Surah: Suratur Rum

Ayah : 23

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ مَنَامُكُم بِٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَٱبۡتِغَآؤُكُم مِّن فَضۡلِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَسۡمَعُونَ

Yana kuma daga cikin ayoyinsa barcinku da daddare da kuma rana da neman falalarsa da kuke yi. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga masu ji (na lura)



Surah: Suratur Rum

Ayah : 24

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ يُرِيكُمُ ٱلۡبَرۡقَ خَوۡفٗا وَطَمَعٗا وَيُنَزِّلُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَيُحۡيِۦ بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَآۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ

Yana kuma daga cikin ayoyinsa nuna muku walqiya da Yake yi don tsoratarwa da kwaxaitarwa, Ya kuma saukar da ruwa daga sama, sai Ya raya qasa da shi bayan mutuwarta. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutane da suke hankalta



Surah: Suratur Rum

Ayah : 25

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَن تَقُومَ ٱلسَّمَآءُ وَٱلۡأَرۡضُ بِأَمۡرِهِۦۚ ثُمَّ إِذَا دَعَاكُمۡ دَعۡوَةٗ مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ إِذَآ أَنتُمۡ تَخۡرُجُونَ

Yana kuma daga cikin ayoyinsa sama da qasa su tsaya da umarninsa. Sannan kuma yayin da Ya kira ku (don ku tashi) daga qasa sai ga ku kuna fitowa



Surah: Suratur Rum

Ayah : 37

أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Yanzu ba su gani ba cewa Allah Yana shimfixa arziki ga wanda Ya ga dama, Yana kuma quntatawa (ga wanda ya ga dama)? Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutanen da suke yin imani



Surah: Suratur Rum

Ayah : 46

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَن يُرۡسِلَ ٱلرِّيَاحَ مُبَشِّرَٰتٖ وَلِيُذِيقَكُم مِّن رَّحۡمَتِهِۦ وَلِتَجۡرِيَ ٱلۡفُلۡكُ بِأَمۡرِهِۦ وَلِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

Yana kuma daga ayoyinsa cewa Yana aiko iska tana mai yin albishir (da ruwa) kuma don Ya xanxana muku rahamarsa, don kuma jiragen ruwa su riqa gudana da umarninsa, kuma don ku nema daga falalarsa ko kwa gode



Surah: Suratu Luqman

Ayah : 31

أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱلۡفُلۡكَ تَجۡرِي فِي ٱلۡبَحۡرِ بِنِعۡمَتِ ٱللَّهِ لِيُرِيَكُم مِّنۡ ءَايَٰتِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّكُلِّ صَبَّارٖ شَكُورٖ

Ba ka gani cewa jiragen ruwa suna tafiya a cikin kogi da ni’imar Allah, don Ya nuna muku (wasu) daga ayoyinsa? Lalle a game da wannan akwai ayoyi ga duk mai yawan haquri, mai yawan godiya



Surah: Suratu Saba’i

Ayah : 9

أَفَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَىٰ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ إِن نَّشَأۡ نَخۡسِفۡ بِهِمُ ٱلۡأَرۡضَ أَوۡ نُسۡقِطۡ عَلَيۡهِمۡ كِسَفٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّكُلِّ عَبۡدٖ مُّنِيبٖ

Ba sa dubawa su ga abin da yake gabansu da abin da yake bayansu na sama da qasa? In da Mun ga dama sai Mu nutsar da su cikin qasa ko kuma Mu rufto musu da wani yanki daga sama. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya ga duk wani bawa mai komawa ga Allah



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 38

وَٱلشَّمۡسُ تَجۡرِي لِمُسۡتَقَرّٖ لَّهَاۚ ذَٰلِكَ تَقۡدِيرُ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡعَلِيمِ

Rana kuma tana gudu zuwa wurin da aka iyakance mata. Wannan tsari ne na (Allah) Mabuwayi, Masani



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 39

وَٱلۡقَمَرَ قَدَّرۡنَٰهُ مَنَازِلَ حَتَّىٰ عَادَ كَٱلۡعُرۡجُونِ ٱلۡقَدِيمِ

Wata kuma Mun qaddara masa masaukai, har ya koma kamar tsohuwar zarbar dabino



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 40

لَا ٱلشَّمۡسُ يَنۢبَغِي لَهَآ أَن تُدۡرِكَ ٱلۡقَمَرَ وَلَا ٱلَّيۡلُ سَابِقُ ٱلنَّهَارِۚ وَكُلّٞ فِي فَلَكٖ يَسۡبَحُونَ

Ba zai yiwu rana ta riski wata ba, dare kuma ba zai riga yini ba. Kowanne kuwa yana iyo ne a cikin falaki



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 41

وَءَايَةٞ لَّهُمۡ أَنَّا حَمَلۡنَا ذُرِّيَّتَهُمۡ فِي ٱلۡفُلۡكِ ٱلۡمَشۡحُونِ

Kuma wata aya ce a gare su cewa Mu Muka xauki iyayensu a cikin jirgin ruwa wanda aka maqare[1]


1- Watau wanda Allah ya tserar da zuriyar Annabi Adamu () a cikinsa a zamanin Annabi Nuhu () bayan varkewar ruwan Xufana.


