۞سَيَقُولُ ٱلسُّفَهَآءُ مِنَ ٱلنَّاسِ مَا وَلَّىٰهُمۡ عَن قِبۡلَتِهِمُ ٱلَّتِي كَانُواْ عَلَيۡهَاۚ قُل لِّلَّهِ ٱلۡمَشۡرِقُ وَٱلۡمَغۡرِبُۚ يَهۡدِي مَن يَشَآءُ إِلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ
Ba da jimawa ba wawayen mutane za su ce: “Mene ne ya sa su juyawa su bar alqibilar da a da suke a kanta?”[1] Ka ce: “Gabas da yamma na Allah ne, Yana shiryar da wanda Ya ga dama zuwa ga tafarki madaidaici.”
1- Kafin saukar aya ta 144, Annabi () da sahabbansa a Makka suna fuskantar Baitul Maqdis yayin sallolinsu. Bayan sun yi hijira zuwa Madina sai Allah ya canza musu alqibla zuwa Ka’aba. Daga nan ne Yahudawa da Mushirikan Larabwa suka samu abin magana.
وَكَذَٰلِكَ جَعَلۡنَٰكُمۡ أُمَّةٗ وَسَطٗا لِّتَكُونُواْ شُهَدَآءَ عَلَى ٱلنَّاسِ وَيَكُونَ ٱلرَّسُولُ عَلَيۡكُمۡ شَهِيدٗاۗ وَمَا جَعَلۡنَا ٱلۡقِبۡلَةَ ٱلَّتِي كُنتَ عَلَيۡهَآ إِلَّا لِنَعۡلَمَ مَن يَتَّبِعُ ٱلرَّسُولَ مِمَّن يَنقَلِبُ عَلَىٰ عَقِبَيۡهِۚ وَإِن كَانَتۡ لَكَبِيرَةً إِلَّا عَلَى ٱلَّذِينَ هَدَى ٱللَّهُۗ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُضِيعَ إِيمَٰنَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِٱلنَّاسِ لَرَءُوفٞ رَّحِيمٞ
Kamar haka ne Muka sanya ku al’umma tsaka-tsaki (zavavvu) don ku zamo masu shaida ga mutane, kuma Manzo ya zamo mai shaida a gare ku. Kuma ba Mu sanya alqiblar da ka kasance a kanta ba sai don Mu bayyana wanda yake biyayya ga Manzo da wanda zai ja da baya (ya bijire). Kuma lalle wannan babban lamari ne sai dai ga waxanda Allah Ya shiryar. Kuma Allah ba zai tava tozarta imaninku ba. Lalle Allah Mai tausayi ne, Mai jin qai ga mutane
قَدۡ نَرَىٰ تَقَلُّبَ وَجۡهِكَ فِي ٱلسَّمَآءِۖ فَلَنُوَلِّيَنَّكَ قِبۡلَةٗ تَرۡضَىٰهَاۚ فَوَلِّ وَجۡهَكَ شَطۡرَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۚ وَحَيۡثُ مَا كُنتُمۡ فَوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ شَطۡرَهُۥۗ وَإِنَّ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ لَيَعۡلَمُونَ أَنَّهُ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّهِمۡۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا يَعۡمَلُونَ
Haqiqa Mun ga jujjuyawar fuskarka zuwa sama, to lalle za Mu fuskantar da kai zuwa ga alqibilar da za ka yarda da ita. Don haka ka juyar da fuskarka wajajen Masallaci mai alfarma; ku ma (Musulmi) a duk inda kuke to ku juyar da fuskokinku wajajensa. Lalle kuma waxanda aka ba su Littafi suna sane da cewa, lalle shi (wannan canji) gaskiya ne daga Ubangijinsu. Kuma Allah ba rafkananne ba ne game da abin da suke aikatawa
وَلَئِنۡ أَتَيۡتَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ بِكُلِّ ءَايَةٖ مَّا تَبِعُواْ قِبۡلَتَكَۚ وَمَآ أَنتَ بِتَابِعٖ قِبۡلَتَهُمۡۚ وَمَا بَعۡضُهُم بِتَابِعٖ قِبۡلَةَ بَعۡضٖۚ وَلَئِنِ ٱتَّبَعۡتَ أَهۡوَآءَهُم مِّنۢ بَعۡدِ مَا جَآءَكَ مِنَ ٱلۡعِلۡمِ إِنَّكَ إِذٗا لَّمِنَ ٱلظَّـٰلِمِينَ
Lalle kuma da za ka kawo wa waxanda aka ba su Littafi kowace irin hujja ba za su bi alqibilarka ba; kuma kai ma ba mai bin alqibilarsu ba ne; kuma sashinsu bai zama mai bin alqibilar sashi ba. Kuma haqiqa idan har ka bi soye-soyen zukatansu bayan abin da ya zo maka na gaskiya, to lalle idan ka yi haka tabbas kana cikin azzalumai
