Surah: Suratul Baqara

Ayah : 177

۞لَّيۡسَ ٱلۡبِرَّ أَن تُوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ قِبَلَ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ وَلَٰكِنَّ ٱلۡبِرَّ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ وَٱلۡكِتَٰبِ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ وَءَاتَى ٱلۡمَالَ عَلَىٰ حُبِّهِۦ ذَوِي ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَٰمَىٰ وَٱلۡمَسَٰكِينَ وَٱبۡنَ ٱلسَّبِيلِ وَٱلسَّآئِلِينَ وَفِي ٱلرِّقَابِ وَأَقَامَ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَى ٱلزَّكَوٰةَ وَٱلۡمُوفُونَ بِعَهۡدِهِمۡ إِذَا عَٰهَدُواْۖ وَٱلصَّـٰبِرِينَ فِي ٱلۡبَأۡسَآءِ وَٱلضَّرَّآءِ وَحِينَ ٱلۡبَأۡسِۗ أُوْلَـٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ صَدَقُواْۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُتَّقُونَ

Ba wai aikin xa’a shi ne ku juyar da fuskokinku mahudar rana ko mafaxarta ba ; sai dai aikin xa’a shi ne, wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira da mala’iku da littattafai da annabawa, kuma ya bayar da dukiyarsa, alhalin yana son ta, ga dangi na kusa da marayu da mabuqata da matafiyi da kuma masu roqo (bisa larura) da ‘yantar da bayi, sannan kuma ya tsayar da salla, kuma ya bayar da zakka, da kuma masu cika alqawarinsu idan suka qulla alqawari ; da masu haquri a cikin halin talauci da halin rashin lafiya da lokacin yaqi. Waxannan su ne waxanda suka yi gaskiya, kuma waxannan su ne masu taqawa



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 224

وَلَا تَجۡعَلُواْ ٱللَّهَ عُرۡضَةٗ لِّأَيۡمَٰنِكُمۡ أَن تَبَرُّواْ وَتَتَّقُواْ وَتُصۡلِحُواْ بَيۡنَ ٱلنَّاسِۚ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٞ

Kuma kada ku mayar da Allah Ya zamanto kariya ga rantse-rantsenku don su hana ku aiki na xa’a ko na taqawa ko na sulhu tsakanin mutane. Kuma Allah Mai ji ne, Masani



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 277

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوٰةَ لَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Lalle waxanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka nagari kuma suka tsayar da salla, kuma suka bayar da zakka, to suna da ladansu a wajen Ubangijinsu, kuma babu jin tsoro a gare su, kuma ba za su yi baqin ciki ba



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 57

وَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فَيُوَفِّيهِمۡ أُجُورَهُمۡۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Amma kuma waxanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyuka nagari, to (Allah) zai cika musu ladansu. Kuma Allah ba Ya son azzalumai



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 92

لَن تَنَالُواْ ٱلۡبِرَّ حَتَّىٰ تُنفِقُواْ مِمَّا تُحِبُّونَۚ وَمَا تُنفِقُواْ مِن شَيۡءٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ بِهِۦ عَلِيمٞ

Ba za ku tava dacewa da aiki na alheri ba har sai kun ciyar daga abin da kuke so, kuma abin da duk kuka ciyar kowane iri ne, to lalle Allah Yana sane da shi



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 133

۞وَسَارِعُوٓاْ إِلَىٰ مَغۡفِرَةٖ مِّن رَّبِّكُمۡ وَجَنَّةٍ عَرۡضُهَا ٱلسَّمَٰوَٰتُ وَٱلۡأَرۡضُ أُعِدَّتۡ لِلۡمُتَّقِينَ

Kuma ku yi gaggawa zuwa ga neman gafara ta musamman daga wajen Ubangijinku, da kuma Aljanna wadda faxinta yake daidai da sammai da qasa, an yi tanadinta domin masu taqawa



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 134

ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ فِي ٱلسَّرَّآءِ وَٱلضَّرَّآءِ وَٱلۡكَٰظِمِينَ ٱلۡغَيۡظَ وَٱلۡعَافِينَ عَنِ ٱلنَّاسِۗ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

(Su ne) waxanda suke ciyarwa a cikin halin yalwa da halin qunci, kuma masu voye fushi kuma masu yin afuwa ga mutane. Allah kuwa Yana son masu kyautatawa