Surah: Suratu Yasin

Ayah : 42

وَخَلَقۡنَا لَهُم مِّن مِّثۡلِهِۦ مَا يَرۡكَبُونَ

Muka kuma halitta musu abin da suke hawa kwatankwacinsa



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 43

وَإِن نَّشَأۡ نُغۡرِقۡهُمۡ فَلَا صَرِيخَ لَهُمۡ وَلَا هُمۡ يُنقَذُونَ

Idan kuwa da Mun ga dama, sai Mu nutsar da su, don haka babu wani mai taimakon su, ba kuma za a kuvutar da su ba



Surah: Suratu Yasin

Ayah : 44

إِلَّا رَحۡمَةٗ مِّنَّا وَمَتَٰعًا إِلَىٰ حِينٖ

Sai dai rahama daga gare Mu da kuma jin daxi zuwa wani lokaci



Surah: Suratuz Zumar

Ayah : 42

ٱللَّهُ يَتَوَفَّى ٱلۡأَنفُسَ حِينَ مَوۡتِهَا وَٱلَّتِي لَمۡ تَمُتۡ فِي مَنَامِهَاۖ فَيُمۡسِكُ ٱلَّتِي قَضَىٰ عَلَيۡهَا ٱلۡمَوۡتَ وَيُرۡسِلُ ٱلۡأُخۡرَىٰٓ إِلَىٰٓ أَجَلٖ مُّسَمًّىۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ

Allah Yana karvar rayuka lokacin mutuwarsu, da waxanda kuma ba su mutu ba a lokacin baccinsu; sai Ya riqe waxanda Ya qaddara wa mutuwa, Ya kuma saki sauran har zuwa wani lokaci qayyadadde. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutane masu tunani



Surah: Suratuz Zumar

Ayah : 52

أَوَلَمۡ يَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Yanzu ba su sani ba ne cewa, Allah Yana shimfixa arziki ga wanda Ya ga dama, Yana kuma quntata wa (ga wanda ya ga dama)? Lalle a game da waxannan tabbas akwai ayoyi ga mutane masu yin imani



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 37

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِ ٱلَّيۡلُ وَٱلنَّهَارُ وَٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُۚ لَا تَسۡجُدُواْ لِلشَّمۡسِ وَلَا لِلۡقَمَرِ وَٱسۡجُدُواْۤ لِلَّهِۤ ٱلَّذِي خَلَقَهُنَّ إِن كُنتُمۡ إِيَّاهُ تَعۡبُدُونَ

Kuma dare da wuni da rana da wata suna daga ayoyinsa. Kada ku yi sujjada ga rana ko ga wata, ku yi sujjada ga Allah Wanda Ya halicce su idan har kun kasance Shi kaxai kuke bauta wa



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 39

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنَّكَ تَرَى ٱلۡأَرۡضَ خَٰشِعَةٗ فَإِذَآ أَنزَلۡنَا عَلَيۡهَا ٱلۡمَآءَ ٱهۡتَزَّتۡ وَرَبَتۡۚ إِنَّ ٱلَّذِيٓ أَحۡيَاهَا لَمُحۡيِ ٱلۡمَوۡتَىٰٓۚ إِنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

Yana kuma daga ayoyinsa cewa lalle za ka ga qasa a qeqashe, to idan Mun saukar mata da ruwa sai ta girgiza ta kumbura (ta fitar da tsirrai). Lalle wanda Ya raya ta Shi ne Mai raya matattu. Lalle Shi Mai iko ne a kan komai



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 53

سَنُرِيهِمۡ ءَايَٰتِنَا فِي ٱلۡأٓفَاقِ وَفِيٓ أَنفُسِهِمۡ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَهُمۡ أَنَّهُ ٱلۡحَقُّۗ أَوَلَمۡ يَكۡفِ بِرَبِّكَ أَنَّهُۥ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ

Ba da daxewa ba za Mu nuna musu ayoyinmu a cikin nahiyoyi da kuma a kan kawunansu har sai sun gane cewa lalle shi (Alqur’ani) gaskiya ne. Yanzu bai ishe ka ba game da Ubangijinka cewa Shi lalle Mai shaida ne a kan komai?



