Surah: Suratul Fatiha

Ayah : 4

مَٰلِكِ يَوۡمِ ٱلدِّينِ

Mamallakin ranar sakamako



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 112

بَلَىٰۚ مَنۡ أَسۡلَمَ وَجۡهَهُۥ لِلَّهِ وَهُوَ مُحۡسِنٞ فَلَهُۥٓ أَجۡرُهُۥ عِندَ رَبِّهِۦ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

E! Wanda ya miqa fuskarsa ga Allah alhali yana mai kyautata aikinsa, to yana da ladansa a wajen Ubangijinsa, kuma babu tsoro a tare da su kuma ba za su yi baqin ciki ba



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 261

مَّثَلُ ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ كَمَثَلِ حَبَّةٍ أَنۢبَتَتۡ سَبۡعَ سَنَابِلَ فِي كُلِّ سُنۢبُلَةٖ مِّاْئَةُ حَبَّةٖۗ وَٱللَّهُ يُضَٰعِفُ لِمَن يَشَآءُۚ وَٱللَّهُ وَٰسِعٌ عَلِيمٌ

Misalin waxanda suke ciyar da dukiyoyinsu a hanyar Allah, kamar misalin qwaya xaya ce da ta fitar da zangarniya bakwai, a cikinta kowace zangarniya kuma (aka sami) qwaya xari. Kuma Allah Yana ninninkawa ga wanda Ya ga dama, kuma Allah Mai yalwa ne, Masani



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 262

ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُمۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ثُمَّ لَا يُتۡبِعُونَ مَآ أَنفَقُواْ مَنّٗا وَلَآ أَذٗى لَّهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Waxanda suke ciyar da dukiyoyinsu a hanyar Allah, sannan ba sa bin abin da suka ciyar da gori ko cuta, (waxannan) suna da ladansu a wajen Ubangijinsu, kuma babu tsoro a tare da su, kuma ba za su yi baqin ciki ba



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 274

ٱلَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمۡوَٰلَهُم بِٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِ سِرّٗا وَعَلَانِيَةٗ فَلَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Waxanda suke ciyar da dukiyoyinsu dare da rana a voye da kuma a sarari, to suna da ladansu a wajen Ubangijinsu, kuma babu tsoro a tare da su, kuma ba za su yi baqin ciki ba



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 277

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَوُاْ ٱلزَّكَوٰةَ لَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Lalle waxanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka nagari kuma suka tsayar da salla, kuma suka bayar da zakka, to suna da ladansu a wajen Ubangijinsu, kuma babu jin tsoro a gare su, kuma ba za su yi baqin ciki ba



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 57

وَأَمَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فَيُوَفِّيهِمۡ أُجُورَهُمۡۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Amma kuma waxanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyuka nagari, to (Allah) zai cika musu ladansu. Kuma Allah ba Ya son azzalumai



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 136

أُوْلَـٰٓئِكَ جَزَآؤُهُم مَّغۡفِرَةٞ مِّن رَّبِّهِمۡ وَجَنَّـٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَنِعۡمَ أَجۡرُ ٱلۡعَٰمِلِينَ

Waxannan sakamakonsu shi ne gafara ta musamman daga Ubangijinsu, da gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu. Kuma madalla da sakamakon masu aiki



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 145

وَمَا كَانَ لِنَفۡسٍ أَن تَمُوتَ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِ كِتَٰبٗا مُّؤَجَّلٗاۗ وَمَن يُرِدۡ ثَوَابَ ٱلدُّنۡيَا نُؤۡتِهِۦ مِنۡهَا وَمَن يُرِدۡ ثَوَابَ ٱلۡأٓخِرَةِ نُؤۡتِهِۦ مِنۡهَاۚ وَسَنَجۡزِي ٱلشَّـٰكِرِينَ

Kuma babu wani rai da zai mutu sai da izinin Allah, rubutaccen abu ne qayyadajje. Kuma duk wanda yake nufin sakamakon duniya, za Mu ba shi daga gare ta, wanda kuma yake nufin sakamakon lahira, to za Mu ba shi daga gare ta. Kuma da sannu za Mu saka ma masu godiya



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 148

فَـَٔاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ ثَوَابَ ٱلدُّنۡيَا وَحُسۡنَ ثَوَابِ ٱلۡأٓخِرَةِۗ وَٱللَّهُ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Sai Allah Ya ba su ladan duniya da kyakkyawan lada na lahira. Kuma Allah Yana son masu kyautatawa



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 171

۞يَسۡتَبۡشِرُونَ بِنِعۡمَةٖ مِّنَ ٱللَّهِ وَفَضۡلٖ وَأَنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Suna ta farin ciki da ni’ima daga Allah da falala, kuma Allah ba Ya tozarta ladan masu imani



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 172

ٱلَّذِينَ ٱسۡتَجَابُواْ لِلَّهِ وَٱلرَّسُولِ مِنۢ بَعۡدِ مَآ أَصَابَهُمُ ٱلۡقَرۡحُۚ لِلَّذِينَ أَحۡسَنُواْ مِنۡهُمۡ وَٱتَّقَوۡاْ أَجۡرٌ عَظِيمٌ

Waxanda suka amsa kiran Allah da Manzo bayan miki ya same su a jikinsu[1]. Lalle waxanda suka kyautata a cikinsu, kuma suka yi taqawa, suna da lada mai girma


1- Bayan dawowa daga yaqin Uhudu, Annabi () ya nemi sahabbai da su koma don su tunkari kafirai da aka samu labarin za su sake dawo wa Madina yaqarsa. Aka fita har da masu raunuka a jikinsu.


Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 195

فَٱسۡتَجَابَ لَهُمۡ رَبُّهُمۡ أَنِّي لَآ أُضِيعُ عَمَلَ عَٰمِلٖ مِّنكُم مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰۖ بَعۡضُكُم مِّنۢ بَعۡضٖۖ فَٱلَّذِينَ هَاجَرُواْ وَأُخۡرِجُواْ مِن دِيَٰرِهِمۡ وَأُوذُواْ فِي سَبِيلِي وَقَٰتَلُواْ وَقُتِلُواْ لَأُكَفِّرَنَّ عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡ وَلَأُدۡخِلَنَّهُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ ثَوَابٗا مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِۚ وَٱللَّهُ عِندَهُۥ حُسۡنُ ٱلثَّوَابِ

Sai Ubangijinsu Ya amsa musu (cewa): “Lalle Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki daga cikinku ba, namiji ne ko mace; sashinku yana tare da sashe. To waxanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidajensu kuma aka cutar da su wajen bin tafarkina kuma suka yi yaqi kuma aka kashe su, lalle zan kankare musu kurakuransu, kuma lalle zan shigar da su gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu. (Wannan) lada ne daga wajen Allah, kuma a wurin Allah ne mafi kyawun lada yake.”



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 199

وَإِنَّ مِنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ لَمَن يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكُمۡ وَمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِمۡ خَٰشِعِينَ لِلَّهِ لَا يَشۡتَرُونَ بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ ثَمَنٗا قَلِيلًاۚ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡۗ إِنَّ ٱللَّهَ سَرِيعُ ٱلۡحِسَابِ

Kuma lalle a cikin Ma’abota Littafi, tabbas akwai waxanda suke yin imani da Allah da kuma abin da aka saukar muku da kuma abin da aka saukar musu, suna masu qasqantar da kai ga Allah, ba sa musanya ayoyin Allah da wani xan farashi qanqani. Waxannan suna da lada a wajen Ubangijinsu. Lalle Allah Mai gaggawar hisabi ne



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 40

إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَظۡلِمُ مِثۡقَالَ ذَرَّةٖۖ وَإِن تَكُ حَسَنَةٗ يُضَٰعِفۡهَا وَيُؤۡتِ مِن لَّدُنۡهُ أَجۡرًا عَظِيمٗا

Lalle Allah ba Ya zalunci ko da daidai da nauyin jaririyar tururuwa; kuma idan ya kasance aiki ne mai kyau to zai ninka shi, kuma Ya ba da lada mai girma daga wurinsa



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 74

۞فَلۡيُقَٰتِلۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ ٱلَّذِينَ يَشۡرُونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا بِٱلۡأٓخِرَةِۚ وَمَن يُقَٰتِلۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَيُقۡتَلۡ أَوۡ يَغۡلِبۡ فَسَوۡفَ نُؤۡتِيهِ أَجۡرًا عَظِيمٗا

To waxanda suke sayen rayuwar lahira da ta duniya, sai su yi yaqi don xaukaka kalmar Allah. Duk wanda yake yin yaqi don xaukaka kalmar Allah kuwa, sai aka kashe shi ko kuma ya yi galaba, to za Mu ba shi lada mai girma



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 100

۞وَمَن يُهَاجِرۡ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ يَجِدۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُرَٰغَمٗا كَثِيرٗا وَسَعَةٗۚ وَمَن يَخۡرُجۡ مِنۢ بَيۡتِهِۦ مُهَاجِرًا إِلَى ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ ثُمَّ يُدۡرِكۡهُ ٱلۡمَوۡتُ فَقَدۡ وَقَعَ أَجۡرُهُۥ عَلَى ٱللَّهِۗ وَكَانَ ٱللَّهُ غَفُورٗا رَّحِيمٗا

Kuma duk wanda ya yi hijira saboda Allah, zai samu wuraren hijira masu yawa da yalwa a bayan qasa. Kuma duk wanda ya fita daga gidansa, yana mai hijira zuwa ga Allah da Manzonsa, sannan mutuwa ta riske shi, to haqiqa ladansa ya tabbata a wajen Allah. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan gafara ne, Mai yawan jin qai



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 134

مَّن كَانَ يُرِيدُ ثَوَابَ ٱلدُّنۡيَا فَعِندَ ٱللَّهِ ثَوَابُ ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ سَمِيعَۢا بَصِيرٗا

