Surah: Suratul Baqara

Ayah : 96

وَلَتَجِدَنَّهُمۡ أَحۡرَصَ ٱلنَّاسِ عَلَىٰ حَيَوٰةٖ وَمِنَ ٱلَّذِينَ أَشۡرَكُواْۚ يَوَدُّ أَحَدُهُمۡ لَوۡ يُعَمَّرُ أَلۡفَ سَنَةٖ وَمَا هُوَ بِمُزَحۡزِحِهِۦ مِنَ ٱلۡعَذَابِ أَن يُعَمَّرَۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِمَا يَعۡمَلُونَ

Kuma lalle za ka same su sun fi kowa kwaxayin tsawon rai, fiye ma da waxanda suka yi shirka. Kowane xayansu yana burin ina ma za a raya shi shekara dubu. Hakan kuma ba zai nesanta shi daga azaba ba don an yi masa tsawon rai. Kuma Allah Mai ganin abin da suka kasance suna aikatawa ne



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 137

فَإِنۡ ءَامَنُواْ بِمِثۡلِ مَآ ءَامَنتُم بِهِۦ فَقَدِ ٱهۡتَدَواْۖ وَّإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا هُمۡ فِي شِقَاقٖۖ فَسَيَكۡفِيكَهُمُ ٱللَّهُۚ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Don haka idan sun yi imani da irin abin da kuka yi imani da shi, to haqiqa sun shiriya, idan kuwa suka juya da baya, to haqiqa su suna cikin savani. To da sannu Allah zai isar maka da su, kuma Shi Mai ji ne, Mai gani



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 144

قَدۡ نَرَىٰ تَقَلُّبَ وَجۡهِكَ فِي ٱلسَّمَآءِۖ فَلَنُوَلِّيَنَّكَ قِبۡلَةٗ تَرۡضَىٰهَاۚ فَوَلِّ وَجۡهَكَ شَطۡرَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۚ وَحَيۡثُ مَا كُنتُمۡ فَوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ شَطۡرَهُۥۗ وَإِنَّ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ لَيَعۡلَمُونَ أَنَّهُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّهِمۡۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا يَعۡمَلُونَ

Haqiqa Mun ga jujjuyawar fuskarka zuwa sama, to lalle za Mu fuskantar da kai zuwa ga alqibilar da za ka yarda da ita. Don haka ka juyar da fuskarka wajajen Masallaci mai alfarma; ku ma (Musulmi) a duk inda kuke to ku juyar da fuskokinku wajajensa. Lalle kuma waxanda aka ba su Littafi suna sane da cewa, lalle shi (wannan canji) gaskiya ne daga Ubangijinsu. Kuma Allah ba rafkananne ba ne game da abin da suke aikatawa



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 20

فَإِنۡ حَآجُّوكَ فَقُلۡ أَسۡلَمۡتُ وَجۡهِيَ لِلَّهِ وَمَنِ ٱتَّبَعَنِۗ وَقُل لِّلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡأُمِّيِّـۧنَ ءَأَسۡلَمۡتُمۡۚ فَإِنۡ أَسۡلَمُواْ فَقَدِ ٱهۡتَدَواْۖ وَّإِن تَوَلَّوۡاْ فَإِنَّمَا عَلَيۡكَ ٱلۡبَلَٰغُۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِٱلۡعِبَادِ

To idan sun yi jayayya da kai, sai ka ce: “Ni na miqa wuyana ne ga Allah, haka ma wanda ya bi ni.” Kuma ka faxa wa waxanda aka bai wa Littafi da Ummiyyai (Larabawa): “Shin kun miqa wuya?” To idan sun miqa wuya, haqiqa sun shiryu; idan kuwa suka juya baya, to babu abin da yake a kanka sai isar da saqo. Kuma Allah Mai ganin bayinsa ne



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 38

هُنَالِكَ دَعَا زَكَرِيَّا رَبَّهُۥۖ قَالَ رَبِّ هَبۡ لِي مِن لَّدُنكَ ذُرِّيَّةٗ طَيِّبَةًۖ إِنَّكَ سَمِيعُ ٱلدُّعَآءِ

A wannan lokacin sai Zakariyya ya roqi Ubangijinsa, ya ce: “Ya Ubangijina, Ka ba ni zurriyya ta gari daga gare Ka, lalle Kai Mai amsa roqo ne.”



