Surah: Suratul A’araf

Ayah : 100

أَوَلَمۡ يَهۡدِ لِلَّذِينَ يَرِثُونَ ٱلۡأَرۡضَ مِنۢ بَعۡدِ أَهۡلِهَآ أَن لَّوۡ نَشَآءُ أَصَبۡنَٰهُم بِذُنُوبِهِمۡۚ وَنَطۡبَعُ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ فَهُمۡ لَا يَسۡمَعُونَ

Ko kuwa bai bayyana ba ga waxanda suke gaje qasa bayan gushewar mutanenta (na farko) cewa, idan da Mun ga dama da Mun kama su da zunubansu. Kuma da Mun rufe zukatansu don haka ba za su iya ji ba?



Surah: Suratul Anfal

Ayah : 52

كَدَأۡبِ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ فَأَخَذَهُمُ ٱللَّهُ بِذُنُوبِهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ قَوِيّٞ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

(Al’adar kafiran Makka) kamar al’adar mutanen Fir’auna ce da kuma waxanda suke gabaninsu. Sun kafirce wa ayoyin Allah, saboda haka Allah Ya kama su da zunubansu. Lalle Allah Mai qarfi ne, Mai tsananin uquba



Surah: Suratul Anfal

Ayah : 54

كَدَأۡبِ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ فَأَهۡلَكۡنَٰهُم بِذُنُوبِهِمۡ وَأَغۡرَقۡنَآ ءَالَ فِرۡعَوۡنَۚ وَكُلّٞ كَانُواْ ظَٰلِمِينَ

Kamar al’adar mutanen Fir’auna ce da kuma waxanda suke gabaninsu. Sun qaryata ayoyin Ubangijinsu, sai Muka hallaka su saboda zunubansu, Muka kuma nutsar da mutanen Fir’auna (a cikin kogi). Dukkaninsu kuwa sun kasance azzalumai



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 102

وَءَاخَرُونَ ٱعۡتَرَفُواْ بِذُنُوبِهِمۡ خَلَطُواْ عَمَلٗا صَٰلِحٗا وَءَاخَرَ سَيِّئًا عَسَى ٱللَّهُ أَن يَتُوبَ عَلَيۡهِمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ

Wasu kuwa sun yi iqirari da laifinsu, sun gauraya kyakkyawan aiki da wani mummuna, to tabbas Allah zai karvi tubansu. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 17

وَكَمۡ أَهۡلَكۡنَا مِنَ ٱلۡقُرُونِ مِنۢ بَعۡدِ نُوحٖۗ وَكَفَىٰ بِرَبِّكَ بِذُنُوبِ عِبَادِهِۦ خَبِيرَۢا بَصِيرٗا

Al’umma nawa ne Muka hallaka bayan Nuhu? Kuma ai ya isa Ubangijinka Ya zamana Mai cikakken sani ne da gani ga zunuban bayinsa



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 31

وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَوۡلَٰدَكُمۡ خَشۡيَةَ إِمۡلَٰقٖۖ نَّحۡنُ نَرۡزُقُهُمۡ وَإِيَّاكُمۡۚ إِنَّ قَتۡلَهُمۡ كَانَ خِطۡـٔٗا كَبِيرٗا

Kada kuma ku kashe ‘ya’yayenku don tsoron talauci: Mu ne Muke arzuta su har ma da ku. Lalle kashe su kuskure ne babba



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 38

كُلُّ ذَٰلِكَ كَانَ سَيِّئُهُۥ عِندَ رَبِّكَ مَكۡرُوهٗا

Duk waxancan abubuwa mummunansu a wurin Ubangijinka abin qi ne



Surah: Suratul Qasas

Ayah : 78

قَالَ إِنَّمَآ أُوتِيتُهُۥ عَلَىٰ عِلۡمٍ عِندِيٓۚ أَوَلَمۡ يَعۡلَمۡ أَنَّ ٱللَّهَ قَدۡ أَهۡلَكَ مِن قَبۡلِهِۦ مِنَ ٱلۡقُرُونِ مَنۡ هُوَ أَشَدُّ مِنۡهُ قُوَّةٗ وَأَكۡثَرُ جَمۡعٗاۚ وَلَا يُسۡـَٔلُ عَن ذُنُوبِهِمُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ

Ya ce: “Ai ni an ba ni ita (wato dukiyar) ta hanyar ilimin da nake da shi ne.” Shin yanzu bai sani ba ne cewa haqiqa Allah Ya hallaka wasu al’ummun da suke a gabaninsa waxanda suka fi shi qarfi da kuma yawan tarin (dukiya)? Ba kuwa za a tambayi masu laifi game da laifinsu ba[1]


1- Watau zai hallaka su kawai ba tare da tsayawa a yi musu tambayoyi a kan laifukansu ba, ballantana a saurari hanzarinsu.


