Surah: Suratul Baqara

Ayah : 255

ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡحَيُّ ٱلۡقَيُّومُۚ لَا تَأۡخُذُهُۥ سِنَةٞ وَلَا نَوۡمٞۚ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ مَن ذَا ٱلَّذِي يَشۡفَعُ عِندَهُۥٓ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦۚ يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيۡءٖ مِّنۡ عِلۡمِهِۦٓ إِلَّا بِمَا شَآءَۚ وَسِعَ كُرۡسِيُّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۖ وَلَا يَـُٔودُهُۥ حِفۡظُهُمَاۚ وَهُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡعَظِيمُ

Allah, babu wani abin bauta wa da cancanta sai Shi, Rayayye, Tsayayye da Zatinsa; gyangyaxi ba ya kama shi, ballantana barci. Abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin qasa nasa ne shi kaxai. Wane ne ya isa ya yi ceto a wurinsa in ba da izininsa ba? Ya san abin da yake tare da su a yanzu da kuma abin da zai biyo bayansu; kuma ba sa iya sanin wani abu cikin iliminsa sai abin da Ya ga dama. Kursiyyunsa ya yalwaci sammai da qasa, kuma kiyaye su ba zai nauyaye Shi ba, kuma Shi ne Maxaukaki Mai girma



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 2

ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡحَيُّ ٱلۡقَيُّومُ

Allah, babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, Shi Rayayye ne, Tsayayye da Zatinsa



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 180

وَلَا يَحۡسَبَنَّ ٱلَّذِينَ يَبۡخَلُونَ بِمَآ ءَاتَىٰهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦ هُوَ خَيۡرٗا لَّهُمۖ بَلۡ هُوَ شَرّٞ لَّهُمۡۖ سَيُطَوَّقُونَ مَا بَخِلُواْ بِهِۦ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۗ وَلِلَّهِ مِيرَٰثُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۗ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

Kuma waxanda suke yin rowar abin da Allah Ya ba su na falalarsa kar su yi tsammanin hakan alheri ne a gare su; a’a, hakan sharri ne a gare su; da sannu za a yi musu saqandami da abin da suka yi rowa da shi a ranar alqiyama. Kuma Allah Shi ne Mai gadon sammai da qasa. Kuma Allah Mai cikakken sanin abin da kuke aikatawa ne



Surah: Suratul Hijr

Ayah : 23

وَإِنَّا لَنَحۡنُ نُحۡيِۦ وَنُمِيتُ وَنَحۡنُ ٱلۡوَٰرِثُونَ

Lalle kuma tabbas Mu Muke rayawa kuma Muke kashewa, Mu ne kuma Masu gaje (komai)



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 40

إِنَّا نَحۡنُ نَرِثُ ٱلۡأَرۡضَ وَمَنۡ عَلَيۡهَا وَإِلَيۡنَا يُرۡجَعُونَ

Lalle Mu ne za Mu gaje qasa da wanda yake bayanta kuma gare Mu ne za a komar da su



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 80

وَنَرِثُهُۥ مَا يَقُولُ وَيَأۡتِينَا فَرۡدٗا

Kuma Mu gaje abin da yake faxa xin (na dukiyarsa da ‘ya’yansa), ya kuma zo mana shi kaxai[1]


1- Watau Allah zai xauke shi kacokam lokacin mutuwarsa, ya raba shi da dukiyarsa da ‘ya’yansa da yake taqama da su.


Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 111

۞وَعَنَتِ ٱلۡوُجُوهُ لِلۡحَيِّ ٱلۡقَيُّومِۖ وَقَدۡ خَابَ مَنۡ حَمَلَ ظُلۡمٗا

Kuma dukkanin fuskoki suka qasqanta ga (Allah) Rayayye, Tsayayye (da Zatinsa). Haqiqa kuma duk wanda ya yo dakon zalunci ya tave



Surah: Suratul Furqan

Ayah : 58

وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱلۡحَيِّ ٱلَّذِي لَا يَمُوتُ وَسَبِّحۡ بِحَمۡدِهِۦۚ وَكَفَىٰ بِهِۦ بِذُنُوبِ عِبَادِهِۦ خَبِيرًا

Kuma ka dogara ga (Allah) Rayayye Wanda ba zai mutu ba, kuma ka yi tasbihi da godiyar sa, kuma Ya isa Masani ga zunuban bayinsa



Surah: Suratul Qasas

Ayah : 58

وَكَمۡ أَهۡلَكۡنَا مِن قَرۡيَةِۭ بَطِرَتۡ مَعِيشَتَهَاۖ فَتِلۡكَ مَسَٰكِنُهُمۡ لَمۡ تُسۡكَن مِّنۢ بَعۡدِهِمۡ إِلَّا قَلِيلٗاۖ وَكُنَّا نَحۡنُ ٱلۡوَٰرِثِينَ

Kuma al’umma nawa ce Muka hallakar wadda ta butulce wa rayuwarta? To ga gidajensu can ba a zaune su ba a bayansu sai kaxan[1]; Mu ne Muka kasance magadan


1- Watau daga matafiya da sukan ya da zango su zauna na xan lokaci.


Surah: Suratul Qasas

Ayah : 88

وَلَا تَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَۘ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۚ كُلُّ شَيۡءٍ هَالِكٌ إِلَّا وَجۡهَهُۥۚ لَهُ ٱلۡحُكۡمُ وَإِلَيۡهِ تُرۡجَعُونَ

Kuma kada ka bauta wa wani abin bauta daban tare da Allah. Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Kowane abu mai halaka ne sai Fuskarsa kawai. Hukunci (duk) nasa ne, zuwa gare Shi kuma za a mayar da ku



Surah: Suratu Ghafir

Ayah : 65

هُوَ ٱلۡحَيُّ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ فَٱدۡعُوهُ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَۗ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Shi Rayayye ne, babu wani abin bauta da gaskiya sai Shi, sai ku roqe Shi kuna masu tsantsanta addini a gare Shi. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai



Surah: Suratur Rahman

Ayah : 27

وَيَبۡقَىٰ وَجۡهُ رَبِّكَ ذُو ٱلۡجَلَٰلِ وَٱلۡإِكۡرَامِ

Fuskar Ubangijinka kuwa Ma’abocin girma da karamci ne kawai take wanzuwa



Surah: Suratul Hadid

Ayah : 10

وَمَا لَكُمۡ أَلَّا تُنفِقُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلِلَّهِ مِيرَٰثُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ لَا يَسۡتَوِي مِنكُم مَّنۡ أَنفَقَ مِن قَبۡلِ ٱلۡفَتۡحِ وَقَٰتَلَۚ أُوْلَـٰٓئِكَ أَعۡظَمُ دَرَجَةٗ مِّنَ ٱلَّذِينَ أَنفَقُواْ مِنۢ بَعۡدُ وَقَٰتَلُواْۚ وَكُلّٗا وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ وَٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٞ

Kuma me ya same ku ne da ba za ku ciyar saboda Allah ba, alhali kuwa gadon sammai da qasa na Allah ne? Wanda ya ciyar daga cikinku tun kafin buxe (Makka)[1] ya kuma yi yaqi, ba zai zama daidai (da wanda bai yi) ba. Waxannan su suka fi girman daraja a kan waxanda suka ciyar daga bisani, suka kuma yi yaqi. Amma kuma kowannensu Allah Ya yi masa alqawarin Aljanna. Allah kuma Masanin abin da kuke aikatawa ne


1- Wasu daga cikin malamai sun fassara Fat’hu a wannan ayar da cewa ana nufin Sulhul Hudaibiyya.