Surah: Suratul Baqara

Ayah : 176

ذَٰلِكَ بِأَنَّ ٱللَّهَ نَزَّلَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّۗ وَإِنَّ ٱلَّذِينَ ٱخۡتَلَفُواْ فِي ٱلۡكِتَٰبِ لَفِي شِقَاقِۭ بَعِيدٖ

Wannan ya faru ne saboda lalle Allah Ya saukar da Littafinsa da gaskiya. Kuma lalle duk waxanda suka yi savani dangane da Littafin, tabbas suna cikin savawa mai nisa



Surah: Suratul Baqara

Ayah : 252

تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱللَّهِ نَتۡلُوهَا عَلَيۡكَ بِٱلۡحَقِّۚ وَإِنَّكَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ

Waxannan ayoyin Allah ne, Muna karanta maka su da gaskiya, kuma lalle kai tabbas kana cikin manzanni



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 3

نَزَّلَ عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ مُصَدِّقٗا لِّمَا بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَأَنزَلَ ٱلتَّوۡرَىٰةَ وَٱلۡإِنجِيلَ

Ya saukar maka da Littafi da gaskiya, yana mai gaskata abin da ya gabace shi, kuma Ya saukar da Attaura da Linjila



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 7

هُوَ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ مِنۡهُ ءَايَٰتٞ مُّحۡكَمَٰتٌ هُنَّ أُمُّ ٱلۡكِتَٰبِ وَأُخَرُ مُتَشَٰبِهَٰتٞۖ فَأَمَّا ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِمۡ زَيۡغٞ فَيَتَّبِعُونَ مَا تَشَٰبَهَ مِنۡهُ ٱبۡتِغَآءَ ٱلۡفِتۡنَةِ وَٱبۡتِغَآءَ تَأۡوِيلِهِۦۖ وَمَا يَعۡلَمُ تَأۡوِيلَهُۥٓ إِلَّا ٱللَّهُۗ وَٱلرَّـٰسِخُونَ فِي ٱلۡعِلۡمِ يَقُولُونَ ءَامَنَّا بِهِۦ كُلّٞ مِّنۡ عِندِ رَبِّنَاۗ وَمَا يَذَّكَّرُ إِلَّآ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ

Shi ne Wanda ya saukar maka da Littafi, a cikinsa akwai ayoyi masu bayyanannun hukunce-hukunce, su ne asalin Littafin, akwai kuma waxansu masu rikitarwa[1]; to amma waxanda suke da karkata a zukatansu sai su riqa bin abin da yake rikitarwar a cikinsu don neman fitina da kuma neman sanin haqiqanin fassararsa. Kuma babu wanda ya san haqiqanin fassararsa sai Allah. Kuma masu zurfi cikin ilimi suna cewa: “Mun yi imani da shi, dukkaninsa daga wurin Ubangijinmu yake.” Kuma ba mai wa’azantuwa sai masu hankali


1- Ayoyi masu rikitarwa, su ne waxanda ma’anoninsu ba su fito fili ba.


Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 108

تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱللَّهِ نَتۡلُوهَا عَلَيۡكَ بِٱلۡحَقِّۗ وَمَا ٱللَّهُ يُرِيدُ ظُلۡمٗا لِّلۡعَٰلَمِينَ

Waxannan ayoyin Allah ne Muke karanta maka su da gaskiya. Kuma Allah ba Ya nufin zalunci ga talikai



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 105

إِنَّآ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ بِٱلۡحَقِّ لِتَحۡكُمَ بَيۡنَ ٱلنَّاسِ بِمَآ أَرَىٰكَ ٱللَّهُۚ وَلَا تَكُن لِّلۡخَآئِنِينَ خَصِيمٗا

Lalle Mu Mun saukar maka da Littafi da gaskiya domin ka yi hukunci a tsakanin mutane da abin da Allah Ya sanar da kai, kuma kada ka zamo mai ba da kariya ga maha’inta



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 113

وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكَ وَرَحۡمَتُهُۥ لَهَمَّت طَّآئِفَةٞ مِّنۡهُمۡ أَن يُضِلُّوكَ وَمَا يُضِلُّونَ إِلَّآ أَنفُسَهُمۡۖ وَمَا يَضُرُّونَكَ مِن شَيۡءٖۚ وَأَنزَلَ ٱللَّهُ عَلَيۡكَ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡحِكۡمَةَ وَعَلَّمَكَ مَا لَمۡ تَكُن تَعۡلَمُۚ وَكَانَ فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكَ عَظِيمٗا