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 156

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَقَالُواْ لِإِخۡوَٰنِهِمۡ إِذَا ضَرَبُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ أَوۡ كَانُواْ غُزّٗى لَّوۡ كَانُواْ عِندَنَا مَا مَاتُواْ وَمَا قُتِلُواْ لِيَجۡعَلَ ٱللَّهُ ذَٰلِكَ حَسۡرَةٗ فِي قُلُوبِهِمۡۗ وَٱللَّهُ يُحۡيِۦ وَيُمِيتُۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku kasance kamar waxanda suka kafirta, kuma suka riqa faxa wa ‘yan’uwansu yayin da suka yi tafiya a bayan qasa, ko kuma suka kasance mayaqa: “In da sun kasance tare da mu, ai da ba su mutu ba, kuma da ba a kashe su ba,” don Allah Ya sanya waccan (maganar) ta zamo nadama a cikin zukatansu. Kuma Allah Shi ne Mai rayawa, kuma Shi ne Mai kashewa. Kuma Allah Mai ganin abin da kuke aikatawa ne



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 163

هُمۡ دَرَجَٰتٌ عِندَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِمَا يَعۡمَلُونَ

Su darajoji ne a wajen Allah. Allah kuma Mai ganin abin da suke aikatawa ne



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 181

لَّقَدۡ سَمِعَ ٱللَّهُ قَوۡلَ ٱلَّذِينَ قَالُوٓاْ إِنَّ ٱللَّهَ فَقِيرٞ وَنَحۡنُ أَغۡنِيَآءُۘ سَنَكۡتُبُ مَا قَالُواْ وَقَتۡلَهُمُ ٱلۡأَنۢبِيَآءَ بِغَيۡرِ حَقّٖ وَنَقُولُ ذُوقُواْ عَذَابَ ٱلۡحَرِيقِ

Tabbas haqiqa Allah ya ji maganar waxannan da suka ce: “Lalle Allah mataulaci ne, mu ne mawadata.” Da sannu za Mu rubuta abin da suka faxa, da kuma kisan da suka riqa yi wa annabawa ba tare da wani haqqi ba, kuma za Mu ce: “Ku xanxani azaba mai quna



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 58

۞إِنَّ ٱللَّهَ يَأۡمُرُكُمۡ أَن تُؤَدُّواْ ٱلۡأَمَٰنَٰتِ إِلَىٰٓ أَهۡلِهَا وَإِذَا حَكَمۡتُم بَيۡنَ ٱلنَّاسِ أَن تَحۡكُمُواْ بِٱلۡعَدۡلِۚ إِنَّ ٱللَّهَ نِعِمَّا يَعِظُكُم بِهِۦٓۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ سَمِيعَۢا بَصِيرٗا

Lalle Allah Yana umartar ku da ku mayar da amanoni ga masu su, kuma idan za ku yi hukunci a tsakanin mutane, to ku yi hukunci da adalci. Lalle kam madalla da abin da Allah Yake muku wa’azi da shi. Lalle Allah Ya kasance Mai ji ne, Mai gani



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 148

۞لَّا يُحِبُّ ٱللَّهُ ٱلۡجَهۡرَ بِٱلسُّوٓءِ مِنَ ٱلۡقَوۡلِ إِلَّا مَن ظُلِمَۚ وَكَانَ ٱللَّهُ سَمِيعًا عَلِيمًا

Allah ba Ya son bayyana mummunan zance, sai dai wanda aka zalunce shi. Kuma Allah Ya kasance Mai ji ne, Mai yawan sani



Surah: Suratul An’am

Ayah : 103

لَّا تُدۡرِكُهُ ٱلۡأَبۡصَٰرُ وَهُوَ يُدۡرِكُ ٱلۡأَبۡصَٰرَۖ وَهُوَ ٱللَّطِيفُ ٱلۡخَبِيرُ

Gannai ba sa riskar Sa[1], Shi ne Yake riskar gannai, kuma Shi Mai tausasawa ne, Mai cikakken sani


1- A duniya babu wanda zai ga Allah quru-quru da idonsa. Amma a lahira muminai za su gan shi kamar yadda ya zo a Suratul Qiyama aya ta 22 zuwa 23. Hadisai masu yawa sun tabbatar da hakan.