Surah: Suratul Qasas

Ayah : 84

مَن جَآءَ بِٱلۡحَسَنَةِ فَلَهُۥ خَيۡرٞ مِّنۡهَاۖ وَمَن جَآءَ بِٱلسَّيِّئَةِ فَلَا يُجۡزَى ٱلَّذِينَ عَمِلُواْ ٱلسَّيِّـَٔاتِ إِلَّا مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Duk wanda ya zo da kyakkyawan aiki, to yana da (lada) fiye da aikinsa; wanda kuma ya zo da mummunan aiki, to ba za a saka wa waxanda suka aikata munanan ayyuka ba face daidai da abin da suka kasance suna aikatawa



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 12

وَقَالَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّبِعُواْ سَبِيلَنَا وَلۡنَحۡمِلۡ خَطَٰيَٰكُمۡ وَمَا هُم بِحَٰمِلِينَ مِنۡ خَطَٰيَٰهُم مِّن شَيۡءٍۖ إِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ

Kuma waxanda suka kafirta suka ce da waxanda suka yi imani: “Ku bi tafarkinmu, (mu) lalle za mu xauke muku laifuffukanku,” alhali kuwa su ba za su iya xauke wani abu na laifuffukansu ba; lalle su dai tabbas maqaryata ne



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 13

وَلَيَحۡمِلُنَّ أَثۡقَالَهُمۡ وَأَثۡقَالٗا مَّعَ أَثۡقَالِهِمۡۖ وَلَيُسۡـَٔلُنَّ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ عَمَّا كَانُواْ يَفۡتَرُونَ

Tabbas kuma za su xauki zunubansu da kuma wasu zunuban tare da zunubansu[1]; kuma tabbas za a tambaye su a ranar alqiyama game da abin da suka kasance suna qirqira


1- Watau tare da zunuban waxanda suka yaudara suka vatar da su, ba kuma tare da an rage zunuban mabiyansu ba.


Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 40

فَكُلًّا أَخَذۡنَا بِذَنۢبِهِۦۖ فَمِنۡهُم مَّنۡ أَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِ حَاصِبٗا وَمِنۡهُم مَّنۡ أَخَذَتۡهُ ٱلصَّيۡحَةُ وَمِنۡهُم مَّنۡ خَسَفۡنَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ وَمِنۡهُم مَّنۡ أَغۡرَقۡنَاۚ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيَظۡلِمَهُمۡ وَلَٰكِن كَانُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ يَظۡلِمُونَ

Kowanne (cikin al’ummun da suka gabata) Mun kama shi da laifinsa; daga cikinsu akwai waxanda Muka aiko wa da duwatsu, akwai kuma waxanda tsawa ta kama su, kuma daga cikinsu akwai waxanda Muka kifar da su cikin qasa, akwai kuma daga cikinsu waxanda Muka nutsar a ruwa. Allah kuma bai kasance Yana zaluntar su ba, sai dai kawai kawunansu suke zalunta



Surah: Suratul Ahzab

Ayah : 58

وَٱلَّذِينَ يُؤۡذُونَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ بِغَيۡرِ مَا ٱكۡتَسَبُواْ فَقَدِ ٱحۡتَمَلُواْ بُهۡتَٰنٗا وَإِثۡمٗا مُّبِينٗا

Waxanda suke cutar muminai maza da muminai mata ba tare da sun yi laifi ba, to haqiqa sun xauki nauyin qage da kuma zunubi bayyananne



Surah: Suratuz Zumar

Ayah : 53

۞قُلۡ يَٰعِبَادِيَ ٱلَّذِينَ أَسۡرَفُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمۡ لَا تَقۡنَطُواْ مِن رَّحۡمَةِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ جَمِيعًاۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ

Ka ce[1]: “Ya ku bayina waxanda suka vata kawunansu sosai (da kafirci da savon Allah), kada ku xebe qauna daga rahamar Allah. Lalle Allah Yana gafarta zunubai baki xaya[2]. Lalle Shi Mai gafara ne, Mai rahama


1- Allah ne yake umartar Manzonsa () da ya faxa wa muminai bayin Allah.


2- Watau ga wanda ya tuba.


Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 21

۞أَوَلَمۡ يَسِيرُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَيَنظُرُواْ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلَّذِينَ كَانُواْ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَانُواْ هُمۡ أَشَدَّ مِنۡهُمۡ قُوَّةٗ وَءَاثَارٗا فِي ٱلۡأَرۡضِ فَأَخَذَهُمُ ٱللَّهُ بِذُنُوبِهِمۡ وَمَا كَانَ لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ مِن وَاقٖ

Shin ba sa tafiya a bayan qasa sannan su ga yaya qarshen waxanda suka kasance gabaninsu ya zama? Su sun kasance sun fi su tsananin qarfi da barin gurabe na tarihi a bayan qasa, sai Allah Ya kama su da laifukansu, ba su kuma da wani mai kare su daga Allah