Surah: Suratus Shura

Ayah : 29

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ خَلۡقُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَثَّ فِيهِمَا مِن دَآبَّةٖۚ وَهُوَ عَلَىٰ جَمۡعِهِمۡ إِذَا يَشَآءُ قَدِيرٞ

Yana kuma daga cikin ayoyinsa halittar sammai da qasa da kuma dabbobin da Ya yaxa a cikinsu. Kuma shi Mai iko ne a kan Ya tara su idan Ya ga dama



Surah: Suratus Shura

Ayah : 30

وَمَآ أَصَٰبَكُم مِّن مُّصِيبَةٖ فَبِمَا كَسَبَتۡ أَيۡدِيكُمۡ وَيَعۡفُواْ عَن كَثِيرٖ

Abin da kuma ya same ku na wata masifa, to saboda abin da hannayenku ne suka tsuwurwurta, Yana kuma yin afuwa ga wasu (laifuka) masu yawa



Surah: Suratus Shura

Ayah : 31

وَمَآ أَنتُم بِمُعۡجِزِينَ فِي ٱلۡأَرۡضِۖ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ ٱللَّهِ مِن وَلِيّٖ وَلَا نَصِيرٖ

Kuma ku ba za ku gagara ba a bayan qasa; kuma ba ku da wani majivinci ko mataimaki in ba Allah ba



Surah: Suratus Shura

Ayah : 32

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِ ٱلۡجَوَارِ فِي ٱلۡبَحۡرِ كَٱلۡأَعۡلَٰمِ

Daga cikin ayoyinsa kuma akwai jiragen ruwa masu gudu a cikin kogi kamar duwatsu



Surah: Suratul Jasiya

Ayah : 4

وَفِي خَلۡقِكُمۡ وَمَا يَبُثُّ مِن دَآبَّةٍ ءَايَٰتٞ لِّقَوۡمٖ يُوقِنُونَ

A cikin halittarku ma da abin da Yake bazawa na dabbobi, akwai ayoyi ga mutane masu sakankancewa



Surah: Suratul Jasiya

Ayah : 5

وَٱخۡتِلَٰفِ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ وَمَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مِن رِّزۡقٖ فَأَحۡيَا بِهِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَا وَتَصۡرِيفِ ٱلرِّيَٰحِ ءَايَٰتٞ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ

Da kuma sassavawar dare da yini da abin da Ya saukar daga sama na arziki, sai Ya raya qasa da shi bayan mutuwarta, da kuma jujjuyawar iska, akwai ayoyi ga mutanen da suke hankalta



Surah: Suratul Jasiya

Ayah : 12

۞ٱللَّهُ ٱلَّذِي سَخَّرَ لَكُمُ ٱلۡبَحۡرَ لِتَجۡرِيَ ٱلۡفُلۡكُ فِيهِ بِأَمۡرِهِۦ وَلِتَبۡتَغُواْ مِن فَضۡلِهِۦ وَلَعَلَّكُمۡ تَشۡكُرُونَ

Allah ne wanda Ya hore muku kogi don jiragen ruwa su riqa gudu a cikinsa da umarninsa, don kuma ku nema daga falalarsa don kuma ku gode



Surah: Suratul Jasiya

Ayah : 13

وَسَخَّرَ لَكُم مَّا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعٗا مِّنۡهُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ

Ya kuma hore muku abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa gaba xayansu daga gare Shi. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutanen da suke yin tunani



Surah: Suratul Fat’h

Ayah : 20

وَعَدَكُمُ ٱللَّهُ مَغَانِمَ كَثِيرَةٗ تَأۡخُذُونَهَا فَعَجَّلَ لَكُمۡ هَٰذِهِۦ وَكَفَّ أَيۡدِيَ ٱلنَّاسِ عَنكُمۡ وَلِتَكُونَ ءَايَةٗ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ وَيَهۡدِيَكُمۡ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا

Allah kuma Ya yi muku alqawarin wasu ganimomi masu yawa da za ku yi ta kwasar su, sai Ya gaggauto muku da wannan (ganimar Khaibara) Ya kuma kame muku hannayen mutanen (wato Yahudu), don kuwa (wannan) ya zama aya ga muminai, Ya kuma shiryar da su hanya madaidaiciya



Surah: Suratuz Zariyat

Ayah : 20

وَفِي ٱلۡأَرۡضِ ءَايَٰتٞ لِّلۡمُوقِنِينَ

A cikin qasa kuma akwai ayoyi ga masu sakankancewa



Surah: Suratuz Zariyat

Ayah : 21

وَفِيٓ أَنفُسِكُمۡۚ أَفَلَا تُبۡصِرُونَ

Da kuma cikin kawunanku. Yanzu ba kwa lura ba?