Surah: Suratu Muhammad

Ayah : 3

ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱتَّبَعُواْ ٱلۡبَٰطِلَ وَأَنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّبَعُواْ ٱلۡحَقَّ مِن رَّبِّهِمۡۚ كَذَٰلِكَ يَضۡرِبُ ٱللَّهُ لِلنَّاسِ أَمۡثَٰلَهُمۡ

Wannan (sakamako) kuwa saboda waxanda suka kafirta sun bi varna, waxanda kuwa suka yi imani sun bi shiriya daga Ubangijinsu. Kamar haka ne Allah Yake buga wa mutane misalansu



Surah: Suratul Fat’h

Ayah : 28

هُوَ ٱلَّذِيٓ أَرۡسَلَ رَسُولَهُۥ بِٱلۡهُدَىٰ وَدِينِ ٱلۡحَقِّ لِيُظۡهِرَهُۥ عَلَى ٱلدِّينِ كُلِّهِۦۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدٗا

Shi ne Wanda Ya aiko Manzonsa da shiriya da kuma addini na gaskiya don Ya xora shi a kan kowane addini. Allah kuma Ya isa Mai shaida



Surah: Suratu Qaf 

Ayah : 19

وَجَآءَتۡ سَكۡرَةُ ٱلۡمَوۡتِ بِٱلۡحَقِّۖ ذَٰلِكَ مَا كُنتَ مِنۡهُ تَحِيدُ

Kuma magagin mutuwa ya zo da gaskiya; wannan ne abin da ka kasance kana kakkauce wa



Surah: Suratun Najm

Ayah : 28

وَمَا لَهُم بِهِۦ مِنۡ عِلۡمٍۖ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّۖ وَإِنَّ ٱلظَّنَّ لَا يُغۡنِي مِنَ ٱلۡحَقِّ شَيۡـٔٗا

Kuma ba su da wani ilimi game da haka; ba abin da suke bi sai zato; shi kuma zato, lalle ba ya wadatar da komai game da gaskiya



Surah: Suratul Waqi’a

Ayah : 95

إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ حَقُّ ٱلۡيَقِينِ

Lalle wannan (bayani na cikin wannan Surar) shi ne haqiqanin gaskiya



Surah: Suratus Saff 

Ayah : 8

يُرِيدُونَ لِيُطۡفِـُٔواْ نُورَ ٱللَّهِ بِأَفۡوَٰهِهِمۡ وَٱللَّهُ مُتِمُّ نُورِهِۦ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡكَٰفِرُونَ

Suna nufin su dusashe hasken Allah da bakunansu, Allah kuwa Mai cika haskensa ne ko da kafirai sun qi



Surah: Suratus Saff 

Ayah : 9

هُوَ ٱلَّذِيٓ أَرۡسَلَ رَسُولَهُۥ بِٱلۡهُدَىٰ وَدِينِ ٱلۡحَقِّ لِيُظۡهِرَهُۥ عَلَى ٱلدِّينِ كُلِّهِۦ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُشۡرِكُونَ

Shi ne Wanda Ya aiko Manzonsa da shiriya da kuma addinin gaskiya don Ya xora shi a kan kowane addini, ko da kuwa mushirikai sun qi



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 51

وَإِنَّهُۥ لَحَقُّ ٱلۡيَقِينِ

Kuma lalle shi tabbas gaskiya ce ta sakankancewa



Surah: Suratul Asr

Ayah : 3

إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلۡحَقِّ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلصَّبۡرِ

Sai dai waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, suka kuma yi wa juna wasiyya da gaskiya, suka kuma yi wa juna wasiyya da haquri