Ba don falalar Allah da rahamarsa a kanka ba kuwa, lalle da waxansu jama’a daga cikinsu sun yi niyyar su vatar da kai, ba kuwa kowa za su iya vatarwa ba sai dai kawunansu; kuma ba za su cuce ka da komai ba. Kuma Allah Ya saukar maka da Littafi da hikima, kuma Ya sanar da kai abin da a da ba ka sani ba. Kuma falalar Allah mai girma ce gare ka



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 136

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ ءَامِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلَّذِي نَزَّلَ عَلَىٰ رَسُولِهِۦ وَٱلۡكِتَٰبِ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ مِن قَبۡلُۚ وَمَن يَكۡفُرۡ بِٱللَّهِ وَمَلَـٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ فَقَدۡ ضَلَّ ضَلَٰلَۢا بَعِيدًا

Ya ku waxanda suka yi imani, ku yi imani[1] da Allah da Manzonsa da Littafin da Ya saukar ga Manzonsa da Littafin da Ya saukar gabaninsa. Duk wanda kuwa ya kafirce wa Allah da mala’ikunsa da littattafansa da manzanninsa da ranar qarshe, to haqiqa ya vace vata mai nisa


1- Watau ku tsaya qyam a kan imaninsu da Allah da Annabinsa (), su riqe addininsu da kyau.


Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 166

لَّـٰكِنِ ٱللَّهُ يَشۡهَدُ بِمَآ أَنزَلَ إِلَيۡكَۖ أَنزَلَهُۥ بِعِلۡمِهِۦۖ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَشۡهَدُونَۚ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ شَهِيدًا

Amma Allah Yana shaida game da abin da Ya saukar maka; Ya saukar da shi ne da iliminsa; haka mala’iku ma suna shaidawa. Kuma Allah Ya isa Mai shaida



Surah: Suratul An’am

Ayah : 114

أَفَغَيۡرَ ٱللَّهِ أَبۡتَغِي حَكَمٗا وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ إِلَيۡكُمُ ٱلۡكِتَٰبَ مُفَصَّلٗاۚ وَٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَعۡلَمُونَ أَنَّهُۥ مُنَزَّلٞ مِّن رَّبِّكَ بِٱلۡحَقِّۖ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُمۡتَرِينَ

(Ka ce) “Shin wanin Allah zan nema a matsayin mai yi mana hukunci, alhalin Shi ne wanda Ya saukar muku da littafi mai bayani dalla-dalla?” Waxanda Muka ba su littafi kuwa suna sane da cewa, lalle shi saukakke ne daga Ubangijinka da gaskiya; don haka lalle kada ka kasance daga cikin masu kokwanto



Surah: Suratul An’am

Ayah : 155

وَهَٰذَا كِتَٰبٌ أَنزَلۡنَٰهُ مُبَارَكٞ فَٱتَّبِعُوهُ وَٱتَّقُواْ لَعَلَّكُمۡ تُرۡحَمُونَ

Kuma wannan Littafi (Alqur’ani) Mun saukar da shi, yana mai cike da albarka, don haka ku bi shi, kuma ku kiyaye dokokin (Allah), domin a ji qan ku



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 2

كِتَٰبٌ أُنزِلَ إِلَيۡكَ فَلَا يَكُن فِي صَدۡرِكَ حَرَجٞ مِّنۡهُ لِتُنذِرَ بِهِۦ وَذِكۡرَىٰ لِلۡمُؤۡمِنِينَ

(Wannan) Littafi ne da aka saukar maka, don haka kada wani qunci ya kasance a qirjinka a sanadiyyarsa, don ka yi gargaxi da shi, kuma da tunatarwa ga muminai



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 196

إِنَّ وَلِـِّۧيَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي نَزَّلَ ٱلۡكِتَٰبَۖ وَهُوَ يَتَوَلَّى ٱلصَّـٰلِحِينَ

“Lalle Majivincin lamarina Shi ne Allah Wanda Ya saukar da Littafi; kuma Shi Yake jivintar lamarin salihan bayi.”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 16

قُل لَّوۡ شَآءَ ٱللَّهُ مَا تَلَوۡتُهُۥ عَلَيۡكُمۡ وَلَآ أَدۡرَىٰكُم بِهِۦۖ فَقَدۡ لَبِثۡتُ فِيكُمۡ عُمُرٗا مِّن قَبۡلِهِۦٓۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ

Ka ce: “Da Allah Ya ga dama da ban karanta muku shi ba, kuma da (Allah) bai sanar da ku shi ba, domin haqiqa na zauna cikinku shekaru masu yawa[1] tun gabaninsa. Me ya sa ba za ku hankalta ba?”


