Surah: Suratul Baqara

Ayah : 229

ٱلطَّلَٰقُ مَرَّتَانِۖ فَإِمۡسَاكُۢ بِمَعۡرُوفٍ أَوۡ تَسۡرِيحُۢ بِإِحۡسَٰنٖۗ وَلَا يَحِلُّ لَكُمۡ أَن تَأۡخُذُواْ مِمَّآ ءَاتَيۡتُمُوهُنَّ شَيۡـًٔا إِلَّآ أَن يَخَافَآ أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ ٱللَّهِۖ فَإِنۡ خِفۡتُمۡ أَلَّا يُقِيمَا حُدُودَ ٱللَّهِ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡهِمَا فِيمَا ٱفۡتَدَتۡ بِهِۦۗ تِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِ فَلَا تَعۡتَدُوهَاۚ وَمَن يَتَعَدَّ حُدُودَ ٱللَّهِ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Saki sau biyu ne (xaya bayan xaya), don haka ko dai ya riqe ta ta hanyar da aka sani, ko kuma ya sake ta tare da kyautatawa. Kuma bai halatta gare ku ba ku karvi wani abu daga cikin abin da kuka ba su, sai fa idan su (ma’aurata) biyu sun ji tsoron ba za su tsayar da dokokin Allah ba. To idan kuka ji tsoron ba za su tsayar da dokokin Allah ba, to babu laifi a gare su game da abin da ta fanshi kanta da shi[1]. Waxannan iyakokin Allah ne, kada ku qetare su, kuma duk wanda ya qetare iyakokin Allah, to waxannan su ne azzalumai


1- Idan mace ta ga ba za ta iya zama da mijinta ba, to babu laifi ta mayar masa abin da ya kashe, sai su rabu. Wannan shi ne: Khul’u.