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 135

وَٱلَّذِينَ إِذَا فَعَلُواْ فَٰحِشَةً أَوۡ ظَلَمُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ ذَكَرُواْ ٱللَّهَ فَٱسۡتَغۡفَرُواْ لِذُنُوبِهِمۡ وَمَن يَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ إِلَّا ٱللَّهُ وَلَمۡ يُصِرُّواْ عَلَىٰ مَا فَعَلُواْ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ

(Su ne) kuma waxanda idan sun aikata mummunan aiki, ko suka zalunci kansu, nan take sai su tuna da Allah, sai su nemi gafarar zunubansu. Wane ne kuwa mai gafarta zunubbai in ba Allah ba? Kuma ba sa zarcewa a kan abin da suka yi, alhali suna sane



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 199

وَإِنَّ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ لَمَن يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكُمۡ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِمۡ خَٰشِعِينَ لِلَّهِ لَا يَشۡتَرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ ثَمَنٗا قَلِيلًاۚ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

Kuma lalle a cikin Ma’abota Littafi, tabbas akwai waxanda suke yin imani da Allah da kuma abin da aka saukar muku da kuma abin da aka saukar musu, suna masu qasqantar da kai ga Allah, ba sa musanya ayoyin Allah da wani xan farashi qanqani. Waxannan suna da lada a wajen Ubangijinsu. Lalle Allah Mai gaggawar hisabi ne



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 124

وَمَن يَعۡمَلۡ مِنَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ مِن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَأُوْلَـٰٓئِكَ يَدۡخُلُونَ ٱلۡجَنَّةَ وَلَا يُظۡلَمُونَ نَقِيرٗا

Kuma wanda ya yi wani aiki nagari, namiji ne ko mace, alhali yana mumini, to waxannan za su shiga Aljanna, kuma ba za a zalunce su gwargwadon xigon bayan qwallon dabino ba



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 2

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُحِلُّواْ شَعَـٰٓئِرَ ٱللَّهِ وَلَا ٱلشَّهۡرَ ٱلۡحَرَامَ وَلَا ٱلۡهَدۡيَ وَلَا ٱلۡقَلَـٰٓئِدَ وَلَآ ءَآمِّينَ ٱلۡبَيۡتَ ٱلۡحَرَامَ يَبۡتَغُونَ فَضۡلٗا مِّن رَّبِّهِمۡ وَرِضۡوَٰنٗاۚ وَإِذَا حَلَلۡتُمۡ فَٱصۡطَادُواْۚ وَلَا يَجۡرِمَنَّكُمۡ شَنَـَٔانُ قَوۡمٍ أَن صَدُّوكُمۡ عَنِ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ أَن تَعۡتَدُواْۘ وَتَعَاوَنُواْ عَلَى ٱلۡبِرِّ وَٱلتَّقۡوَىٰۖ وَلَا تَعَاوَنُواْ عَلَى ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ شَدِيدُ ٱلۡعِقَابِ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku halatta keta alfarmar alamomin addinin Allah, ko (ku wulaqanta) Wata mai alfarma[1] ko dabbobin hadaya ko dabbobin hadaya masu alama da (tare) masu nufin ziyarar Xaki mai alfarma, suna neman falala daga wurin Ubangijinsu da yardarsa. Idan kuwa kuka kwance Harami, to ku yi farauta (idan kuna so). Kuma kada qiyayyar wasu mutane da suka hana ku isa masallaci mai alfarma, ta sa ku yi ta’addanci. Kuma ku taimaki juna a kan aikin alheri da taqawa; kada kuma ku taimaka wa juna a kan ayyukan savo da ta’addanci. Kuma ku kiyaye dokokin Allah; lalle Allah Mai tsananin uquba ne


1- Watanni masu alfarma su ne: Zulqi’ida, Zulhijja, Al-Muharram da Rajab. An haramta yaqi a cikinsu.


Surah: Suratul A’araf

Ayah : 42

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَا نُكَلِّفُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَآ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Waxanda kuwa suka yi imani, kuma suka aikata kyawawan ayyuka, ba ma xora wa rai, sai abin da zai iya, waxannan su ne ‘yan Aljanna, su masu dawwama ne a cikinta



Surah: Suratul Anfal

Ayah : 1

يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلۡأَنفَالِۖ قُلِ ٱلۡأَنفَالُ لِلَّهِ وَٱلرَّسُولِۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَصۡلِحُواْ ذَاتَ بَيۡنِكُمۡۖ وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥٓ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ

Suna tambayar ka game da ganimomi[1]; ka ce (da su): “Ganimomi na Allah ne da kuma Manzo; saboda haka ku kiyaye dokokin Allah, ku kuma gyara tsakaninku, kuma ku bi Allah da Manzonsa, idan kun kasance muminai.”


