Surah: Suratul Baqara

Ayah : 121

ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَتۡلُونَهُۥ حَقَّ تِلَاوَتِهِۦٓ أُوْلَـٰٓئِكَ يُؤۡمِنُونَ بِهِۦۗ وَمَن يَكۡفُرۡ بِهِۦ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡخَٰسِرُونَ

Waxanda Muka saukar musu da littafi suna karanta shi yadda ya cancanta a karanta shi, waxannan su ne suke yin imani da shi. Kuma waxanda suka kafirce masa to waxannan su ne hasararru



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 113

۞لَيۡسُواْ سَوَآءٗۗ مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَٰبِ أُمَّةٞ قَآئِمَةٞ يَتۡلُونَ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ ءَانَآءَ ٱلَّيۡلِ وَهُمۡ يَسۡجُدُونَ

Ba dukansu ne suka zama xaya ba. Cikin Ma’abota Littafi akwai al’umma tsayayya, suna karanta Littafin Allah a cikin dare alhalin suna sujada



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 82

أَفَلَا يَتَدَبَّرُونَ ٱلۡقُرۡءَانَۚ وَلَوۡ كَانَ مِنۡ عِندِ غَيۡرِ ٱللَّهِ لَوَجَدُواْ فِيهِ ٱخۡتِلَٰفٗا كَثِيرٗا

Shin ba za su yi zuzzurfan tunani game da (ayoyin) Alqur’ani ba ne? Kuma da a ce ya kasance daga wajen wani yake ba Allah ba, tabbas da sun sami savani mai yawa a cikinsa



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 204

وَإِذَا قُرِئَ ٱلۡقُرۡءَانُ فَٱسۡتَمِعُواْ لَهُۥ وَأَنصِتُواْ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ

Kuma idan an karanta Alqur’ani, to ku saurare shi, ku kuma yi tsit, don a ji qan ku



Surah: Suratun Nahl

Ayah : 98

فَإِذَا قَرَأۡتَ ٱلۡقُرۡءَانَ فَٱسۡتَعِذۡ بِٱللَّهِ مِنَ ٱلشَّيۡطَٰنِ ٱلرَّجِيمِ

To idan za ka karanta Alqur’ani sai ka nemi tsarin Allah daga Shaixan korarre (daga rahamar Allah)



Surah: Suratul Kahf 

Ayah : 27

وَٱتۡلُ مَآ أُوحِيَ إِلَيۡكَ مِن كِتَابِ رَبِّكَۖ لَا مُبَدِّلَ لِكَلِمَٰتِهِۦ وَلَن تَجِدَ مِن دُونِهِۦ مُلۡتَحَدٗا

Kuma ka karanta abin da aka yiwo maka wahayi da shi daga littafin Ubangijinka: Ba mai canja kalmominsa; ba kuma za ka sami wata mafaka ba in ba ta wurinsa ba



Surah: Suratul Furqan

Ayah : 30

وَقَالَ ٱلرَّسُولُ يَٰرَبِّ إِنَّ قَوۡمِي ٱتَّخَذُواْ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ مَهۡجُورٗا

Manzo kuma ya ce: “Ya Ubangijina, lalle mutanena sun riqi wannan Alqur’ani abin qaurace wa[1].”


1- Watau ta hanyar guje wa sauraron sa da rashin karanta shi da aiki da koyarwarsa.


Surah: Suratun Namli

Ayah : 92

وَأَنۡ أَتۡلُوَاْ ٱلۡقُرۡءَانَۖ فَمَنِ ٱهۡتَدَىٰ فَإِنَّمَا يَهۡتَدِي لِنَفۡسِهِۦۖ وَمَن ضَلَّ فَقُلۡ إِنَّمَآ أَنَا۠ مِنَ ٱلۡمُنذِرِينَ

“An kuma (umarce ni) da in karanta Alqur’ani; don haka duk wanda ya shiriya, to ya shiriya ne don amfanin kansa; wanda kuwa ya vace sai ka ce (da shi): ‘Da ma ni ina cikin masu gargaxi ne kawai’”



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 45

ٱتۡلُ مَآ أُوحِيَ إِلَيۡكَ مِنَ ٱلۡكِتَٰبِ وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَۖ إِنَّ ٱلصَّلَوٰةَ تَنۡهَىٰ عَنِ ٱلۡفَحۡشَآءِ وَٱلۡمُنكَرِۗ وَلَذِكۡرُ ٱللَّهِ أَكۡبَرُۗ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ مَا تَصۡنَعُونَ

Ka karanta abin da ake yi maka wahayinsa na Alqur’ani, ka kuma tsai da salla; lalle salla tana hana alfasha da kuma abin qi. Kuma tabbas ambaton Allah shi ne mafi girma. Kuma Allah Yana sane da abin da kuke aikatawa



Surah: Suratul Ahzab

Ayah : 34

وَٱذۡكُرۡنَ مَا يُتۡلَىٰ فِي بُيُوتِكُنَّ مِنۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ وَٱلۡحِكۡمَةِۚ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ لَطِيفًا خَبِيرًا

