Surah: Suratul A’araf

Ayah : 194

إِنَّ ٱلَّذِينَ تَدۡعُونَ مِن دُونِ ٱللَّهِ عِبَادٌ أَمۡثَالُكُمۡۖ فَٱدۡعُوهُمۡ فَلۡيَسۡتَجِيبُواْ لَكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

Lalle waxanda kuke kira ba Allah ba bayi ne kamarku, to ku kirawo su mana, sai su kuma su amsa muku idan kun kasance masu gaskiya ne



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 106

وَلَا تَدۡعُ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَنفَعُكَ وَلَا يَضُرُّكَۖ فَإِن فَعَلۡتَ فَإِنَّكَ إِذٗا مِّنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ

“Kada kuma ka bauta wa wani ba Allah ba, abin da ba zai amfane ka ba, ba kuma zai cuce ka ba; to idan kuwa ka aikata haka to lalle daga sannan ka zama cikin azzalumai.’”



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 14

لَهُۥ دَعۡوَةُ ٱلۡحَقِّۚ وَٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِهِۦ لَا يَسۡتَجِيبُونَ لَهُم بِشَيۡءٍ إِلَّا كَبَٰسِطِ كَفَّيۡهِ إِلَى ٱلۡمَآءِ لِيَبۡلُغَ فَاهُ وَمَا هُوَ بِبَٰلِغِهِۦۚ وَمَا دُعَآءُ ٱلۡكَٰفِرِينَ إِلَّا فِي ضَلَٰلٖ

Gare Shi (Shi kaxai) kira na gaske yake; waxanda kuwa suke bauta wa wasu ba Shi ba, to ba sa amsa musu da komai illa tamkar wanda ya shimfixa tafukansa ga ruwa don ya isa bakinsa, ba kuwa zai isa gare shi ba[1]. Addu’ar kafirai kuma ba a komai take ba illa a cikin vata


1- Watau kamar mai shimfixa hannunsa a kan ruwa yana jiran ya taso ya shiga bakinsa yake yin aikin wofi, hakanan mai bautar wanin Allah shi ma yake yin bautar banza da wofi.


Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 56

قُلِ ٱدۡعُواْ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُم مِّن دُونِهِۦ فَلَا يَمۡلِكُونَ كَشۡفَ ٱلضُّرِّ عَنكُمۡ وَلَا تَحۡوِيلًا

Ka ce (da su): “Ku kirawo waxanda kuka riya (cewa su ne iyayen gijinku) ba Shi ba, to ba su da ikon yaye muku cuta ko juyar da ita.”



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 57

أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ يَبۡتَغُونَ إِلَىٰ رَبِّهِمُ ٱلۡوَسِيلَةَ أَيُّهُمۡ أَقۡرَبُ وَيَرۡجُونَ رَحۡمَتَهُۥ وَيَخَافُونَ عَذَابَهُۥٓۚ إِنَّ عَذَابَ رَبِّكَ كَانَ مَحۡذُورٗا

Waxancan da suke bauta wa[1], su ma suna neman hanya ne zuwa ga Ubangijinsu, a cikinsu wa zai fi kusanci? Suna kuma qaunar rahamarsa, kuma suna tsoron azabarsa. Lalle azabar Ubangijinka ta kasance abar tsoro ce


1- Watau kamar mala’iku ko annabawa ko salihan bayi.


Surah: Suratul Kahf 

Ayah : 52

وَيَوۡمَ يَقُولُ نَادُواْ شُرَكَآءِيَ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُمۡ فَدَعَوۡهُمۡ فَلَمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَهُمۡ وَجَعَلۡنَا بَيۡنَهُم مَّوۡبِقٗا

Kuma (ka tuna) ranar da (Allah) zai ce (da kafirai): “Ku kirawo abokan tarayyar nawa waxanda kuka riya (cewa su ne iyayen gijinku)”, to sai suka kirawo su, sai ba su amsa musu ba, Muka kuma sanya mahallaka a tsakaninsu



