Surah: Suratul Baqara

Ayah : 102

وَٱتَّبَعُواْ مَا تَتۡلُواْ ٱلشَّيَٰطِينُ عَلَىٰ مُلۡكِ سُلَيۡمَٰنَۖ وَمَا كَفَرَ سُلَيۡمَٰنُ وَلَٰكِنَّ ٱلشَّيَٰطِينَ كَفَرُواْ يُعَلِّمُونَ ٱلنَّاسَ ٱلسِّحۡرَ وَمَآ أُنزِلَ عَلَى ٱلۡمَلَكَيۡنِ بِبَابِلَ هَٰرُوتَ وَمَٰرُوتَۚ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِنۡ أَحَدٍ حَتَّىٰ يَقُولَآ إِنَّمَا نَحۡنُ فِتۡنَةٞ فَلَا تَكۡفُرۡۖ فَيَتَعَلَّمُونَ مِنۡهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِۦ بَيۡنَ ٱلۡمَرۡءِ وَزَوۡجِهِۦۚ وَمَا هُم بِضَآرِّينَ بِهِۦ مِنۡ أَحَدٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُمۡ وَلَا يَنفَعُهُمۡۚ وَلَقَدۡ عَلِمُواْ لَمَنِ ٱشۡتَرَىٰهُ مَا لَهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنۡ خَلَٰقٖۚ وَلَبِئۡسَ مَا شَرَوۡاْ بِهِۦٓ أَنفُسَهُمۡۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ

Sai suka bi abin da shexanu suke karantawa a (zamanin) mulkin Sulaimanu; kuma Sulaimanu bai kafirta ba, sai dai shexanun su ne suka kafirta; suna koya wa mutane tsafi da abin da aka saukar wa mala’iku biyu, Haruta da Maruta, a garin Babila. Kuma ba sa koya wa wani (tsafin) har sai sun faxa masa cewa: “Mu fa jarraba ce, don haka kada ka kafirta”. Sai (mutane) suka riqa koyo daga wajensu su biyu abin da suke raba tsakanin miji da matarsa da shi. Kuma ba za su iya cutar da wani da shi ba sai da izinin Allah. Sai su koyi abin da zai cutar da su kuma ba zai amfane su ba. Kuma haqiqa sun san cewa, tabbas duk wanda ya zavi (sihiri) ba shi da wani rabo a lahira. Kuma lalle tir da abin da suka sayar da kawunansu da shi, da a ce sun san (haqiqanin makomarsu)



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 116

قَالَ أَلۡقُواْۖ فَلَمَّآ أَلۡقَوۡاْ سَحَرُوٓاْ أَعۡيُنَ ٱلنَّاسِ وَٱسۡتَرۡهَبُوهُمۡ وَجَآءُو بِسِحۡرٍ عَظِيمٖ

Ya ce: “Ku jefa”. To yayin da suka jefa (sandunansu) sai suka sihirce idon mutane[1], kuma suka gigita su, suka zo da wani tsafi babba


1- Sihiri ba ya canza haqiqanin abu zuwa wani abu daban sai dai ya zama rufa ido kawai.


Surah: Suratul A’araf

Ayah : 117

۞وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنۡ أَلۡقِ عَصَاكَۖ فَإِذَا هِيَ تَلۡقَفُ مَا يَأۡفِكُونَ

Muka kuma yi wahayi ga Musa cewa: “Jefa sandarka.” Sai ga shi nan take tana haxiye abin da suke qagowa



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 118

فَوَقَعَ ٱلۡحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Sai gaskiya ta tabbata, abin da kuma suka kasance suna aikatawa sai ya lalace



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 77

قَالَ مُوسَىٰٓ أَتَقُولُونَ لِلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَكُمۡۖ أَسِحۡرٌ هَٰذَا وَلَا يُفۡلِحُ ٱلسَّـٰحِرُونَ

Musa ya ce: “Yanzu kwa riqa ce wa gaskiya (tsafi) lokacin da ta zo muku? Yanzu wannan ne tsafin, alhali kuwa matsafa ba sa cin nasara?”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 78

قَالُوٓاْ أَجِئۡتَنَا لِتَلۡفِتَنَا عَمَّا وَجَدۡنَا عَلَيۡهِ ءَابَآءَنَا وَتَكُونَ لَكُمَا ٱلۡكِبۡرِيَآءُ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا نَحۡنُ لَكُمَا بِمُؤۡمِنِينَ

Suka ce: “Yanzu ka zo mana ne don ka raba mu da abin da muka sami iyayenmu a kansa, ku kuma (kai da Haruna) ku zamanto ku ne masu girma a bayan qasa? Mu kam ba za mu yi imani da ku ba!”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 79

وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ ٱئۡتُونِي بِكُلِّ سَٰحِرٍ عَلِيمٖ

