Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 101

وَكَيۡفَ تَكۡفُرُونَ وَأَنتُمۡ تُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتُ ٱللَّهِ وَفِيكُمۡ رَسُولُهُۥۗ وَمَن يَعۡتَصِم بِٱللَّهِ فَقَدۡ هُدِيَ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Ta yaya kuma za ku kafirce, ga shi kuwa ana karanta muku ayoyin Allah, kuma Manzonsa yana tare da ku? Duk kuwa wanda ya riqi Allah, to haqiqa an shiryar da shi tafarki madaidaici



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 44

إِنَّآ أَنزَلۡنَا ٱلتَّوۡرَىٰةَ فِيهَا هُدٗى وَنُورٞۚ يَحۡكُمُ بِهَا ٱلنَّبِيُّونَ ٱلَّذِينَ أَسۡلَمُواْ لِلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلرَّبَّـٰنِيُّونَ وَٱلۡأَحۡبَارُ بِمَا ٱسۡتُحۡفِظُواْ مِن كِتَٰبِ ٱللَّهِ وَكَانُواْ عَلَيۡهِ شُهَدَآءَۚ فَلَا تَخۡشَوُاْ ٱلنَّاسَ وَٱخۡشَوۡنِ وَلَا تَشۡتَرُواْ بِـَٔايَٰتِي ثَمَنٗا قَلِيلٗاۚ وَمَن لَّمۡ يَحۡكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَٰفِرُونَ

Lalle Mu Muka saukar da Attaura, (wadda) a cikinta akwai shiriya da haske. Annabawa waxanda suka miqa wuya suna hukunci da ita, ga waxanda suke Yahudawa, da malamai na-Allah da malamai masana, saboda abin da aka xora musu na kiyaye Littafin Allah, kuma sun kasance masu ba da shaida a kansa. Don haka kada ku ji tsoron mutane, ku ji tsoro Na Ni kaxai, kuma kada ku musanya ayoyina da wani xan farashi qanqani. Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba kuwa, to waxannan su ne kafirai



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 45

وَكَتَبۡنَا عَلَيۡهِمۡ فِيهَآ أَنَّ ٱلنَّفۡسَ بِٱلنَّفۡسِ وَٱلۡعَيۡنَ بِٱلۡعَيۡنِ وَٱلۡأَنفَ بِٱلۡأَنفِ وَٱلۡأُذُنَ بِٱلۡأُذُنِ وَٱلسِّنَّ بِٱلسِّنِّ وَٱلۡجُرُوحَ قِصَاصٞۚ فَمَن تَصَدَّقَ بِهِۦ فَهُوَ كَفَّارَةٞ لَّهُۥۚ وَمَن لَّمۡ يَحۡكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Kuma Mun wajabta a kansu a cikinta (Attaura), lalle rai da rai, kuma ido da ido, kuma hanci da hanci, kuma kunne da kunne, kuma haqori da haqori, raunuka kuma a yi ramuwa. To duk wanda ya yi sadaka da shi, to wannan kaffara ce gare shi. Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba kuwa, to waxannan su ne azzalumai



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 47

وَلۡيَحۡكُمۡ أَهۡلُ ٱلۡإِنجِيلِ بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فِيهِۚ وَمَن لَّمۡ يَحۡكُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ

Lalle kuma ma’abota Linjila su yi hukunci da abin da Allah Ya saukar a cikinsa. Duk wanda bai yi hukunci da abin da Allah Ya saukar ba kuwa, to waxannan su ne fasiqai



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 48

وَأَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَمُهَيۡمِنًا عَلَيۡهِۖ فَٱحۡكُم بَيۡنَهُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُۖ وَلَا تَتَّبِعۡ أَهۡوَآءَهُمۡ عَمَّا جَآءَكَ مِنَ ٱلۡحَقِّۚ لِكُلّٖ جَعَلۡنَا مِنكُمۡ شِرۡعَةٗ وَمِنۡهَاجٗاۚ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَجَعَلَكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَلَٰكِن لِّيَبۡلُوَكُمۡ فِي مَآ ءَاتَىٰكُمۡۖ فَٱسۡتَبِقُواْ ٱلۡخَيۡرَٰتِۚ إِلَى ٱللَّهِ مَرۡجِعُكُمۡ جَمِيعٗا فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ فِيهِ تَخۡتَلِفُونَ

