Surah: Suratul Baqara

Ayah : 211

سَلۡ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ كَمۡ ءَاتَيۡنَٰهُم مِّنۡ ءَايَةِۭ بَيِّنَةٖۗ وَمَن يُبَدِّلۡ نِعۡمَةَ ٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَتۡهُ فَإِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Ka tambayi Banu Isra’ila, sau nawa Muka ba su wata aya bayyananniya? Kuma duk wanda ya musanya ni’imar Allah bayan ta zo masa, to lalle Allah Mai tsananin uquba ne



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 285

ءَامَنَ ٱلرَّسُولُ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِ مِن رَّبِّهِۦ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَۚ كُلٌّ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَمَلَـٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّن رُّسُلِهِۦۚ وَقَالُواْ سَمِعۡنَا وَأَطَعۡنَاۖ غُفۡرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيۡكَ ٱلۡمَصِيرُ

Manzon ya yi imani da abin da aka saukar masa daga Ubangijinsa, muminai ma haka, kowanne ya yi imani da Allah da mala’ikunsa da littattafansa da manzanninsa, (suna cewa) : “Ba ma nuna bambanci tsakanin xaya daga cikin manzanninsa.” Kuma suka ce: “Mun ji kuma mun bi ; muna neman gafararka ya Ubangijinmu, kuma zuwa gare Ka ne makoma take



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 3

حُرِّمَتۡ عَلَيۡكُمُ ٱلۡمَيۡتَةُ وَٱلدَّمُ وَلَحۡمُ ٱلۡخِنزِيرِ وَمَآ أُهِلَّ لِغَيۡرِ ٱللَّهِ بِهِۦ وَٱلۡمُنۡخَنِقَةُ وَٱلۡمَوۡقُوذَةُ وَٱلۡمُتَرَدِّيَةُ وَٱلنَّطِيحَةُ وَمَآ أَكَلَ ٱلسَّبُعُ إِلَّا مَا ذَكَّيۡتُمۡ وَمَا ذُبِحَ عَلَى ٱلنُّصُبِ وَأَن تَسۡتَقۡسِمُواْ بِٱلۡأَزۡلَٰمِۚ ذَٰلِكُمۡ فِسۡقٌۗ ٱلۡيَوۡمَ يَئِسَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن دِينِكُمۡ فَلَا تَخۡشَوۡهُمۡ وَٱخۡشَوۡنِۚ ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ وَأَتۡمَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ نِعۡمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلۡإِسۡلَٰمَ دِينٗاۚ فَمَنِ ٱضۡطُرَّ فِي مَخۡمَصَةٍ غَيۡرَ مُتَجَانِفٖ لِّإِثۡمٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

An haramta muku (cin) mushe da jini da naman alade da abin da aka yanka shi da sunan wanin Allah, da (dabbar) da ta shaqe, da wadda aka doke ta, da wadda ta gangaro (daga sama), da dabbar da aka tunkura da qaho, da kuma abin da namun daji masu farauta suka ci, sai dai abin da kuka samu damar yankawa (daga cikinsu), da kuma abin da aka yanka a kan gumaka, da kuma neman sanin sa’a da kibau. Wannan fasiqanci ne. A yau kafirai sun xebe tsammani daga (karya) addininku, don haka kar ku ji tsoron su, ku ji tsoro Na Ni kaxai. A yau Na cika muku addininku, kuma Na cika muku ni’imata, kuma Na yardar muku Musulunci ya zamo shi ne addininku. Duk wanda ya matsu (ya ci abin da aka ambata a baya) saboda yunwa, ba yana mai karkata zuwa ga zunubi ba, to lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai



Surah: Suratul An’am

Ayah : 70

وَذَرِ ٱلَّذِينَ ٱتَّخَذُواْ دِينَهُمۡ لَعِبٗا وَلَهۡوٗا وَغَرَّتۡهُمُ ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَاۚ وَذَكِّرۡ بِهِۦٓ أَن تُبۡسَلَ نَفۡسُۢ بِمَا كَسَبَتۡ لَيۡسَ لَهَا مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلِيّٞ وَلَا شَفِيعٞ وَإِن تَعۡدِلۡ كُلَّ عَدۡلٖ لَّا يُؤۡخَذۡ مِنۡهَآۗ أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ أُبۡسِلُواْ بِمَا كَسَبُواْۖ لَهُمۡ شَرَابٞ مِّنۡ حَمِيمٖ وَعَذَابٌ أَلِيمُۢ بِمَا كَانُواْ يَكۡفُرُونَ