Kuma ku tuna abin da ake karantawa a cikin gidajenku na ayoyin Allah da kuma hikima. Lalle Allah Ya kasance Mai tausayawa ne, Masani



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 29

إِنَّ ٱلَّذِينَ يَتۡلُونَ كِتَٰبَ ٱللَّهِ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنفَقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ سِرّٗا وَعَلَانِيَةٗ يَرۡجُونَ تِجَٰرَةٗ لَّن تَبُورَ

Lalle waxanda suke karanta Littafin Allah suka kuma tsai da salla suka kuma ciyar daga abin da Muka arzuta su a voye da sarari, suna burin kasuwancin da ba zai yi tazgaro ba



Surah: Suratu Sad

Ayah : 29

كِتَٰبٌ أَنزَلۡنَٰهُ إِلَيۡكَ مُبَٰرَكٞ لِّيَدَّبَّرُوٓاْ ءَايَٰتِهِۦ وَلِيَتَذَكَّرَ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Littafi ne mai albarka da Muka saukar maka da shi domin su yi tuntuntuni game da ayoyinsa, don kuma masu hankula su wa’azantu



Surah: Suratu Muhammad

Ayah : 24

أَفَلَا يَتَدَبَّرُونَ ٱلۡقُرۡءَانَ أَمۡ عَلَىٰ قُلُوبٍ أَقۡفَالُهَآ

Yanzu ba za su yi tunani na basira ba (game da) Alqur’ani ba, ko kuwa akwai wani rufi ne a kan zukatansu?



Surah: Suratul Muzzammil

Ayah : 4

أَوۡ زِدۡ عَلَيۡهِ وَرَتِّلِ ٱلۡقُرۡءَانَ تَرۡتِيلًا

Ko ka qara a kansa, ka kuma karanta Alqur’ani daki-daki



Surah: Suratul Muzzammil

Ayah : 20

۞إِنَّ رَبَّكَ يَعۡلَمُ أَنَّكَ تَقُومُ أَدۡنَىٰ مِن ثُلُثَيِ ٱلَّيۡلِ وَنِصۡفَهُۥ وَثُلُثَهُۥ وَطَآئِفَةٞ مِّنَ ٱلَّذِينَ مَعَكَۚ وَٱللَّهُ يُقَدِّرُ ٱلَّيۡلَ وَٱلنَّهَارَۚ عَلِمَ أَن لَّن تُحۡصُوهُ فَتَابَ عَلَيۡكُمۡۖ فَٱقۡرَءُواْ مَا تَيَسَّرَ مِنَ ٱلۡقُرۡءَانِۚ عَلِمَ أَن سَيَكُونُ مِنكُم مَّرۡضَىٰ وَءَاخَرُونَ يَضۡرِبُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ يَبۡتَغُونَ مِن فَضۡلِ ٱللَّهِ وَءَاخَرُونَ يُقَٰتِلُونَ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِۖ فَٱقۡرَءُواْ مَا تَيَسَّرَ مِنۡهُۚ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتُواْ ٱلزَّكَوٰةَ وَأَقۡرِضُواْ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗاۚ وَمَا تُقَدِّمُواْ لِأَنفُسِكُم مِّنۡ خَيۡرٖ تَجِدُوهُ عِندَ ٱللَّهِ هُوَ خَيۡرٗا وَأَعۡظَمَ أَجۡرٗاۚ وَٱسۡتَغۡفِرُواْ ٱللَّهَۖ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمُۢ

Lalle Ubangijinka Yana sane da cewa kai kana tsayawa qasa da kashi biyu cikin uku na dare, da kuma rabinsa, da kuma xaya bisa ukunsa, kai da wata jama’ar da take tare da kai. Allah ne kuma Yake qaddara dare da rana. Ya san kuma cewa, ba za ku iya qididdige (sa’o’insa) ba, don haka sai Ya yafe muku; to sai ku karanta abin da ya sauqaqa daga Alqur’ani. Ya san cewa daga cikinku akwai waxanda za su kasance marasa lafiya, waxansu kuma suna tafiya a bayan qasa don fatauci suna neman falala daga Allah, waxansu kuma suna yin yaqi saboda Allah; to sai ku karanta abin da ya sauqaqa daga gare shi (Alqur’ani). Ku kuma tsayar da salla, ku kuma ba da zakka, kuma ku bai wa Allah rance kyakkyawa[1]. Kuma abin da kuka gabatar wa kanku na wani alheri, to za ku same shi wurin Allah, shi ya fi alheri ya kuma fi girman lada. Ku kuma nemi gafarar Allah; lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai


1- Watau su ciyar da dukiyoyinsu don Allah wuraren da suka dace.


Surah: Suratul Alaq

Ayah : 1

ٱقۡرَأۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلَّذِي خَلَقَ

Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, Wanda Ya yi halitta



Surah: Suratul Alaq

Ayah : 3

ٱقۡرَأۡ وَرَبُّكَ ٱلۡأَكۡرَمُ

Ka yi karatu alhali Ubangijinka Shi ne mafi karamci