Kuma Mun saukar maka da Littafin (Alqur’ani) da gaskiya, yana mai gaskata abin da ya gabace shi na sauran littattafai, kuma mai xaukaka a kansu; don haka ka yi hukunci a tsakaninsu da abin da Allah Ya saukar; kuma kada ka bi soye-soyen zukatansu ka bar abin da ya zo maka na gaskiya don bin son zuciyarsu. Kowanne daga cikinku Mun sanya musu tsari na shari’a da tsari na rayuwa. Kuma in da Allah Ya ga dama, da sai Ya sanya ku ku zamo al’umma xaya, sai dai kuma don Ya jarrabe ku cikin abin da Ya ba ku; don haka sai ku yi gaggawar aikata ayyuka na alheri. Gaba xaya makomarku zuwa ga Allah take, kuma zai ba ku labarin abin da kuka kasance kuna savani a kansa



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 49

وَأَنِ ٱحۡكُم بَيۡنَهُم بِمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ وَلَا تَتَّبِعۡ أَهۡوَآءَهُمۡ وَٱحۡذَرۡهُمۡ أَن يَفۡتِنُوكَ عَنۢ بَعۡضِ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ إِلَيۡكَۖ فَإِن تَوَلَّوۡاْ فَٱعۡلَمۡ أَنَّمَا يُرِيدُ ٱللَّهُ أَن يُصِيبَهُم بِبَعۡضِ ذُنُوبِهِمۡۗ وَإِنَّ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلنَّاسِ لَفَٰسِقُونَ

Kuma ka yi hukunci a tsakaninsu da abin da Allah Ya saukar, kuma kada ka bi soye-soyen zukatansu, kuma ka yi hattara da su, don kada su fitine ka ka bar wani sashi na abin da Allah Ya saukar maka; idan kuwa sun juya baya, to ka sani lalle Allah Yana nufin Ya kama su ne da wani sashi na zunubansu. Kuma lalle yawancin mutane fasiqai ne



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 50

أَفَحُكۡمَ ٱلۡجَٰهِلِيَّةِ يَبۡغُونَۚ وَمَنۡ أَحۡسَنُ مِنَ ٱللَّهِ حُكۡمٗا لِّقَوۡمٖ يُوقِنُونَ

Shin hukuncin jahiliyya suke nema ne? To wane ne ya fi Allah kyakkyawan hukunci ga mutanen da suke da sakankancewa?



Surah: Suratul Qasas

Ayah : 50

فَإِن لَّمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَكَ فَٱعۡلَمۡ أَنَّمَا يَتَّبِعُونَ أَهۡوَآءَهُمۡۚ وَمَنۡ أَضَلُّ مِمَّنِ ٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ بِغَيۡرِ هُدٗى مِّنَ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

To idan ba su amsa maka ba, to ka sani cewa ba abin da suke bi sai soye-soyen zukatansu kawai. Ba kuwa wanda ya fi vacewa kamar wanda ya bi son zuciyarsa ba tare da wata shiriya daga Allah ba. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai



Surah: Suratul Jasiya

Ayah : 23

أَفَرَءَيۡتَ مَنِ ٱتَّخَذَ إِلَٰهَهُۥ هَوَىٰهُ وَأَضَلَّهُ ٱللَّهُ عَلَىٰ عِلۡمٖ وَخَتَمَ عَلَىٰ سَمۡعِهِۦ وَقَلۡبِهِۦ وَجَعَلَ عَلَىٰ بَصَرِهِۦ غِشَٰوَةٗ فَمَن يَهۡدِيهِ مِنۢ بَعۡدِ ٱللَّهِۚ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ

Shin kuwa ka ga wanda ya xauki son zuciyarsa (shi ne) abin bautarsa, Allah kuwa Ya vatar da shi a kan yana sane[1], Ya kuma rufe jinsa da zuciyarsa, kuma Ya sanya yana a kan ganinsa, to wane ne zai shiryar da shi in ba Allah ba? Me ya sa ba kwa wa’azantuwa?


1- Watau ya vatar da shi bayan ilimi ya zo masa, saboda Allah ya san cewa ya cancanci vata.