Surah: Suratul Anfal

Ayah : 61

۞وَإِن جَنَحُواْ لِلسَّلۡمِ فَٱجۡنَحۡ لَهَا وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Idan kuma suka karkato ga sulhu, to sai kai ma ka karkato gare shi, ka kuma dogara ga Allah. Lalle Shi Mai ji ne Masani



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 105

وَقُلِ ٱعۡمَلُواْ فَسَيَرَى ٱللَّهُ عَمَلَكُمۡ وَرَسُولُهُۥ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَۖ وَسَتُرَدُّونَ إِلَىٰ عَٰلِمِ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

Ka kuma ce: “Ku yi aiki, Allah ne zai ga aikinku shi da Manzonsa da kuma muminai, kuma za a mayar da ku zuwa ga Masanin abin da yake voye da na sarari, sannan Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa



Surah: Suratu Hud

Ayah : 112

فَٱسۡتَقِمۡ كَمَآ أُمِرۡتَ وَمَن تَابَ مَعَكَ وَلَا تَطۡغَوۡاْۚ إِنَّهُۥ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ

Don haka sai ka tsaya totar kamar yadda aka umarce ka kai da waxanda suka tuba tare da kai, kada kuwa ku wuce iyaka. Lalle Shi (Allah) Mai ganin abin da kuke aikatawa ne



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 96

قُلۡ كَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدَۢا بَيۡنِي وَبَيۡنَكُمۡۚ إِنَّهُۥ كَانَ بِعِبَادِهِۦ خَبِيرَۢا بَصِيرٗا

Ka ce: “Allah Ya isa shaida tsakanina da ku: Lalle Shi ya zamanto Masani ne ga bayinsa, kuma Mai ganin (abin da suke aikatawa) ne.”



Surah: Suratul Kahf 

Ayah : 26

قُلِ ٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا لَبِثُواْۖ لَهُۥ غَيۡبُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ أَبۡصِرۡ بِهِۦ وَأَسۡمِعۡۚ مَا لَهُم مِّن دُونِهِۦ مِن وَلِيّٖ وَلَا يُشۡرِكُ فِي حُكۡمِهِۦٓ أَحَدٗا

Ka ce: “Allah ne Mafi sanin tsawon zaman da suka yi.” Gaibun da yake sammai da qasa nasa ne. Wa ya yi gani irin nasa, wa kuma ya yi ji irin nasa (watau Allah). Ba su da wani majivinci in ban da Shi; ba Ya kuma tarayya da wani a cikin hukuncinsa



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 46

قَالَ لَا تَخَافَآۖ إِنَّنِي مَعَكُمَآ أَسۡمَعُ وَأَرَىٰ

Ya ce: “Kada ku ji tsoro; haqiqa Ni ina tare da ku, ina ji kuma ina ganin (komai)



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 75

ٱللَّهُ يَصۡطَفِي مِنَ ٱلۡمَلَـٰٓئِكَةِ رُسُلٗا وَمِنَ ٱلنَّاسِۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعُۢ بَصِيرٞ

Allah Yana zavar manzanni daga mala’iku kuma daga mutane. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani



Surah: Suratul Furqan

Ayah : 20

وَمَآ أَرۡسَلۡنَا قَبۡلَكَ مِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ إِلَّآ إِنَّهُمۡ لَيَأۡكُلُونَ ٱلطَّعَامَ وَيَمۡشُونَ فِي ٱلۡأَسۡوَاقِۗ وَجَعَلۡنَا بَعۡضَكُمۡ لِبَعۡضٖ فِتۡنَةً أَتَصۡبِرُونَۗ وَكَانَ رَبُّكَ بَصِيرٗا

Kuma ba Mu aiko manzanni ba gabaninka sai cewa lalle suna cin abinci kuma suna tafiya cikin kasuwanni. Mun kuwa sanya wasunku su zama fitina ga wasu. Shin za ku yi haquri? Ubangijinka kuwa Ya kasance Mai gani ne



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 217

وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱلۡعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ

Ka kuma dogara ga Mabuwayi, Mai rahama



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 218

ٱلَّذِي يَرَىٰكَ حِينَ تَقُومُ

Wanda Yake ganin ka yayin da kake tashi (don yin salla)



Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 219

وَتَقَلُّبَكَ فِي ٱلسَّـٰجِدِينَ

Da kuma (yayin) jujjuyawarka cikin masu sujjada[1]


1- Watau masallata a sallar jam’i.


