Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 102

قَالَ لَقَدۡ عَلِمۡتَ مَآ أَنزَلَ هَـٰٓؤُلَآءِ إِلَّا رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ بَصَآئِرَ وَإِنِّي لَأَظُنُّكَ يَٰفِرۡعَوۡنُ مَثۡبُورٗا

(Musa) ya ce: “Haqiqa ka sani ba wanda ya saukar da waxannan (ayoyin) sai Ubangijin sammai da qasa don su zama hujjoji, kuma lalle ina tsammanin kai Fir’auna halakakke ne.”



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 103

فَأَرَادَ أَن يَسۡتَفِزَّهُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ فَأَغۡرَقۡنَٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ جَمِيعٗا

Sai ya yi nufin ya girgiza su a qasar (ta Masar don ya fitar da su daga ciki), to sai Muka nutsar da shi da duk wanda yake tare da shi gaba xaya



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 43

ٱذۡهَبَآ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ

“Ku tafi wurin Fir’auna, don ko lalle ya wuce iyaka



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 44

فَقُولَا لَهُۥ قَوۡلٗا لَّيِّنٗا لَّعَلَّهُۥ يَتَذَكَّرُ أَوۡ يَخۡشَىٰ

“Sai ku gaya masa magana mai taushi, ko wataqila zai wa’azantu ko kuma ya ji tsoron (azabar Allah).”



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 45

قَالَا رَبَّنَآ إِنَّنَا نَخَافُ أَن يَفۡرُطَ عَلَيۡنَآ أَوۡ أَن يَطۡغَىٰ

(Musa da Haruna) suka ce: “Ya Ubangijinmu, lalle mu muna tsoron ya far mana ko kuma ya wuce iyaka (wajen yi mana uquba).”



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 46

قَالَ لَا تَخَافَآۖ إِنَّنِي مَعَكُمَآ أَسۡمَعُ وَأَرَىٰ

Ya ce: “Kada ku ji tsoro; haqiqa Ni ina tare da ku, ina ji kuma ina ganin (komai)



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 47

فَأۡتِيَاهُ فَقُولَآ إِنَّا رَسُولَا رَبِّكَ فَأَرۡسِلۡ مَعَنَا بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ وَلَا تُعَذِّبۡهُمۡۖ قَدۡ جِئۡنَٰكَ بِـَٔايَةٖ مِّن رَّبِّكَۖ وَٱلسَّلَٰمُ عَلَىٰ مَنِ ٱتَّبَعَ ٱلۡهُدَىٰٓ

“Sai ku tafi wajensa sannan ku ce (da shi): “Lalle mu manzannin Ubangijinka ne, sai ka sakar mana Banu-Isra’ila, kada kuma ka azabtar da su; haqiqa mun zo maka da aya daga Ubangijinka; aminci kuwa ya tabbata ga wanda ya bi shiriya



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 48

إِنَّا قَدۡ أُوحِيَ إِلَيۡنَآ أَنَّ ٱلۡعَذَابَ عَلَىٰ مَن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ

“Lalle mu an yi mana wahayi cewa, ita azaba lalle tana nan ga wanda ya qaryata ya kuma ba da baya.”



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 49

قَالَ فَمَن رَّبُّكُمَا يَٰمُوسَىٰ

(Fir’auna) ya ce: “Wane ne Ubangijin naku ya Musa?”



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 50

قَالَ رَبُّنَا ٱلَّذِيٓ أَعۡطَىٰ كُلَّ شَيۡءٍ خَلۡقَهُۥ ثُمَّ هَدَىٰ

(Musa) ya ce: “Ubangijinmu (Shi ne) Wanda Ya bai wa kowane abu surar halittarsa sannan Ya shiryar (da shi yadda zai yi tasarrufi).”



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 51

قَالَ فَمَا بَالُ ٱلۡقُرُونِ ٱلۡأُولَىٰ

(Fir’auna) ya ce: “To mene ne halin da al’ummun farko suke ciki?”



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 52

قَالَ عِلۡمُهَا عِندَ رَبِّي فِي كِتَٰبٖۖ لَّا يَضِلُّ رَبِّي وَلَا يَنسَى

(Musa) ya ce: “Saninsu yana wurin Ubangijina a cikin Lauhul-Mahafuzu; Ubangijina kuma ba Ya kuskure (cikin iliminsa) kuma ba Ya mantuwa



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 53

ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ مَهۡدٗا وَسَلَكَ لَكُمۡ فِيهَا سُبُلٗا وَأَنزَلَ مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءٗ فَأَخۡرَجۡنَا بِهِۦٓ أَزۡوَٰجٗا مِّن نَّبَاتٖ شَتَّىٰ

“(Shi ne) Wanda Ya sanya muku qasa a shimfixe, Ya kuma sanya muku hanyoyi na tafiya cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama”, sannan Muka fitar da dangogin shuke-shuke iri-iri da shi (ruwa)



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 54

كُلُواْ وَٱرۡعَوۡاْ أَنۡعَٰمَكُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٖ لِّأُوْلِي ٱلنُّهَىٰ

Ku ci (daga tsirran) kuma ku yi kiwon dabbobinku. Lalle a game da wannan akwai ayoyi ga ma’abota hankula



