَّذِيٓ أَتۡقَنَ كُلَّ شَيۡءٍۚ إِنَّهُۥ خَبِيرُۢ بِمَا تَفۡعَلُونَ
Kuma za ka ga duwatsu ka zaci a tsaye suke cak, alhali kuwa su suna tafiya ne irin tafiyar gizagizai. Aikin Allah kenan wanda Ya kyautata halittar kowane irin abu. Lalle Shi Masanin abin da kuke aikatawa ne
وَمَا قَدَرُواْ ٱللَّهَ حَقَّ قَدۡرِهِۦ وَٱلۡأَرۡضُ جَمِيعٗا قَبۡضَتُهُۥ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَٱلسَّمَٰوَٰتُ مَطۡوِيَّـٰتُۢ بِيَمِينِهِۦۚ سُبۡحَٰنَهُۥ وَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ
Ba su kuma girmama Allah ba kamar yadda Ya cancanta a girmama Shi, alhali qasa ga baki xayanta tana cikin Damqarsa ranar alqiyama, sammai kuma suna nannaxe a Hannunsa na dama. Tsarki ya tabbata a gare Shi, Ya kuma xaukaka game da abin da suke yin shirka (da shi)
وَنُفِخَ فِي ٱلصُّورِ فَصَعِقَ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا مَن شَآءَ ٱللَّهُۖ ثُمَّ نُفِخَ فِيهِ أُخۡرَىٰ فَإِذَا هُمۡ قِيَامٞ يَنظُرُونَ
Aka kuma busa qaho, sai duk abin da yake cikin sammai da qasa ya halaka sai wanda Allah Ya ga dama; sannan aka sake yin wata busar, sai ga su a tsaye suna jiran tsammani
وَأَشۡرَقَتِ ٱلۡأَرۡضُ بِنُورِ رَبِّهَا وَوُضِعَ ٱلۡكِتَٰبُ وَجِاْيٓءَ بِٱلنَّبِيِّـۧنَ وَٱلشُّهَدَآءِ وَقُضِيَ بَيۡنَهُم بِٱلۡحَقِّ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ
Qasa kuma ta yi haske da hasken Ubangijinta, aka kuma ajiye takardu (na ayyuka), kuma aka zo da annabawa da masu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakaninsu da gaskiya, ba kuma za a zalunce su ba
يَوۡمَ تَشَقَّقُ ٱلۡأَرۡضُ عَنۡهُمۡ سِرَاعٗاۚ ذَٰلِكَ حَشۡرٌ عَلَيۡنَا يَسِيرٞ
A ranar da qasa za ta tsattsage musu (su fito) da gaggawa. Wannan tattarawa ce mai sauqi a gare Mu
إِذَا رُجَّتِ ٱلۡأَرۡضُ رَجّٗا
Idan aka girgiza qasa girgizawa
وَبُسَّتِ ٱلۡجِبَالُ بَسّٗا
Aka kuma dandaqe duwatsu dandaqewa
فَكَانَتۡ هَبَآءٗ مُّنۢبَثّٗا
Suka zama qura abar sheqewa
وَحُمِلَتِ ٱلۡأَرۡضُ وَٱلۡجِبَالُ فَدُكَّتَا دَكَّةٗ وَٰحِدَةٗ
Aka kuma xaga qasa da duwatsu sai aka dandaqe su dandaqewa baki xaya
يَوۡمَ تَرۡجُفُ ٱلۡأَرۡضُ وَٱلۡجِبَالُ وَكَانَتِ ٱلۡجِبَالُ كَثِيبٗا مَّهِيلًا
A ranar da qasa da duwatsu za su girgiza, duwatsun kuma su kasance rairayi tilis
وَسُيِّرَتِ ٱلۡجِبَالُ فَكَانَتۡ سَرَابًا
Aka kuma tafiyar da duwatsu sai suka zama kawalwalniya
وَإِذَا ٱلۡأَرۡضُ مُدَّتۡ
Kuma idan qasa aka miqe ta
وَأَلۡقَتۡ مَا فِيهَا وَتَخَلَّتۡ
Ta kuma jefar da abin da yake cikinta ta wofinta[1]
1- Watau cikinta ya koma fayau babu sauran wani abu.
وَأَذِنَتۡ لِرَبِّهَا وَحُقَّتۡ
Ta kuma saurari Ubangijinta kuma ya wajaba (ta saurara)
كَلَّآۖ إِذَا دُكَّتِ ٱلۡأَرۡضُ دَكّٗا دَكّٗا
Ba haka ne ba, idan aka girgiza qasa matuqar girgiza
إِذَا زُلۡزِلَتِ ٱلۡأَرۡضُ زِلۡزَالَهَا
Idan aka girgiza qasa matuqar girgiza ta
وَأَخۡرَجَتِ ٱلۡأَرۡضُ أَثۡقَالَهَا
Qasar kuma ta fitar da nauyaye-nauyayenta[1]
1- Watau ta fitar da mutanen da ke cikinta da sauran ma’adanan qarqashinta.
وَقَالَ ٱلۡإِنسَٰنُ مَا لَهَا
Mutum kuma ya ce: “Me ya same ta?”
يَوۡمَئِذٖ تُحَدِّثُ أَخۡبَارَهَا
A wannan ranar ne za ta ba da labaranta[1]
1- Watau ayyukan da aka yi a kanta masu kyau da munana.
بِأَنَّ رَبَّكَ أَوۡحَىٰ لَهَا
Don Ubangijinka Ya umarce ta (da yin haka)