Duk wanda ya kasance yana son ladan duniya, to ladan duniya da na lahira duk a hannun Allah suke. Kuma Allah Ya kasance Mai ji ne, Mai gani



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 170

وَٱلَّذِينَ يُمَسِّكُونَ بِٱلۡكِتَٰبِ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ إِنَّا لَا نُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُصۡلِحِينَ

Waxanda kuwa suke riqo da Littafi, kuma suke tsayar da salla, to lalle Mu ba ma tozarta ladan masu gyara



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 21

يُبَشِّرُهُمۡ رَبُّهُم بِرَحۡمَةٖ مِّنۡهُ وَرِضۡوَٰنٖ وَجَنَّـٰتٖ لَّهُمۡ فِيهَا نَعِيمٞ مُّقِيمٌ

Ubangijinsu Yana yi musu albishir da rahama da yarda daga gare Shi, kana da gidajen Aljanna (waxanda) a cikinsu suke da ni’imomi masu xorewa



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 22

خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ عِندَهُۥٓ أَجۡرٌ عَظِيمٞ

Su madawwama ne a cikinsu har abada. Lalle lada mai girma yana wurin Allah



Surah: Suratu Hud

Ayah : 115

وَٱصۡبِرۡ فَإِنَّ ٱللَّهَ لَا يُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kuma ka yi haquri, domin lalle Allah ba Ya tozarta ladan masu kyautatawa



Surah: Suratu Yusuf 

Ayah : 56

وَكَذَٰلِكَ مَكَّنَّا لِيُوسُفَ فِي ٱلۡأَرۡضِ يَتَبَوَّأُ مِنۡهَا حَيۡثُ يَشَآءُۚ نُصِيبُ بِرَحۡمَتِنَا مَن نَّشَآءُۖ وَلَا نُضِيعُ أَجۡرَ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kamar haka ne Muka kafa Yusufu a bayan qasa; yana zama a cikinta inda ya ga dama. Muna bayar da rahamarmu ga wanda Muka ga dama, ba kuwa za Mu tozarta ladan masu kyautatawa ba



Surah: Suratu Yusuf 

Ayah : 57

وَلَأَجۡرُ ٱلۡأٓخِرَةِ خَيۡرٞ لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَكَانُواْ يَتَّقُونَ

Kuma lalle ladan lahira shi ya fi ga waxanda suka yi imani kuma suka zamanto suna kiyaye dokokin (Allah)



Surah: Suratun Nahl

Ayah : 41

وَٱلَّذِينَ هَاجَرُواْ فِي ٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ مَا ظُلِمُواْ لَنُبَوِّئَنَّهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا حَسَنَةٗۖ وَلَأَجۡرُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَكۡبَرُۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ

Waxanda kuma suka yi hijira saboda Allah bayan an zalunce su lalle za Mu shirya musu kyakkyawar (rayuwa) a duniya; ladan lahira kuma ya fi girma da a ce sun kasance suna sane da (haka)



Surah: Suratun Nahl

Ayah : 96

مَا عِندَكُمۡ يَنفَدُ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ بَاقٖۗ وَلَنَجۡزِيَنَّ ٱلَّذِينَ صَبَرُوٓاْ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Abin da yake wurinku yana qarewa; abin da kuwa yake wurin Allah wanzajje ne. Lalle kuwa tabbas za Mu saka wa waxanda suka yi haquri ladansu da mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa



Surah: Suratun Nahl

Ayah : 97

مَنۡ عَمِلَ صَٰلِحٗا مِّن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَلَنُحۡيِيَنَّهُۥ حَيَوٰةٗ طَيِّبَةٗۖ وَلَنَجۡزِيَنَّهُمۡ أَجۡرَهُم بِأَحۡسَنِ مَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ

Wanda ya yi kyakkyawan aiki namiji ko mace alhali shi yana mumini, to lalle za Mu raya shi rayuwa mai daxi, kuma za Mu saka musu ladansu da mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa



Surah: Suratul Kahf 

Ayah : 30

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ إِنَّا لَا نُضِيعُ أَجۡرَ مَنۡ أَحۡسَنَ عَمَلًا

Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari tabbas Mu ba ma tozarta ladan wanda ya kyautata aiki



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 75

وَمَن يَأۡتِهِۦ مُؤۡمِنٗا قَدۡ عَمِلَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمُ ٱلدَّرَجَٰتُ ٱلۡعُلَىٰ

Wanda kuwa ya zo masa yana mumini ya zamana ya yi aiki na gari, to waxannan suna da (sakamakon samun) darajoji maxaukaka



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 76

جَنَّـٰتُ عَدۡنٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ جَزَآءُ مَن تَزَكَّىٰ

(Watau) gidajen Aljanna na dawwama waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, masu dawwama ne a cikinsu. Wannan kuwa shi ne sakamakon wanda ya tsarkaka (daga savo)