Surah: Suratus Shu’ara

Ayah : 220

إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ

Haqiqa Shi Mai ji ne, Masani



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 31

وَٱلَّذِيٓ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ هُوَ ٱلۡحَقُّ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِۗ إِنَّ ٱللَّهَ بِعِبَادِهِۦ لَخَبِيرُۢ بَصِيرٞ

Kuma abin da Muka yiwo maka wahayinsa na Littafi shi ne gaskiya, yana gaskata abin da yake gabaninsa (na littattafai). Lalle Allah game da bayinsa Masani ne, Mai gani



Surah: Suratu Fussilat

Ayah : 40

إِنَّ ٱلَّذِينَ يُلۡحِدُونَ فِيٓ ءَايَٰتِنَا لَا يَخۡفَوۡنَ عَلَيۡنَآۗ أَفَمَن يُلۡقَىٰ فِي ٱلنَّارِ خَيۡرٌ أَم مَّن يَأۡتِيٓ ءَامِنٗا يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ ٱعۡمَلُواْ مَا شِئۡتُمۡ إِنَّهُۥ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٌ

Lalle waxanda suke fanxara game da ayoyinmu[1], ba za su voyu gare Mu ba. Yanzu wanda za a jefa shi a cikin wuta, shi ya fi ko kuma wanda zai zo yana amintacce a ranar alqiyama? Ku aikata abin da kuka ga dama, lalle Shi Mai ganin abin da kuke aikatawa ne


1- Watau suke fanxare wa ayoyinsa, suna qaryata su, suna musunta su da jirkita ma’anoninsa ko canza lafuzansu.


Surah: Suratus Shura

Ayah : 11

فَاطِرُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ جَعَلَ لَكُم مِّنۡ أَنفُسِكُمۡ أَزۡوَٰجٗا وَمِنَ ٱلۡأَنۡعَٰمِ أَزۡوَٰجٗا يَذۡرَؤُكُمۡ فِيهِۚ لَيۡسَ كَمِثۡلِهِۦ شَيۡءٞۖ وَهُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡبَصِيرُ

(Shi ne) Mahaliccin sammai da qasa. Ya halitta muku mataye daga jinsinku, daga dabbobi ma (Ya halicce su) maza da mata; Yana yaxa ku ta hanyarsa (haxin jinsin biyu). Babu wani abu da ya yi kama da Shi[1]; kuma Shi Mai ji ne, Mai gani


1- Watau ba ya da mai kama da shi a Zatinsa da siffofinsa da sunayensa da ayyukansa.


Surah: Suratuz Zukhruf 

Ayah : 80

أَمۡ يَحۡسَبُونَ أَنَّا لَا نَسۡمَعُ سِرَّهُمۡ وَنَجۡوَىٰهُمۚ بَلَىٰ وَرُسُلُنَا لَدَيۡهِمۡ يَكۡتُبُونَ

Ko suna tsammanin cewa Mu ba Ma jin asirinsu da ganawarsu ne? Ba haka ba ne, manzanninmu suna tare da su suna rubutawa



Surah: Suratul Hujurat

Ayah : 18

إِنَّ ٱللَّهَ يَعۡلَمُ غَيۡبَ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَٱللَّهُ بَصِيرُۢ بِمَا تَعۡمَلُونَ

Lalle Allah Yana sane da abin da yake voye a sammai da qasa, Allah kuma Mai ganin abin da kuke aikatawa ne



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 1

قَدۡ سَمِعَ ٱللَّهُ قَوۡلَ ٱلَّتِي تُجَٰدِلُكَ فِي زَوۡجِهَا وَتَشۡتَكِيٓ إِلَى ٱللَّهِ وَٱللَّهُ يَسۡمَعُ تَحَاوُرَكُمَآۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعُۢ بَصِيرٌ

Haqiqa Allah ya ji zancen wadda take muhawara da kai game da (lamarin) mijinta[1], tana kuma kai qara zuwa ga Allah, Allah kuma Yana jin muhawararku. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani


1- Ita ce Khaulatu ‘yar Sa’alaba (), mijinta kuwa shi ne Ausu xan Samit ().


Surah: Suratul Mulk

Ayah : 19

أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَى ٱلطَّيۡرِ فَوۡقَهُمۡ صَـٰٓفَّـٰتٖ وَيَقۡبِضۡنَۚ مَا يُمۡسِكُهُنَّ إِلَّا ٱلرَّحۡمَٰنُۚ إِنَّهُۥ بِكُلِّ شَيۡءِۭ بَصِيرٌ

Shin ba sa ganin tsuntsaye a samansu suna shimfixa (fikafikansu) suna kuma rufe su? Ba wanda yake riqe da su sai (Allah) Mai rahama. Lalle Shi Mai ganin komai ne