Surah: Suratus Shura

Ayah : 40

وَجَزَـٰٓؤُاْ سَيِّئَةٖ سَيِّئَةٞ مِّثۡلُهَاۖ فَمَنۡ عَفَا وَأَصۡلَحَ فَأَجۡرُهُۥ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّهُۥ لَا يُحِبُّ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Kuma sakamakon mummunan (abu) shi ne mayar da mummuna kamarsa; to wanda ya yi afuwa ya kuma kyautata, to ladansa yana wurin Allah. Lalle Shi ba Ya son azzalumai



Surah: Suratul Hujurat

Ayah : 12

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱجۡتَنِبُواْ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلظَّنِّ إِنَّ بَعۡضَ ٱلظَّنِّ إِثۡمٞۖ وَلَا تَجَسَّسُواْ وَلَا يَغۡتَب بَّعۡضُكُم بَعۡضًاۚ أَيُحِبُّ أَحَدُكُمۡ أَن يَأۡكُلَ لَحۡمَ أَخِيهِ مَيۡتٗا فَكَرِهۡتُمُوهُۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ تَوَّابٞ رَّحِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, ku nisanci yawancin zace-zace, lalle shashin zace-zace laifi ne; kada kuma ku riqa binciken laifukan wasu, kuma kada shashinku ya riqa gibar shashi. Yanzu xayanku zai so ya ci naman xan’uwansa matacce? To sai kuka qi shi. To ku kiyaye dokokin Allah. Lalle Allah Mai karvar tuba ne, Mai jin qai



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 8

أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ نُهُواْ عَنِ ٱلنَّجۡوَىٰ ثُمَّ يَعُودُونَ لِمَا نُهُواْ عَنۡهُ وَيَتَنَٰجَوۡنَ بِٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِ وَمَعۡصِيَتِ ٱلرَّسُولِۖ وَإِذَا جَآءُوكَ حَيَّوۡكَ بِمَا لَمۡ يُحَيِّكَ بِهِ ٱللَّهُ وَيَقُولُونَ فِيٓ أَنفُسِهِمۡ لَوۡلَا يُعَذِّبُنَا ٱللَّهُ بِمَا نَقُولُۚ حَسۡبُهُمۡ جَهَنَّمُ يَصۡلَوۡنَهَاۖ فَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

Shin ba ka ga waxanda aka hana su ganawa ba, sannan suke koma wa abin da aka hane su yinsa, suke kuma ganawa a kan savo da ta’addanci, da kuma sava wa Manzo? Idan kuma suka zo wurinka sai su gaishe ka da lafazin da Allah bai gaishe ka da shi ba[1], su riqa cewa a ransu: “Me ya hana Allah Ya azabtar da mu saboda abin da muka faxa?” Jahannama ta ishe su, za su shige ta; saboda haka makoma ta munana


1- Watau suna ce masa: Assamu alaika, ma’ana mutuwa ta tabbata a kanka.


Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 9

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِذَا تَنَٰجَيۡتُمۡ فَلَا تَتَنَٰجَوۡاْ بِٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِ وَمَعۡصِيَتِ ٱلرَّسُولِ وَتَنَٰجَوۡاْ بِٱلۡبِرِّ وَٱلتَّقۡوَىٰۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ ٱلَّذِيٓ إِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, idan za ku gana to kada ku yi ganawar savo da ta’addanci da kuma sava wa Manzo. (A maimakon haka) ku gana a kan ayyukan alheri da taqawa; kuma ku kiyaye dokokin Allah wanda zuwa gare Shi ne za a tattaro ku



Surah: Suratus Saff 

Ayah : 12

يَغۡفِرۡ لَكُمۡ ذُنُوبَكُمۡ وَيُدۡخِلۡكُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ وَمَسَٰكِنَ طَيِّبَةٗ فِي جَنَّـٰتِ عَدۡنٖۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ

(Idan kun yi haka) zai gafarta muku zunubanku Ya kuma shigar da ku gidajen Aljanna (waxanda) qoramu suke gudana ta qarqashinsu da kuma wuraren zama masu kyau, a cikin gidajen Aljanna na dawwama. Wannan shi ne babban rabo



Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 9

وَجَآءَ فِرۡعَوۡنُ وَمَن قَبۡلَهُۥ وَٱلۡمُؤۡتَفِكَٰتُ بِٱلۡخَاطِئَةِ

Fir’auna kuma da waxanda suke gabaninsa da (alqaryar) da aka kifar[1], sun zo da manyan laifuka


1- Watau alqaryun Annabi Lux () waxanda Allah () ya kifar da su saboda miyagun laifuffukansu.


Surah: Suratul Haqqa

Ayah : 10

فَعَصَوۡاْ رَسُولَ رَبِّهِمۡ فَأَخَذَهُمۡ أَخۡذَةٗ رَّابِيَةً

Sai suka sava wa Manzon Ubangijinsu, sai Muka kama su kamawa mai qaruwa



Surah: Suratut Takwir

Ayah : 9

بِأَيِّ ذَنۢبٖ قُتِلَتۡ

Da wane laifi ne aka kashe ta?