Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 67

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ

Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 119

فَأَنجَيۡنَٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ فِي ٱلۡفُلۡكِ ٱلۡمَشۡحُونِ

Sai Muka tserar da shi da waxanda suke tare da shi a cikin jirgin ruwan da ke maqare (da mutane da dabbobi)



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 120

ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا بَعۡدُ ٱلۡبَاقِينَ

Sannan bayan haka Muka nutsar da sauran



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 121

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ

Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 139

فَكَذَّبُوهُ فَأَهۡلَكۡنَٰهُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ

Sai suka qaryata shi, sannan Muka hallaka su. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 154

مَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٞ مِّثۡلُنَا فَأۡتِ بِـَٔايَةٍ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّـٰدِقِينَ

“Kai ba kowa ba ne sai mutum kamarmu, to ka zo mana da aya idan ka kasance daga masu gaskiya.”



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 155

قَالَ هَٰذِهِۦ نَاقَةٞ لَّهَا شِرۡبٞ وَلَكُمۡ شِرۡبُ يَوۡمٖ مَّعۡلُومٖ

(Salihu) ya ce: “Wannan taguwa ce[1], tana da (ranar) shanta ku ma kuna da rana sananniya ta shanku


1- Watau a matsayin mu’ujiza ga Annabi Salihu ().


Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 156

وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوٓءٖ فَيَأۡخُذَكُمۡ عَذَابُ يَوۡمٍ عَظِيمٖ

“Kada kuwa ku shafe ta da mugun abu, sai azabar wani yini mai girma ta kama ku.”



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 157

فَعَقَرُوهَا فَأَصۡبَحُواْ نَٰدِمِينَ

Sai suka soke ta, sai kuwa suka wayi gari suna masu nadama



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 158

فَأَخَذَهُمُ ٱلۡعَذَابُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ

Sai azaba ta kama su. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; kuma yawancinsu ba su zamanto muminai ba



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 170

فَنَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ

Sai Muka tserar da shi da iyalinsa gaba xaya



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 171

إِلَّا عَجُوزٗا فِي ٱلۡغَٰبِرِينَ

Sai fa wata tsohuwa (watau matarsa) da ta (kasance tana) cikin hallakakku



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 172

ثُمَّ دَمَّرۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ

Sannan Muka hallaka sauran



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 173

وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهِم مَّطَرٗاۖ فَسَآءَ مَطَرُ ٱلۡمُنذَرِينَ

Muka kuma saukar musu da ruwa na azaba; to ruwan azabar waxanda aka yi wa gargaxi ya munana



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 174

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ

Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; yawancinsu kuwa ba su zamanto muminai ba



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 189

فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمۡ عَذَابُ يَوۡمِ ٱلظُّلَّةِۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٍ

Sai suka qaryata shi, sannan sai azabar yinin girgije (na wuta) ta kama su. Lalle ta kasance azabar wani yini ne mai girma



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 190

إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ

Lalle a game da wannan tabbas akwai aya; sai dai kuma yawancinsu ba su kasance muminai ba



Surah: Suratun Namli

Ayah : 50

وَمَكَرُواْ مَكۡرٗا وَمَكَرۡنَا مَكۡرٗا وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ

Kuma suka shirya makirci, Mu kuma Muka shirya rusa makircinsu alhali kuwa su ba su sani ba



Surah: Suratun Namli

Ayah : 51

فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ مَكۡرِهِمۡ أَنَّا دَمَّرۡنَٰهُمۡ وَقَوۡمَهُمۡ أَجۡمَعِينَ

Sai ka duba ka ga yadda qarshen makircinsu ya zama, watau Mun hallakar da su tare da mutanensu baki xaya



Surah: Suratun Namli

Ayah : 52

فَتِلۡكَ بُيُوتُهُمۡ خَاوِيَةَۢ بِمَا ظَلَمُوٓاْۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّقَوۡمٖ يَعۡلَمُونَ

To ga gidajensu can a rugurguje babu kowa saboda zaluncinsu. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya ga mutanen da suke ganewa



Surah: Suratun Namli

Ayah : 86

أَلَمۡ يَرَوۡاْ أَنَّا جَعَلۡنَا ٱلَّيۡلَ لِيَسۡكُنُواْ فِيهِ وَٱلنَّهَارَ مُبۡصِرًاۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يُؤۡمِنُونَ