1- Annabi () ya zauna a cikin mutanensa shekara arba’in kafin a fara yi masa wahayi.


Surah: Suratu Yunus

Ayah : 37

وَمَا كَانَ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانُ أَن يُفۡتَرَىٰ مِن دُونِ ٱللَّهِ وَلَٰكِن تَصۡدِيقَ ٱلَّذِي بَيۡنَ يَدَيۡهِ وَتَفۡصِيلَ ٱلۡكِتَٰبِ لَا رَيۡبَ فِيهِ مِن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Wannan Alqur’ani bai yiwuwa a qage shi daga (tunanin) wani wanda ba Allah ba, sai dai (shi) gaskatawa ne ga abin da ya gabace shi (na littattafan da aka saukar), kuma bayani ne dalla-dalla na hukunce-hukuncen (da Allah ya saukar); babu kokwanto a cikinsa cewa daga Ubangijin talikai yake



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 94

فَإِن كُنتَ فِي شَكّٖ مِّمَّآ أَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ فَسۡـَٔلِ ٱلَّذِينَ يَقۡرَءُونَ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلِكَۚ لَقَدۡ جَآءَكَ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُمۡتَرِينَ

To idan kana tababa[1] game da abin da Muka saukar maka to sai ka tambayi waxanda suke karanta littafi gabaninka. Haqiqa gaskiya ta zo maka daga Ubangijinka; to kada ka zama daga cikin masu kokwanto


1- Annabi () ba tava yin tababa ba game da wahayin da Allah () ya yi masa, amma abin nufi a nan shi ne kafa hujja ga Ahlulkitab a kan gaskiyar Annabi ().


Surah: Suratu Hud

Ayah : 1

الٓرۚ كِتَٰبٌ أُحۡكِمَتۡ ءَايَٰتُهُۥ ثُمَّ فُصِّلَتۡ مِن لَّدُنۡ حَكِيمٍ خَبِيرٍ

ALIF LAM RA[1]. (Wannan) Littafi ne da aka kyautata ayoyinsa sannan aka bayyana su filla-filla, daga wurin Mai hikima, Masani


1- Duba Suratul Baqara aya ta 1, hashiya ta 8.


Surah: Suratu Yusuf 

Ayah : 2

إِنَّآ أَنزَلۡنَٰهُ قُرۡءَٰنًا عَرَبِيّٗا لَّعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُونَ

Lalle Mu Muka saukar da shi Alqur’ani da (harshen) Larabci don ku hankalta



Surah: Suratu Yusuf 

Ayah : 3

نَحۡنُ نَقُصُّ عَلَيۡكَ أَحۡسَنَ ٱلۡقَصَصِ بِمَآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ هَٰذَا ٱلۡقُرۡءَانَ وَإِن كُنتَ مِن قَبۡلِهِۦ لَمِنَ ٱلۡغَٰفِلِينَ

Mu ne Muke labarta maka (labari) mafi kyan labartawa ta hanyar yi maka wahayin wannan Alqur’ani, ko da yake gabaninsa kana cikin marasa sanin(sa)



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 1

الٓمٓرۚ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِۗ وَٱلَّذِيٓ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ ٱلۡحَقُّ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَ ٱلنَّاسِ لَا يُؤۡمِنُونَ

ALIF LAM MIM RA[1]. Waxannan ayoyi ne na Littafi (wato Alqur’ani). Wanda kuma aka saukar maka daga Ubangijinka gaskiya ne, sai dai lalle yawancin mutane ba sa yin imani


1- Duba Suratul Baqara, aya ta 1, hashiya ta 8.


Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 1

الٓرۚ كِتَٰبٌ أَنزَلۡنَٰهُ إِلَيۡكَ لِتُخۡرِجَ ٱلنَّاسَ مِنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِ بِإِذۡنِ رَبِّهِمۡ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَمِيدِ

ALIF LAM RA[1]. Littafi ne da Muka saukar maka da shi, don ka fitar da mutane daga duffai zuwa ga haske, da izinin Ubangijinsu zuwa ga tafarkin (Allah) Mabuwayi, Abin godiya


1- Duba Suratul Baqara aya ta 1, hashiya ta 8.


