Surah: Suratul An’am

Ayah : 152

وَلَا تَقۡرَبُواْ مَالَ ٱلۡيَتِيمِ إِلَّا بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ أَشُدَّهُۥۚ وَأَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ وَٱلۡمِيزَانَ بِٱلۡقِسۡطِۖ لَا نُكَلِّفُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَاۖ وَإِذَا قُلۡتُمۡ فَٱعۡدِلُواْ وَلَوۡ كَانَ ذَا قُرۡبَىٰۖ وَبِعَهۡدِ ٱللَّهِ أَوۡفُواْۚ ذَٰلِكُمۡ وَصَّىٰكُم بِهِۦ لَعَلَّكُمۡ تَذَكَّرُونَ

“Kuma kada ku kusanci dukiyar maraya sai da kyakkyawar niyya, har sai qarfinsa ya kawo; kuma ku cika ma’auni na mudu da na nauyi bisa adalci; ba ma xora wa rai sai abin da zai iya. Kuma idan za ku yi magana to ku yi adalci, ko da kuwa a kan xan’uwa ne na kusa; kuma lalle ku cika alqawarin Allah. Wannan ne abin da (Allah) Yake yi muku wasicci da shi, don ku wa’azantu.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 85

وَإِلَىٰ مَدۡيَنَ أَخَاهُمۡ شُعَيۡبٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥۖ قَدۡ جَآءَتۡكُم بَيِّنَةٞ مِّن رَّبِّكُمۡۖ فَأَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ وَٱلۡمِيزَانَ وَلَا تَبۡخَسُواْ ٱلنَّاسَ أَشۡيَآءَهُمۡ وَلَا تُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ بَعۡدَ إِصۡلَٰحِهَاۚ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Kuma (Mun) aika wa mutanen Madyana xan’uwansu Shu’aibu, ya ce: “Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi, haqiqa hujja ta zo muku daga Ubangijinku; don haka ku riqa cika mudu, kuma ku (kiyaye) ma’auni, kuma kada ku tauye wa mutane abubuwansu, kuma kada ku yi varna a bayan qasa bayan an gyara ta. Wannan shi ne mafi alheri a gare ku in kun kasance muminai



Surah: Suratu Hud

Ayah : 84

۞وَإِلَىٰ مَدۡيَنَ أَخَاهُمۡ شُعَيۡبٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥۖ وَلَا تَنقُصُواْ ٱلۡمِكۡيَالَ وَٱلۡمِيزَانَۖ إِنِّيٓ أَرَىٰكُم بِخَيۡرٖ وَإِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٖ مُّحِيطٖ

Kuma Mun aiko wa (mutanen) Madyana xan’uwansu Shu’aibu, ya ce: “Ya ku mutanena, ku bauta wa Allah, ba ku da wani abin bauta ba shi ba, kada kuma ku tauye mudu da sikeli; lalle ni ina ganin ku da alheri (wato wadata), kuma lalle ni ina jiye muku tsoron azabar wata rana mai kewayewa



Surah: Suratu Hud

Ayah : 85

وَيَٰقَوۡمِ أَوۡفُواْ ٱلۡمِكۡيَالَ وَٱلۡمِيزَانَ بِٱلۡقِسۡطِۖ وَلَا تَبۡخَسُواْ ٱلنَّاسَ أَشۡيَآءَهُمۡ وَلَا تَعۡثَوۡاْ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُفۡسِدِينَ

“Kuma ya ku mutanena, ku cika mudu da sikeli da adalci; kada kuwa ku tauye wa mutane abubuwansu, kada kuma ku yaxa varna a bayan qasa



Surah: Suratul Hijr

Ayah : 19

وَٱلۡأَرۡضَ مَدَدۡنَٰهَا وَأَلۡقَيۡنَا فِيهَا رَوَٰسِيَ وَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا مِن كُلِّ شَيۡءٖ مَّوۡزُونٖ

Qasa kuma Mun shimfixa ta Muka sanya manyan duwatsu a cikinta, Muka kuma tsiro da kowane abu a cikinta qayyadajje



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 35

وَأَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ إِذَا كِلۡتُمۡ وَزِنُواْ بِٱلۡقِسۡطَاسِ ٱلۡمُسۡتَقِيمِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ وَأَحۡسَنُ تَأۡوِيلٗا

Kuma ku cika mudu idan kuka yi awo, kuma ku auna nauyi da ma’auni na adalci. Wannan (shi ya fi) alheri ya kuma fi kyakkyawan qarshe



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 182

وَزِنُواْ بِٱلۡقِسۡطَاسِ ٱلۡمُسۡتَقِيمِ

“Kuma ku riqa yin awon nauyi da ma’auni na adalci



Surah: Suratus Shura

Ayah : 17

ٱللَّهُ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ وَٱلۡمِيزَانَۗ وَمَا يُدۡرِيكَ لَعَلَّ ٱلسَّاعَةَ قَرِيبٞ

Allah ne Ya saukar da Littafi da gaskiya da kuma adalci. Me yake sanar da kai cewa ko alqiyama kusa take



Surah: Suratur Rahman

Ayah : 7

وَٱلسَّمَآءَ رَفَعَهَا وَوَضَعَ ٱلۡمِيزَانَ

Sama kuma Ya xaga ta, Ya kuma kafa adalci



Surah: Suratur Rahman

Ayah : 8

أَلَّا تَطۡغَوۡاْ فِي ٱلۡمِيزَانِ

Don kada ku yi zalunci a abin awo



Surah: Suratur Rahman

Ayah : 9

وَأَقِيمُواْ ٱلۡوَزۡنَ بِٱلۡقِسۡطِ وَلَا تُخۡسِرُواْ ٱلۡمِيزَانَ

Kuma ku tabbatar da awo da adalci kada kuma ku tauye abin awo



Surah: Suratul Hadid

Ayah : 25

لَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلَنَا بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَأَنزَلۡنَا مَعَهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡمِيزَانَ لِيَقُومَ ٱلنَّاسُ بِٱلۡقِسۡطِۖ وَأَنزَلۡنَا ٱلۡحَدِيدَ فِيهِ بَأۡسٞ شَدِيدٞ وَمَنَٰفِعُ لِلنَّاسِ وَلِيَعۡلَمَ ٱللَّهُ مَن يَنصُرُهُۥ وَرُسُلَهُۥ بِٱلۡغَيۡبِۚ إِنَّ ٱللَّهَ قَوِيٌّ عَزِيزٞ

Haqiqa Mun aiko manzanninmu da (ayoyi) mabayyana, Muka kuma saukar da littafi da ma’auni a tare da su (manzannin) don mutane su tsaya da adalci; Muka kuma saukar da baqin qarfe wanda a tare da shi akwai tsananin qarfi da kuma amfani ga mutane, don kuma Allah Ya bayyanar da wanda yake taimakon Sa da manzanninsa a voye. Lalle Allah Mai qarfi ne, Mabuwayi