Yanzu ba sa gani cewa Mu Muka samar da dare don su nutsu a cikinsa, da kuma rana mai haskakawa (don su yi harka)? Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutanen da suke yin imani



Surah: Suratun Namli

Ayah : 93

وَقُلِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ سَيُرِيكُمۡ ءَايَٰتِهِۦ فَتَعۡرِفُونَهَاۚ وَمَا رَبُّكَ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ

Ka kuma ce: “Dukkan yabo ya tabbata ga Allah; ba da daxewa ba zai nuna muku ayoyinsa, za kuma ku san su. Ubangijinka kuma ba rafkananne ba ne game da abin da kuke aikatawa.”



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 15

فَأَنجَيۡنَٰهُ وَأَصۡحَٰبَ ٱلسَّفِينَةِ وَجَعَلۡنَٰهَآ ءَايَةٗ لِّلۡعَٰلَمِينَ

Sai Muka tserar da shi tare da mutanen jirgin ruwa, Muka kuma sanya shi (jirgin) aya ga talikai



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 34

إِنَّا مُنزِلُونَ عَلَىٰٓ أَهۡلِ هَٰذِهِ ٱلۡقَرۡيَةِ رِجۡزٗا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ بِمَا كَانُواْ يَفۡسُقُونَ

“Lalle mu masu saukar da azaba ce daga sama a kan mutanen wannan alqaryar saboda abin da suka kasance suna aikatawa na fasiqanci.”



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 35

وَلَقَد تَّرَكۡنَا مِنۡهَآ ءَايَةَۢ بَيِّنَةٗ لِّقَوۡمٖ يَعۡقِلُونَ

Kuma haqiqa Mu mun bar aya bayyananniya game da ita (alqaryar) ga mutanen da suke hankalta



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 44

خَلَقَ ٱللَّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَ بِٱلۡحَقِّۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةٗ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ

Allah Ya halicci sammai da qasa da gaskiya. Lalle a game da wannan tabbas akwai aya ga muminai



Surah: Suratur Rum

Ayah : 19

يُخۡرِجُ ٱلۡحَيَّ مِنَ ٱلۡمَيِّتِ وَيُخۡرِجُ ٱلۡمَيِّتَ مِنَ ٱلۡحَيِّ وَيُحۡيِ ٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ مَوۡتِهَاۚ وَكَذَٰلِكَ تُخۡرَجُونَ

Yana fitar da rayayye daga matacce, Yana kuma fitar da matacce daga rayayye, kuma Yana raya qasa bayan mutuwarta. Kamar haka ne kuma za a fito da ku (daga qaburburanku)



Surah: Suratur Rum

Ayah : 20

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنۡ خَلَقَكُم مِّن تُرَابٖ ثُمَّ إِذَآ أَنتُم بَشَرٞ تَنتَشِرُونَ

Yana daga ayoyinsa cewa Ya halicce ku daga turvaya, sannan kuma sai ga ku mutane kun warwatsu (a ko’ina)



Surah: Suratur Rum

Ayah : 21

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦٓ أَنۡ خَلَقَ لَكُم مِّنۡ أَنفُسِكُمۡ أَزۡوَٰجٗا لِّتَسۡكُنُوٓاْ إِلَيۡهَا وَجَعَلَ بَيۡنَكُم مَّوَدَّةٗ وَرَحۡمَةًۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ

Yana kuma daga ayoyinsa cewa Ya halitta muku mata daga jinsinku don ku samu nutsuwa gare su, Ya kuma sanya soyayya da jin qai tsakaninku. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga mutane masu tunani



Surah: Suratur Rum

Ayah : 22

وَمِنۡ ءَايَٰتِهِۦ خَلۡقُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَٱخۡتِلَٰفُ أَلۡسِنَتِكُمۡ وَأَلۡوَٰنِكُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّلۡعَٰلِمِينَ

Yana kuma daga cikin ayoyinsa halittar sammai da qasa da kuma sassavawar harsunanku da launukanku. Lalle a game da wannan tabbas akwai ayoyi ga ma’abota ilimi