Surah: Suratul Hijr

Ayah : 9

إِنَّا نَحۡنُ نَزَّلۡنَا ٱلذِّكۡرَ وَإِنَّا لَهُۥ لَحَٰفِظُونَ

Lalle Mu Muka saukar da Alqur’ani, lalle kuma tabbas Mu za Mu kiyaye shi



Surah: Suratul Hijr

Ayah : 87

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَٰكَ سَبۡعٗا مِّنَ ٱلۡمَثَانِي وَٱلۡقُرۡءَانَ ٱلۡعَظِيمَ

Haqiqa kuma Mun ba ka (ayoyi) bakwai waxanda ake ta nanatawa (wato Suratul Fatiha) da kuma Alqur’ani mai girma



Surah: Suratun Nahl

Ayah : 44

بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَٱلزُّبُرِۗ وَأَنزَلۡنَآ إِلَيۡكَ ٱلذِّكۡرَ لِتُبَيِّنَ لِلنَّاسِ مَا نُزِّلَ إِلَيۡهِمۡ وَلَعَلَّهُمۡ يَتَفَكَّرُونَ

(Mun aiko su) da hujjoji bayyanannu da littattafai. Mun kuma saukar maka da Alqur’ani don ka yi wa mutane bayanin abin da aka saukar musu ko sa yi tunani



Surah: Suratun Nahl

Ayah : 101

وَإِذَا بَدَّلۡنَآ ءَايَةٗ مَّكَانَ ءَايَةٖ وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا يُنَزِّلُ قَالُوٓاْ إِنَّمَآ أَنتَ مُفۡتَرِۭۚ بَلۡ أَكۡثَرُهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

Idan kuma Muka musanya wata aya a madadin wata ayar, alhali kuwa Allah ne Mafi sanin abin da Yake saukarwa, sai su ce: “Kai dai mai qirqirar qarya ne kawai!” A’a, ba haka ba ne, yawancinsu ba su san (komai) ba ne



Surah: Suratun Nahl

Ayah : 102

قُلۡ نَزَّلَهُۥ رُوحُ ٱلۡقُدُسِ مِن رَّبِّكَ بِٱلۡحَقِّ لِيُثَبِّتَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَهُدٗى وَبُشۡرَىٰ لِلۡمُسۡلِمِينَ

Ka ce: “Ruhul Qudusi (watau Mala’ika Jibrilu) ne ya saukar da shi daga Ubangijinka da gaskiya don ya tabbatar da waxanda suka yi imani (a kan dugadugansu), kuma shiriya ne da albishir ga Musulmai.”



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 105

وَبِٱلۡحَقِّ أَنزَلۡنَٰهُ وَبِٱلۡحَقِّ نَزَلَۗ وَمَآ أَرۡسَلۡنَٰكَ إِلَّا مُبَشِّرٗا وَنَذِيرٗا

Kuma da gaskiya Muka saukar da shi (Alqur’ani), kuma da gaskiya ya sauko. Ba Mu kuma aiko ka ba sai mai yin albishir, mai kuma gargaxi



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 106

وَقُرۡءَانٗا فَرَقۡنَٰهُ لِتَقۡرَأَهُۥ عَلَى ٱلنَّاسِ عَلَىٰ مُكۡثٖ وَنَزَّلۡنَٰهُ تَنزِيلٗا

Kuma Mun saukar da Qur’ani, Mun bayyana shi don ka karanta wa mutane shi a sannu a hankali, Mun kuma saukar da shi daki-daki



Surah: Suratul Kahf 

Ayah : 1

ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ عَلَىٰ عَبۡدِهِ ٱلۡكِتَٰبَ وَلَمۡ يَجۡعَل لَّهُۥ عِوَجَاۜ

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda Ya saukar wa da Bawansa Littafi, bai kuma sanya masa wata karkata ba



Surah: Suratul Kahf 

Ayah : 2

قَيِّمٗا لِّيُنذِرَ بَأۡسٗا شَدِيدٗا مِّن لَّدُنۡهُ وَيُبَشِّرَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٱلَّذِينَ يَعۡمَلُونَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ أَنَّ لَهُمۡ أَجۡرًا حَسَنٗا

Daidaitacce ne, don ya yi gargaxi game da azaba mai tsanani daga gare Shi (wato Allah), ya kuma yi wa muminai waxanda suke aiki nagari albishir cewa suna da lada kyakkyawa