Surah: Suratun Nur

Ayah : 21

۞يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَتَّبِعُواْ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ وَمَن يَتَّبِعۡ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِ فَإِنَّهُۥ يَأۡمُرُ بِٱلۡفَحۡشَآءِ وَٱلۡمُنكَرِۚ وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ مَا زَكَىٰ مِنكُم مِّنۡ أَحَدٍ أَبَدٗا وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يُزَكِّي مَن يَشَآءُۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku bi hanyoyin Shaixan, wanda kuwa duk ya bi hanyoyin Shaixan, to lalle shi (Shaixan) umarni yake yi da aikata alfasha da abin qyama. Ba don kuma falalar Allah a gare ku da rahamarsa ba, da babu xaya daga cikinku da zai tsarkaka har abada, sai dai kuma Allah (Shi) Yake tsarkake wanda Ya ga dama, Allah kuwa Mai ji ne, Masani



Surah: Suratun Namli

Ayah : 73

وَإِنَّ رَبَّكَ لَذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَشۡكُرُونَ

Kuma lalle Ubangijinka Mai falala ne ga mutane, sai dai kuma yawancinsu ba sa godewa



Surah: Suratu Luqman

Ayah : 20

أَلَمۡ تَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ سَخَّرَ لَكُم مَّا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَأَسۡبَغَ عَلَيۡكُمۡ نِعَمَهُۥ ظَٰهِرَةٗ وَبَاطِنَةٗۗ وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُجَٰدِلُ فِي ٱللَّهِ بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَلَا هُدٗى وَلَا كِتَٰبٖ مُّنِيرٖ

Yanzu ba kwa gani cewa Allah Ya hore muku abin da yake cikin sammai da kuma abin da yake cikin qasa, Ya kuma cika muku ni’imominsa na sarari da na voye? Daga mutane kuma akwai waxanda suke jayayya game da Allah ba tare da wani ilimi ko wata shiriya ba, ba kuma tare da wani littafi mai haskakawa ba



Surah: Suratu Luqman

Ayah : 31

أَلَمۡ تَرَ أَنَّ ٱلۡفُلۡكَ تَجۡرِي فِي ٱلۡبَحۡرِ بِنِعۡمَتِ ٱللَّهِ لِيُرِيَكُم مِّنۡ ءَايَٰتِهِۦٓۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّكُلِّ صَبَّارٖ شَكُورٖ

Ba ka gani cewa jiragen ruwa suna tafiya a cikin kogi da ni’imar Allah, don Ya nuna muku (wasu) daga ayoyinsa? Lalle a game da wannan akwai ayoyi ga duk mai yawan haquri, mai yawan godiya



Surah: Suratul Ahzab

Ayah : 9

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَةَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ إِذۡ جَآءَتۡكُمۡ جُنُودٞ فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمۡ رِيحٗا وَجُنُودٗا لَّمۡ تَرَوۡهَاۚ وَكَانَ ٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرًا

Ya ku waxanda suka yi imani, ku tuna ni’imar Allah a gare ku lokacin da wasu rundunoni (na gangankon kafurai) suka zo muku, sai Muka aiko musu iska da wasu rundunoni da ba ku gan su ba[1]. Allah kuwa Ya kasance Mai ganin abin da kuke aikatawa ne


1- Watau su ne rundunonin kafiran Quraishawa da qawayensu waxanda suka nufo Madina a shekara ta 5 don su yaqi Musulmi, amma Allah ya karya su.


Surah: Suratul Ahzab

Ayah : 47

وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ بِأَنَّ لَهُم مِّنَ ٱللَّهِ فَضۡلٗا كَبِيرٗا

Ka kuma yi wa muminai albishir cewa, suna da wata falala mai girma daga wurin Allah



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 3

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ ٱذۡكُرُواْ نِعۡمَتَ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡۚ هَلۡ مِنۡ خَٰلِقٍ غَيۡرُ ٱللَّهِ يَرۡزُقُكُم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِۚ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ فَأَنَّىٰ تُؤۡفَكُونَ

Ya ku mutane, ku tuna ni’imar Allah a gare ku. Yanzu akwai wani mahalicci ban da Allah wanda zai arzuta ku daga sama da qasa? Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. To ta yaya ake karkatar da ku?



Surah: Suratu Sad

Ayah : 9

أَمۡ عِندَهُمۡ خَزَآئِنُ رَحۡمَةِ رَبِّكَ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡوَهَّابِ

Ko kuwa a wurinsu ne taskokin rahamar Ubangijinka Mabuwayi Mai baiwa suke?



