Surah: Suratul Mu’uminun

Ayah : 52

وَإِنَّ هَٰذِهِۦٓ أُمَّتُكُمۡ أُمَّةٗ وَٰحِدَةٗ وَأَنَا۠ رَبُّكُمۡ فَٱتَّقُونِ

Kuma lalle wannan addininku ne, addini guda xaya (wato Musulunci), kuma Ni ne Ubangijinku, sai ku kiyaye dokokina



Surah: Suratul Mu’uminun

Ayah : 73

وَإِنَّكَ لَتَدۡعُوهُمۡ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Kuma lalle kai tabbas kana kiran su ne zuwa ga hanya madaidaiciya



Surah: Suratun Nur

Ayah : 46

لَّقَدۡ أَنزَلۡنَآ ءَايَٰتٖ مُّبَيِّنَٰتٖۚ وَٱللَّهُ يَهۡدِي مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Haqiqa Mun saukar da ayoyi masu bayyana komai da komai. Allah kuma Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga tafarki madaidaici



Surah: Suratur Rum

Ayah : 30

فَأَقِمۡ وَجۡهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفٗاۚ فِطۡرَتَ ٱللَّهِ ٱلَّتِي فَطَرَ ٱلنَّاسَ عَلَيۡهَاۚ لَا تَبۡدِيلَ لِخَلۡقِ ٱللَّهِۚ ذَٰلِكَ ٱلدِّينُ ٱلۡقَيِّمُ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَعۡلَمُونَ

To sai ka tsayar da fuskarka ga addini mai kauce wa varna. (Shi ne) asalin halittar da Allah Ya halicci mutane a kanta[1]. Ba wani canji ga halittar Allah. Wannan shi ne miqaqqen addini, sai dai kuma yawancin mutane ba su san (haka ba)


1- Watau kaxaita Allah da bauta. Addinin Musulunci shi ne addinin da ya dace da halittar xan’adam ta asali, watau fixra.


Surah: Suratur Rum

Ayah : 43

فَأَقِمۡ وَجۡهَكَ لِلدِّينِ ٱلۡقَيِّمِ مِن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَ يَوۡمٞ لَّا مَرَدَّ لَهُۥ مِنَ ٱللَّهِۖ يَوۡمَئِذٖ يَصَّدَّعُونَ

To sai ka tsai da fuskarka ga addini madaidaici tun kafin ranar nan da ba ta da makawa ta zo daga Allah; a wannan ranar ne (mutane) za su rarraba[1]


1- Watau wasu su tafi gidan Aljanna, wasu kuma su nufi wutar jahannama.


Surah: Suratu Yasin

Ayah : 4

عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

(Kana) a kan tafarki madaidaici



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 61

وَأَنِ ٱعۡبُدُونِيۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ

Kuma ku bauta min. Wannan shi ne tafarki madaidaici



Surah: Suratuz Zumar

Ayah : 54

وَأَنِيبُوٓاْ إِلَىٰ رَبِّكُمۡ وَأَسۡلِمُواْ لَهُۥ مِن قَبۡلِ أَن يَأۡتِيَكُمُ ٱلۡعَذَابُ ثُمَّ لَا تُنصَرُونَ

“Ku kuma koma zuwa ga Ubangijinku, ku kuma miqa wuya gare Shi tun gabanin azaba ta zo muku sannan ba za a taimake ku ba



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 33

وَمَنۡ أَحۡسَنُ قَوۡلٗا مِّمَّن دَعَآ إِلَى ٱللَّهِ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا وَقَالَ إِنَّنِي مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

Wane ne ya fi kyakkyawar magana fiye da wanda ya yi kira zuwa ga Allah ya kuma yi aiki nagari, kuma ya ce: “Lalle ni ina daga cikin Musulmi?”



Surah: Suratus Shura

Ayah : 13

۞شَرَعَ لَكُم مِّنَ ٱلدِّينِ مَا وَصَّىٰ بِهِۦ نُوحٗا وَٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ وَمَا وَصَّيۡنَا بِهِۦٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ وَعِيسَىٰٓۖ أَنۡ أَقِيمُواْ ٱلدِّينَ وَلَا تَتَفَرَّقُواْ فِيهِۚ كَبُرَ عَلَى ٱلۡمُشۡرِكِينَ مَا تَدۡعُوهُمۡ إِلَيۡهِۚ ٱللَّهُ يَجۡتَبِيٓ إِلَيۡهِ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِيٓ إِلَيۡهِ مَن يُنِيبُ

Ya shar’anta muku (irin) abin da Ya yi wa Nuhu wahayi da shi na addini, da kuma wanda Muka yiwo maka wahayinsa, da kuma abin da Muka yi wa Ibrahimu da Musa da Isa wasiyya da shi cewa: “Ku tsayar da addini, kuma kada ku rarraba a cikinsa.” Abin da kake kiran kafirai zuwa gare shi ya yi musu nauyi. Allah Yana zavar wanda Ya ga dama zuwa gare shi (addini) Yana kuma shiryar da wanda Ya mayar da al’amarinsa zuwa gare Shi



Surah: Suratus Shura

Ayah : 53

صِرَٰطِ ٱللَّهِ ٱلَّذِي لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ أَلَآ إِلَى ٱللَّهِ تَصِيرُ ٱلۡأُمُورُ

(Watau) tafarkin Allah wanda Yake da mulkin abin da yake cikin sammai da abin da yake qasa. Ku saurara, zuwa ga Allah ne kawai al’amura suke komawa



Surah: Suratuz Zukhruf 

Ayah : 43

فَٱسۡتَمۡسِكۡ بِٱلَّذِيٓ أُوحِيَ إِلَيۡكَۖ إِنَّكَ عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

To ka riqe abin da aka yi maka wahayinsa; lalle kai kana kan hanya madaidaiciya



Surah: Suratuz Zukhruf 

Ayah : 61

وَإِنَّهُۥ لَعِلۡمٞ لِّلسَّاعَةِ فَلَا تَمۡتَرُنَّ بِهَا وَٱتَّبِعُونِۚ هَٰذَا صِرَٰطٞ مُّسۡتَقِيمٞ

Lalle kuma shi (Isa) alama ce ta zuwan alqiyama[1], kada ku yi shakka game da ita, kuma ku bi Ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya


1- Watau lokacin da zai sauko daga sama ta biyu a qarshen zamani, kamar yadda tarin hadisan Annabi () suka tabbatar.