Ka rabu da waxanda suka xauki addininsu wasa da sharholiya, rayuwarsu ta duniya kuma ta ruxe su. Ka kuma yi gargaxi da shi (Alqur’ani), saboda kada a jarrabi rai da abin da ya aikata wanda ba ya da wani mataimaki ko mai ceto ban da Allah, ko da kuwa (ran) ya ba da kowace irin fansa ba za a karva ba daga gare shi. Waxancan su ne waxanda aka kange (don yi musu azaba) saboda abin da suka aikata; suna da abin sha na tafasasshen ruwa da kuma azaba mai raxaxi saboda abin da suka zamanto suna kafircewa (da shi)



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 92

إِنَّ هَٰذِهِۦٓ أُمَّتُكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَأَنَا۠ رَبُّكُمۡ فَٱعۡبُدُونِ

Lallai wannan addini naku guda xaya ne (wato Musulunci), kuma Ni ne Ubangijinku, to ku bauta min



Surah: Suratul Mu’uminun

Ayah : 52

وَإِنَّ هَٰذِهِۦٓ أُمَّتُكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَأَنَا۠ رَبُّكُمۡ فَٱتَّقُونِ

Kuma lalle wannan addininku ne, addini guda xaya (wato Musulunci), kuma Ni ne Ubangijinku, sai ku kiyaye dokokina



Surah: Suratul Qasas

Ayah : 61

أَفَمَن وَعَدۡنَٰهُ وَعۡدًا حَسَنٗا فَهُوَ لَٰقِيهِ كَمَن مَّتَّعۡنَٰهُ مَتَٰعَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا ثُمَّ هُوَ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ مِنَ ٱلۡمُحۡضَرِينَ

Yanzu wanda Muka yi wa alqawari kyakkyawa da zai same shi, zai zama kamar wanda Muka jiyar da shi daxin rayuwar duniya, sannan kuma shi yana daga waxanda za a kai su wuta a ranar alqiyama?



Surah: Suratus Sajda

Ayah : 18

أَفَمَن كَانَ مُؤۡمِنٗا كَمَن كَانَ فَاسِقٗاۚ لَّا يَسۡتَوُۥنَ

Yanzu wanda ya zamanto mumini ya zama kamar wanda ya kasance fasiqi? Ai ba za su zama daidai ba



Surah: Suratuz Zumar

Ayah : 11

قُلۡ إِنِّيٓ أُمِرۡتُ أَنۡ أَعۡبُدَ ٱللَّهَ مُخۡلِصٗا لَّهُ ٱلدِّينَ

Ka ce: “Lalle ni an umarce ni da in bauta wa Allah ina mai tsantsanta addini gare Shi



Surah: Suratuz Zumar

Ayah : 12

وَأُمِرۡتُ لِأَنۡ أَكُونَ أَوَّلَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

“An kuma umarce ni da in kasance farkon Musulmi.”



Surah: Suratuz Zumar

Ayah : 13

قُلۡ إِنِّيٓ أَخَافُ إِنۡ عَصَيۡتُ رَبِّي عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٖ

Ka ce: “Lalle ni ina jin tsoron azabar wani yini mai girma idan na savi Ubangijina”



Surah: Suratuz Zumar

Ayah : 14

قُلِ ٱللَّهَ أَعۡبُدُ مُخۡلِصٗا لَّهُۥ دِينِي

Ka ce: “Allah kawai nake bauta wa, ina mai tsantsanta addinina gare Shi



Surah: Suratul A’ala

Ayah : 14

قَدۡ أَفۡلَحَ مَن تَزَكَّىٰ

Haqiqa wanda ya tsarkaka ya rabauta



Surah: Suratul Bayyina

Ayah : 5

وَمَآ أُمِرُوٓاْ إِلَّا لِيَعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ حُنَفَآءَ وَيُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُواْ ٱلزَّكَوٰةَۚ وَذَٰلِكَ دِينُ ٱلۡقَيِّمَةِ

Ba a kuma umarce su ba sai don su bauta wa Allah suna masu tsantsanta addini gare Shi, suna masu kauce wa varna, suna kuma tsayar da salla, kuma suna ba da zakka. Wannan kuwa shi ne addinin miqaqqiyar hanya