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 61

ٱللَّهُ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلَّيۡلَ لِتَسۡكُنُواْ فِيهِ وَٱلنَّهَارَ مُبۡصِرًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلنَّاسِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يَشۡكُرُونَ

Allah ne wanda Ya halitta muku dare don ku natsu a cikinsa, rana kuma don ku ga (yadda za ku yi harka). Lalle Allah Mai falala ne ga mutane, sai dai kuma yawancinsu ba sa godewa



Surah: Suratus Shura

Ayah : 26

وَيَسۡتَجِيبُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَيَزِيدُهُم مِّن فَضۡلِهِۦۚ وَٱلۡكَٰفِرُونَ لَهُمۡ عَذَابٞ شَدِيدٞ

Kuma Yana amsa wa waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, Yana kuma qara musu daga falalarsa. Kafirai kuwa suna da azaba mai tsanani



Surah: Suratus Shura

Ayah : 49

لِّلَّهِ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ يَخۡلُقُ مَا يَشَآءُۚ يَهَبُ لِمَن يَشَآءُ إِنَٰثٗا وَيَهَبُ لِمَن يَشَآءُ ٱلذُّكُورَ

Mulkin sammai da qasa na Allah ne. Yana halittar abin da Ya ga dama. Yana ba da `ya`ya mata ga wanda Ya ga dama, Yana kuma ba da `ya`ya maza ga wanda Ya ga dama



Surah: Suratul Hujurat

Ayah : 7

وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ فِيكُمۡ رَسُولَ ٱللَّهِۚ لَوۡ يُطِيعُكُمۡ فِي كَثِيرٖ مِّنَ ٱلۡأَمۡرِ لَعَنِتُّمۡ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ حَبَّبَ إِلَيۡكُمُ ٱلۡإِيمَٰنَ وَزَيَّنَهُۥ فِي قُلُوبِكُمۡ وَكَرَّهَ إِلَيۡكُمُ ٱلۡكُفۡرَ وَٱلۡفُسُوقَ وَٱلۡعِصۡيَانَۚ أُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلرَّـٰشِدُونَ

Kuma ku sani cewa Manzon Allah yana cikinku. Da zai biye muku game da al’amura masu yawa, tabbas da kun wahala, sai dai kuma Allah Ya sa muku son imani Ya kuma qawata shi a cikin zukatanku, Ya kuma sa muku qin kafirci da fasiqanci da savo. Waxannan su ne shiryayyu



Surah: Suratul Hujurat

Ayah : 8

فَضۡلٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَنِعۡمَةٗۚ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ

(Wannan) falala ce daga Allah da kuma ni’ima, Allah kuwa Masani ne, Mai hikima



Surah: Suratul Hadid

Ayah : 21

سَابِقُوٓاْ إِلَىٰ مَغۡفِرَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ وَجَنَّةٍ عَرۡضُهَا كَعَرۡضِ ٱلسَّمَآءِ وَٱلۡأَرۡضِ أُعِدَّتۡ لِلَّذِينَ ءَامَنُواْ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦۚ ذَٰلِكَ فَضۡلُ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ

Ku yi rige-rige zuwa neman gafara daga Ubangijinku da Aljanna wadda faxinta kamar faxin sammai da qasa yake, an tanade ta don waxanda suka yi imani da Allah da manzanninsa. Wannan falalar Allah ce da Yake ba da ita ga wanda Ya ga dama. Allah kuwa Ma’abocin falala ne, Mai girma



Surah: Suratul Hadid

Ayah : 29

لِّئَلَّا يَعۡلَمَ أَهۡلُ ٱلۡكِتَٰبِ أَلَّا يَقۡدِرُونَ عَلَىٰ شَيۡءٖ مِّن فَضۡلِ ٱللَّهِ وَأَنَّ ٱلۡفَضۡلَ بِيَدِ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ

Don ma’abota littafi su san cewa ba su da hannu a falalar Allah, don ko lalle falala a hannun Allah take, Yana ba da ita ga wanda Ya ga dama. Allah kuma Ma’abocin babbar falala ne



Surah: Suratul Jumu’a

Ayah : 4

ذَٰلِكَ فَضۡلُ ٱللَّهِ يُؤۡتِيهِ مَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ ذُو ٱلۡفَضۡلِ ٱلۡعَظِيمِ

Wannan falala ce daga Allah, Yana bayar da ita ga wanda Ya ga dama. Allah kuwa Ma’abocin babbar falala ne



Surah: Suratud Dhuha

Ayah : 11

وَأَمَّا بِنِعۡمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثۡ

Amma kuma game da ni’imar Ubangijinka sai ka ba da labari