Surah: Suratuz Zukhruf 

Ayah : 63

وَلَمَّا جَآءَ عِيسَىٰ بِٱلۡبَيِّنَٰتِ قَالَ قَدۡ جِئۡتُكُم بِٱلۡحِكۡمَةِ وَلِأُبَيِّنَ لَكُم بَعۡضَ ٱلَّذِي تَخۡتَلِفُونَ فِيهِۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ

Lokacin da kuma Isa ya zo da hujjoji bayyanannu ya ce: “Haqiqa na zo muku da hikima, don kuma in bayyana muku sashin da kuke sassavawa cikinsa; to ku kiyaye dokokin Allah, kuma ku bi ni



Surah: Suratul Fat’h

Ayah : 2

لِّيَغۡفِرَ لَكَ ٱللَّهُ مَا تَقَدَّمَ مِن ذَنۢبِكَ وَمَا تَأَخَّرَ وَيُتِمَّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَيۡكَ وَيَهۡدِيَكَ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا

Don Allah Ya gafarta maka abin da ya gabata na zunubinka, da kuma wanda ya jinkirta, Ya kuma cika maka ni’imarsa, kuma Ya shiryar da kai hanya madaidaiciya



Surah: Suratul Fat’h

Ayah : 20

وَعَدَكُمُ ٱللَّهُ مَغَانِمَ كَثِيرَةٗ تَأۡخُذُونَهَا فَعَجَّلَ لَكُمۡ هَٰذِهِۦ وَكَفَّ أَيۡدِيَ ٱلنَّاسِ عَنكُمۡ وَلِتَكُونَ ءَايَةٗ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ وَيَهۡدِيَكُمۡ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا

Allah kuma Ya yi muku alqawarin wasu ganimomi masu yawa da za ku yi ta kwasar su, sai Ya gaggauto muku da wannan (ganimar Khaibara) Ya kuma kame muku hannayen mutanen (wato Yahudu), don kuwa (wannan) ya zama aya ga muminai, Ya kuma shiryar da su hanya madaidaiciya



Surah: Suratul Fat’h

Ayah : 28

هُوَ ٱلَّذِيٓ أَرۡسَلَ رَسُولَهُۥ بِٱلۡهُدَىٰ وَدِينِ ٱلۡحَقِّ لِيُظۡهِرَهُۥ عَلَى ٱلدِّينِ كُلِّهِۦۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدٗا

Shi ne Wanda Ya aiko Manzonsa da shiriya da kuma addini na gaskiya don Ya xora shi a kan kowane addini. Allah kuma Ya isa Mai shaida



Surah: Suratus Saff 

Ayah : 9

هُوَ ٱلَّذِيٓ أَرۡسَلَ رَسُولَهُۥ بِٱلۡهُدَىٰ وَدِينِ ٱلۡحَقِّ لِيُظۡهِرَهُۥ عَلَى ٱلدِّينِ كُلِّهِۦ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُشۡرِكُونَ

Shi ne Wanda Ya aiko Manzonsa da shiriya da kuma addinin gaskiya don Ya xora shi a kan kowane addini, ko da kuwa mushirikai sun qi



Surah: Suratul Mulk

Ayah : 22

أَفَمَن يَمۡشِي مُكِبًّا عَلَىٰ وَجۡهِهِۦٓ أَهۡدَىٰٓ أَمَّن يَمۡشِي سَوِيًّا عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

Shin wanda yake tafiya a kife a kan fuskarsa shi ya fi zama a kan daidai ko kuma wanda yake tafiya a miqe kan hanya madaidaiciya?



Surah: Suratul Jinn

Ayah : 13

وَأَنَّا لَمَّا سَمِعۡنَا ٱلۡهُدَىٰٓ ءَامَنَّا بِهِۦۖ فَمَن يُؤۡمِنۢ بِرَبِّهِۦ فَلَا يَخَافُ بَخۡسٗا وَلَا رَهَقٗا

“Lalle kuma mu lokacin da muka ji Alqur’ani, sai muka yi imani da shi, to duk wanda zai yi imani da Ubangijinsa, to ba zai ji tsoron qwara ko zalunci ba[1]


1- Watau ba za a tauye masa ladansa ba, kuma ba za a qara masa wani laifin da bai aikata ba.


Surah: Suratul Bayyina

Ayah : 5

وَمَآ أُمِرُوٓاْ إِلَّا لِيَعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ حُنَفَآءَ وَيُقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَيُؤۡتُواْ ٱلزَّكَوٰةَۚ وَذَٰلِكَ دِينُ ٱلۡقَيِّمَةِ

Ba a kuma umarce su ba sai don su bauta wa Allah suna masu tsantsanta addini gare Shi, suna masu kauce wa varna, suna kuma tsayar da salla, kuma suna ba da zakka. Wannan kuwa shi ne addinin miqaqqiyar hanya