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 12

يَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُۥ وَمَا لَا يَنفَعُهُۥۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلضَّلَٰلُ ٱلۡبَعِيدُ

Yana bauta wa wanin Allah, abin da ba zai cuce shi ba kuma ba zai amfane shi ba. Wannan kuwa shi ne vata mai nisa



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 13

يَدۡعُواْ لَمَن ضَرُّهُۥٓ أَقۡرَبُ مِن نَّفۡعِهِۦۚ لَبِئۡسَ ٱلۡمَوۡلَىٰ وَلَبِئۡسَ ٱلۡعَشِيرُ

Yana bauta wa abin da cutarsa ta fi kusa fiye da amfaninsa. Tabbas mataimaki ya munana, kuma tabbas aboki ya munana



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 213

فَلَا تَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَتَكُونَ مِنَ ٱلۡمُعَذَّبِينَ

To kada ka bauta wa wani tare da Allah, sai ka zamanto daga waxanda za a yi wa azaba



Surah: Suratul Qasas

Ayah : 64

وَقِيلَ ٱدۡعُواْ شُرَكَآءَكُمۡ فَدَعَوۡهُمۡ فَلَمۡ يَسۡتَجِيبُواْ لَهُمۡ وَرَأَوُاْ ٱلۡعَذَابَۚ لَوۡ أَنَّهُمۡ كَانُواْ يَهۡتَدُونَ

Kuma aka ce: “Ku kirawo abokan tarayyar naku”, sannan suka kirawo su, sai ba su amsa musu ba, suka kuma ga azaba. (Suka riqa burin) ina ma sun kasance shiryayyu!



Surah: Suratul Qasas

Ayah : 88

وَلَا تَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَۘ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ كُلُّ شَيۡءٍ هَالِكٌ إِلَّا وَجۡهَهُۥۚ لَهُ ٱلۡحُكۡمُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Kuma kada ka bauta wa wani abin bauta daban tare da Allah. Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Kowane abu mai halaka ne sai Fuskarsa kawai. Hukunci (duk) nasa ne, zuwa gare Shi kuma za a mayar da ku



Surah: Suratu Saba’i

Ayah : 22

قُلِ ٱدۡعُواْ ٱلَّذِينَ زَعَمۡتُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ لَا يَمۡلِكُونَ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَلَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا لَهُمۡ فِيهِمَا مِن شِرۡكٖ وَمَا لَهُۥ مِنۡهُم مِّن ظَهِيرٖ

Ka ce: “Ku kirawo waxanda kuka riya (cewa su ne iyayen giji) ba Allah ba;” ba sa mallakar wani abu daidai da qwayar zarra a cikin sammai ko a cikin qasa, ba kuma su da wata tarayya a cikinsu, ba Shi kuma da wani mataimaki daga cikinsu



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 43

لَا جَرَمَ أَنَّمَا تَدۡعُونَنِيٓ إِلَيۡهِ لَيۡسَ لَهُۥ دَعۡوَةٞ فِي ٱلدُّنۡيَا وَلَا فِي ٱلۡأٓخِرَةِ وَأَنَّ مَرَدَّنَآ إِلَى ٱللَّهِ وَأَنَّ ٱلۡمُسۡرِفِينَ هُمۡ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِ

“Ba shakka abin da kuke kira na zuwa gare shi ba shi da wani kira karvavve a duniya ko a lahira, kuma lalle makomarmu zuwa ga Allah ne, mavarnata kuma tabbas su ne ‘yan wuta



Surah: Suratul Ahqaf 

Ayah : 5

وَمَنۡ أَضَلُّ مِمَّن يَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَن لَّا يَسۡتَجِيبُ لَهُۥٓ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ وَهُمۡ عَن دُعَآئِهِمۡ غَٰفِلُونَ

Wane ne ya fi vata fiye da wanda yake bauta wa wani ba Allah ba, wanda ba zai amsa masa ba har zuwa ranar alqiyama, kuma su (ababen bautar) rafkanannu ne game da bautar da suke yi musu?