1- Watau tambayar da sahabbai suka yi wa Annabi () game da hukuncin ganimar yaqin Badar.


Surah: Suratun Nahl

Ayah : 97

مَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَنُحۡيِيَنَّهُۥ حَيَوٰةٗ طَيِّبَةٗۖ وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Wanda ya yi kyakkyawan aiki namiji ko mace alhali shi yana mumini, to lalle za Mu raya shi rayuwa mai daxi, kuma za Mu saka musu ladansu da mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 22

لَّا تَجۡعَلۡ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَتَقۡعُدَ مَذۡمُومٗا مَّخۡذُولٗا

Kada ka haxa wani abin bauta daban tare da Allah, sai ka zama abin zargi tavavve



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 23

۞وَقَضَىٰ رَبُّكَ أَلَّا تَعۡبُدُوٓاْ إِلَّآ إِيَّاهُ وَبِٱلۡوَٰلِدَيۡنِ إِحۡسَٰنًاۚ إِمَّا يَبۡلُغَنَّ عِندَكَ ٱلۡكِبَرَ أَحَدُهُمَآ أَوۡ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُل لَّهُمَآ أُفّٖ وَلَا تَنۡهَرۡهُمَا وَقُل لَّهُمَا قَوۡلٗا كَرِيمٗا

Ubangijinka kuwa Ya hukunta cewa, kada ku bauta wa (wani) sai Shi kaxai, kuma ku kyautatawa iyaye. Ko dai ya zamanto xayansu ne ya manyanta tare da kai, ko kuma dukkansu, to kada ka nuna qosawarka da su, kada kuma ka daka musu tsawa; ka yi musu magana ta girmamawa



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 24

وَٱخۡفِضۡ لَهُمَا جَنَاحَ ٱلذُّلِّ مِنَ ٱلرَّحۡمَةِ وَقُل رَّبِّ ٱرۡحَمۡهُمَا كَمَا رَبَّيَانِي صَغِيرٗا

Ka kuma qasqantar da kai gare su don tausayawa, ka kuma ce: “Ubangijina Ka ji qan su kamar yadda suka raine ni ina xan qarami.”



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 25

رَّبُّكُمۡ أَعۡلَمُ بِمَا فِي نُفُوسِكُمۡۚ إِن تَكُونُواْ صَٰلِحِينَ فَإِنَّهُۥ كَانَ لِلۡأَوَّـٰبِينَ غَفُورٗا

Ubangijinku ne Mafi sanin abin da yake zukatanku. Idan kuka zamanto nagari, to lalle Shi Ya tabbata Mai gafara ne ga masu komawa gare Shi da tuba



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 26

وَءَاتِ ذَا ٱلۡقُرۡبَىٰ حَقَّهُۥ وَٱلۡمِسۡكِينَ وَٱبۡنَ ٱلسَّبِيلِ وَلَا تُبَذِّرۡ تَبۡذِيرًا

Kuma ka bai wa makusanci haqqinsa, da miskini da matafiyi, kada kuma ka yi kowane irin almubazzaranci



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 27

إِنَّ ٱلۡمُبَذِّرِينَ كَانُوٓاْ إِخۡوَٰنَ ٱلشَّيَٰطِينِۖ وَكَانَ ٱلشَّيۡطَٰنُ لِرَبِّهِۦ كَفُورٗا

Lalle masu almubazzaranci sun tabbata dangin shaixanu; Shaixan kuwa ya zamanto mai yawan kafirce wa Ubangijinsa ne



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 28

وَإِمَّا تُعۡرِضَنَّ عَنۡهُمُ ٱبۡتِغَآءَ رَحۡمَةٖ مِّن رَّبِّكَ تَرۡجُوهَا فَقُل لَّهُمۡ قَوۡلٗا مَّيۡسُورٗا

Idan kuwa ka kau da kanka daga gare su don neman wata rahama daga Ubangijinka da kake sa ran samun ta[1], to sai ka yi musu magana mai daxi


1- Watau idan masu neman taimako a wurinsa suka zo ba ya da shi, shi ma yana jiran Allah ya hore masa.


Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 29

وَلَا تَجۡعَلۡ يَدَكَ مَغۡلُولَةً إِلَىٰ عُنُقِكَ وَلَا تَبۡسُطۡهَا كُلَّ ٱلۡبَسۡطِ فَتَقۡعُدَ مَلُومٗا مَّحۡسُورًا

Kada kuma ka ququnce hannunka a wuyanka (ka qi yin kyauta), kada kuma ka shimfixa shi gaba xaya (watau ka saki komai), sai ka wayi gari abin zargi (saboda rowa), mai nadama (saboda almubazaranci)



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 30

إِنَّ رَبَّكَ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِعِبَادِهِۦ خَبِيرَۢا بَصِيرٗا

Lalle Ubangijinka Yana shimfixa arziki ga wanda Ya ga dama, kuma Yana quntatawa (ga wanda Ya ga dama). Lalle Shi Ya tabbata Masani ne, Mai ganin bayinsa



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 31

وَلَا تَقۡتُلُوٓاْ أَوۡلَٰدَكُمۡ خَشۡيَةَ إِمۡلَٰقٖۖ نَّحۡنُ نَرۡزُقُهُمۡ وَإِيَّاكُمۡۚ إِنَّ قَتۡلَهُمۡ كَانَ خِطۡـٔٗا كَبِيرٗا

Kada kuma ku kashe ‘ya’yayenku don tsoron talauci: Mu ne Muke arzuta su har ma da ku. Lalle kashe su kuskure ne babba



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 32

وَلَا تَقۡرَبُواْ ٱلزِّنَىٰٓۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَٰحِشَةٗ وَسَآءَ سَبِيلٗا

Kuma kada ku kusanci zina; lalle ita (zina) ta kasance mugun aiki ne, kuma hanya ce wadda ta munana



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 33

وَلَا تَقۡتُلُواْ ٱلنَّفۡسَ ٱلَّتِي حَرَّمَ ٱللَّهُ إِلَّا بِٱلۡحَقِّۗ وَمَن قُتِلَ مَظۡلُومٗا فَقَدۡ جَعَلۡنَا لِوَلِيِّهِۦ سُلۡطَٰنٗا فَلَا يُسۡرِف فِّي ٱلۡقَتۡلِۖ إِنَّهُۥ كَانَ مَنصُورٗا

Kuma kada ku kashe ran da Allah Ya haramta (kashewa) sai da haqqi. Wanda aka kashe ta hanyar zalunci, to lalle Mun bai wa magajinsa dama (ta ramuwa)[1], to (amma) kada ya wuce gona da iri wajen kisa; lalle shi ya zamanto abin dafa wa baya ne


1- Watau ta hanyar shari’a.


Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 34

وَلَا تَقۡرَبُواْ مَالَ ٱلۡيَتِيمِ إِلَّا بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ حَتَّىٰ يَبۡلُغَ أَشُدَّهُۥۚ وَأَوۡفُواْ بِٱلۡعَهۡدِۖ إِنَّ ٱلۡعَهۡدَ كَانَ مَسۡـُٔولٗا

Kuma kada ku kusanci dukiyar maraya sai dai ta (hanya) wadda take mafi kyau[1], har sai ya kawo qarfi. Kuma ku cika alqawari; lalle alqawari ya kasance abin tambaya ne (a lahira)


1- Watau ta hanyar yi masa kasuwanci da ita.


Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 35

وَأَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ إِذَا كِلۡتُمۡ وَزِنُواْ بِٱلۡقِسۡطَاسِ ٱلۡمُسۡتَقِيمِۚ ذَٰلِكَ خَيۡرٞ وَأَحۡسَنُ تَأۡوِيلٗا

Kuma ku cika mudu idan kuka yi awo, kuma ku auna nauyi da ma’auni na adalci. Wannan (shi ya fi) alheri ya kuma fi kyakkyawan qarshe



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 36

وَلَا تَقۡفُ مَا لَيۡسَ لَكَ بِهِۦ عِلۡمٌۚ إِنَّ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡبَصَرَ وَٱلۡفُؤَادَ كُلُّ أُوْلَـٰٓئِكَ كَانَ عَنۡهُ مَسۡـُٔولٗا

Kada kuma ka dinga bibiyar abin da ba ka da ilimi a kansa. Lalle ji da gani da kuma tunani duk waxannan sun zama abin tambaya ne game da su



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 37

وَلَا تَمۡشِ فِي ٱلۡأَرۡضِ مَرَحًاۖ إِنَّكَ لَن تَخۡرِقَ ٱلۡأَرۡضَ وَلَن تَبۡلُغَ ٱلۡجِبَالَ طُولٗا

Kada kuma ka yi tafiya a bayan qasa kana mai girman kai; lalle kai ba za ka tsaga qasa ba (don qasaita) kuma ba za ka kai tsawon duwatsu ba