ٱلَّذِينَ ءَاتَيۡنَٰهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ يَعۡرِفُونَهُۥ كَمَا يَعۡرِفُونَ أَبۡنَآءَهُمۡۖ وَإِنَّ فَرِيقٗا مِّنۡهُمۡ لَيَكۡتُمُونَ ٱلۡحَقَّ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ
Waxanda Muka ba su Littafi suna sane da shi (Manzon Allah) kamar yadda suke sane da ‘ya’yansu; kuma lalle wani vangare daga cikinsu tabbas suna voye gaskiya alhalin suna sane
ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَ فَلَا تَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُمۡتَرِينَ
Gaskiya kam daga Ubangijinka take, don haka lalle kada ka zama daga cikin masu shakka
وَلِكُلّٖ وِجۡهَةٌ هُوَ مُوَلِّيهَاۖ فَٱسۡتَبِقُواْ ٱلۡخَيۡرَٰتِۚ أَيۡنَ مَا تَكُونُواْ يَأۡتِ بِكُمُ ٱللَّهُ جَمِيعًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ
Kuma kowane vangare yana da inda ya sa gaba, don haka sai ku yi gaggawar cim ma alheri. A duk inda kuke Allah zai zo da ku gaba xaya. Lalle Allah Mai iko ne a kan komai
وَمِنۡ حَيۡثُ خَرَجۡتَ فَوَلِّ وَجۡهَكَ شَطۡرَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۖ وَإِنَّهُۥ لَلۡحَقُّ مِن رَّبِّكَۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ
Ko ta ina ka fito, to ka juyar da fuskarka wajajen Masallaci mai alfarma; kuma lalle shi gaskiya ne daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama gafalalle game da abin da kuke aikatawa ba
وَمِنۡ حَيۡثُ خَرَجۡتَ فَوَلِّ وَجۡهَكَ شَطۡرَ ٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِۚ وَحَيۡثُ مَا كُنتُمۡ فَوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ شَطۡرَهُۥ لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَيۡكُمۡ حُجَّةٌ إِلَّا ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ مِنۡهُمۡ فَلَا تَخۡشَوۡهُمۡ وَٱخۡشَوۡنِي وَلِأُتِمَّ نِعۡمَتِي عَلَيۡكُمۡ وَلَعَلَّكُمۡ تَهۡتَدُونَ
Kuma duk inda ka fita, to ka juyar da fuskarka wajajen Masallaci mai alfarma. Ku ma duk inda kuke to ku juyar da fuskokinku wajajensa, don kada ya zama mutane suna da wata hujja a kanku, sai dai waxanda suka yi zalunci daga cikinsu, don haka kada ku ji tsoron su, ku ji tsorona, kuma domin in cika muku ni’imata, don ku shiriya
قُلۡ أَمَرَ رَبِّي بِٱلۡقِسۡطِۖ وَأَقِيمُواْ وُجُوهَكُمۡ عِندَ كُلِّ مَسۡجِدٖ وَٱدۡعُوهُ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَۚ كَمَا بَدَأَكُمۡ تَعُودُونَ
Ka ce: “Ubangijina Ya yi umarni da adalci; kuma ku tsai da fuskokinku (don Allah) a kowace salla, ku kuma roqe Shi kuna masu tsantsanta addini gare Shi. Kamar yadda Ya fari halittarku, haka za ku koma (wurinsa)
وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰ وَأَخِيهِ أَن تَبَوَّءَا لِقَوۡمِكُمَا بِمِصۡرَ بُيُوتٗا وَٱجۡعَلُواْ بُيُوتَكُمۡ قِبۡلَةٗ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Kuma Muka yi wa Musa wahayi shi da xan’uwansa cewa: “Ku tanadar wa mutanenku gidaje a Masar, ku kuma sanya gidajenku wurin salla.” Ka kuma yi wa muminai albishir (da samun nasara)