Fir’auna kuma ya ce: “Ku zo mini da duk wani qwararren matsafi.”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 80

فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلۡقُواْ مَآ أَنتُم مُّلۡقُونَ

To lokacin da matsafan suka zo, sai Musa ya ce da su: “Ku jefa duk abin da za ku jefa.”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 81

فَلَمَّآ أَلۡقَوۡاْ قَالَ مُوسَىٰ مَا جِئۡتُم بِهِ ٱلسِّحۡرُۖ إِنَّ ٱللَّهَ سَيُبۡطِلُهُۥٓ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُصۡلِحُ عَمَلَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

To lokacin da suka jefa (kayan tsafinsu), sai Musa ya ce: “Ai abin da kuka zo da shi tsafi ne; lalle ko Allah zai vata shi. Lalle Allah ba Ya gyara aikin mavarnata



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 66

قَالَ بَلۡ أَلۡقُواْۖ فَإِذَا حِبَالُهُمۡ وَعِصِيُّهُمۡ يُخَيَّلُ إِلَيۡهِ مِن سِحۡرِهِمۡ أَنَّهَا تَسۡعَىٰ

Ya ce: “A’a, ku (fara) jefawa.” To saboda sihirinsu sai ga igiyoyinsu da sandunansu ana suranta masa cewa su (macizai ne) suna sauri



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 69

وَأَلۡقِ مَا فِي يَمِينِكَ تَلۡقَفۡ مَا صَنَعُوٓاْۖ إِنَّمَا صَنَعُواْ كَيۡدُ سَٰحِرٖۖ وَلَا يُفۡلِحُ ٱلسَّاحِرُ حَيۡثُ أَتَىٰ

“Kuma ka jefar da abin da yake hannunka na dama, za ta haxiye abin da suka aikata; lalle abin da suka aikata makircin matsafi ne; matsafi kuwa ba ya rabauta duk ta inda ya zo.”



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 73

إِنَّآ ءَامَنَّا بِرَبِّنَا لِيَغۡفِرَ لَنَا خَطَٰيَٰنَا وَمَآ أَكۡرَهۡتَنَا عَلَيۡهِ مِنَ ٱلسِّحۡرِۗ وَٱللَّهُ خَيۡرٞ وَأَبۡقَىٰٓ

“Lalle mu kam mun yi imani da Ubangijinmu don Ya gafarta mana laifukanmu da kuma abin da ka tilasta mu a kansa na tsafi. Allah kuwa Shi ne Mafi alherin (sakamako), kuma Shi ne Mafi dawwamar (azaba).”



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 3

لَاهِيَةٗ قُلُوبُهُمۡۗ وَأَسَرُّواْ ٱلنَّجۡوَى ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ هَلۡ هَٰذَآ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُكُمۡۖ أَفَتَأۡتُونَ ٱلسِّحۡرَ وَأَنتُمۡ تُبۡصِرُونَ

Zukatansu suna cikin gafala. Waxanda suka yi zalunci kuma suka voye abin da suka tattauna (na cewa): “Wannan ba wani ne in ban da mutum kamarku; yanzu kwa riqa bin sihiri alhali kuwa ku kuna gani?”



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 46

فَأُلۡقِيَ ٱلسَّحَرَةُ سَٰجِدِينَ

Sai aka durqusar da masu sihirin suna masu sujjada



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 221

هَلۡ أُنَبِّئُكُمۡ عَلَىٰ مَن تَنَزَّلُ ٱلشَّيَٰطِينُ

Shin ba Na ba ku labari ba game da wanda shexanu suke saukar masa?



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 222

تَنَزَّلُ عَلَىٰ كُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٖ

Suna sauka ne a kan duk wani maqaryaci mai yawan laifi



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 223

يُلۡقُونَ ٱلسَّمۡعَ وَأَكۡثَرُهُمۡ كَٰذِبُونَ

Suna jefa wa (bokaye) abin da suka sato jinsa, yawancinsu kuwa maqaryata ne



Surah: Suratul Jinn

Ayah : 6

وَأَنَّهُۥ كَانَ رِجَالٞ مِّنَ ٱلۡإِنسِ يَعُوذُونَ بِرِجَالٖ مِّنَ ٱلۡجِنِّ فَزَادُوهُمۡ رَهَقٗا

“Kuma lalle yadda lamarin yake, wasu mazaje daga mutane sun kasance suna neman tsari daga wasu mazaje na aljannu, saboda haka suka qara musu girman kai



Surah: Suratul Falaq

Ayah : 4

وَمِن شَرِّ ٱلنَّفَّـٰثَٰتِ فِي ٱلۡعُقَدِ

“Da kuma sharrin mata masu tofi a cikin qulle-qulle