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 55

۞مِنۡهَا خَلَقۡنَٰكُمۡ وَفِيهَا نُعِيدُكُمۡ وَمِنۡهَا نُخۡرِجُكُمۡ تَارَةً أُخۡرَىٰ

Daga ita (qasar) Muka halicce ku, kuma a cikinta za Mu mayar da ku, daga ita kuma za Mu fito da ku a wani karon



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 56

وَلَقَدۡ أَرَيۡنَٰهُ ءَايَٰتِنَا كُلَّهَا فَكَذَّبَ وَأَبَىٰ

Kuma haqiqa Mun nuna masa (Fir’auna) ayoyinmu dukkansu, sai ya qaryata kuma ya qi (ba da gaskiya)



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 57

قَالَ أَجِئۡتَنَا لِتُخۡرِجَنَا مِنۡ أَرۡضِنَا بِسِحۡرِكَ يَٰمُوسَىٰ

(Fir’auna) ya ce: “Yanzu ka zo mana ne don ka fitar da mu daga qasarmu da sihirinka, ya Musa?



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 58

فَلَنَأۡتِيَنَّكَ بِسِحۡرٖ مِّثۡلِهِۦ فَٱجۡعَلۡ بَيۡنَنَا وَبَيۡنَكَ مَوۡعِدٗا لَّا نُخۡلِفُهُۥ نَحۡنُ وَلَآ أَنتَ مَكَانٗا سُوٗى

“To lalle kuwa za mu zo maka da wani sihirin irinsa; sai ka sanya lokaci na musamman tsakaninmu da kai wanda mu ba za mu sava masa ba, kai ma haka, (ya zama) wuri ne tsaka-tsaki”



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 59

قَالَ مَوۡعِدُكُمۡ يَوۡمُ ٱلزِّينَةِ وَأَن يُحۡشَرَ ٱلنَّاسُ ضُحٗى

(Musa) ya ce: “Lokacin (da na sanya) muku shi ne ranar idi, kuma a tattara mutane da hantsi.”



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 60

فَتَوَلَّىٰ فِرۡعَوۡنُ فَجَمَعَ كَيۡدَهُۥ ثُمَّ أَتَىٰ

Sai Fir’auna ya juya, sai ya haxa makircinsa, sannan ya zo (wurin da aka shirya)



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 61

قَالَ لَهُم مُّوسَىٰ وَيۡلَكُمۡ لَا تَفۡتَرُواْ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبٗا فَيُسۡحِتَكُم بِعَذَابٖۖ وَقَدۡ خَابَ مَنِ ٱفۡتَرَىٰ

Musa ya ce da su: “Kaiconku! Kada fa ku qirqira wa Allah qarya, sai Ya hallaka ku da azaba; haqiqa kuwa wanda ya qirqira (masa qarya) to ya tave.”



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 62

فَتَنَٰزَعُوٓاْ أَمۡرَهُم بَيۡنَهُمۡ وَأَسَرُّواْ ٱلنَّجۡوَىٰ

Sai suka tattauna al’amarinsu a tsakaninsu, suka kuma gana a asirce



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 63

قَالُوٓاْ إِنۡ هَٰذَٰنِ لَسَٰحِرَٰنِ يُرِيدَانِ أَن يُخۡرِجَاكُم مِّنۡ أَرۡضِكُم بِسِحۡرِهِمَا وَيَذۡهَبَا بِطَرِيقَتِكُمُ ٱلۡمُثۡلَىٰ

Suka ce: “Lalle waxannan biyun (Musa da Haruna) tabbas matsafa ne, suna so ne su fitar da ku daga qasarku da tsafinsu, su kuma tafiyar da kyakkyawar hanyarku (ta rayuwa)



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 64

فَأَجۡمِعُواْ كَيۡدَكُمۡ ثُمَّ ٱئۡتُواْ صَفّٗاۚ وَقَدۡ أَفۡلَحَ ٱلۡيَوۡمَ مَنِ ٱسۡتَعۡلَىٰ

“Sai ku yiwo shiri haxaxxe sannan ku zo sahu-sahu. Haqiqa yau kam wanda ya yi nasara ya rabauta!”



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 65

قَالُواْ يَٰمُوسَىٰٓ إِمَّآ أَن تُلۡقِيَ وَإِمَّآ أَن نَّكُونَ أَوَّلَ مَنۡ أَلۡقَىٰ

Suka ce: “Ya Musa, ko dai ka jefa (naka) ko kuma mu mu fara jefa (namu).”



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 66

قَالَ بَلۡ أَلۡقُواْۖ فَإِذَا حِبَالُهُمۡ وَعِصِيُّهُمۡ يُخَيَّلُ إِلَيۡهِ مِن سِحۡرِهِمۡ أَنَّهَا تَسۡعَىٰ

Ya ce: “A’a, ku (fara) jefawa.” To saboda sihirinsu sai ga igiyoyinsu da sandunansu ana suranta masa cewa su (macizai ne) suna sauri



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 67

فَأَوۡجَسَ فِي نَفۡسِهِۦ خِيفَةٗ مُّوسَىٰ

Sai Musa ya voye (wani abu) na tsoro a ransa



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 68

قُلۡنَا لَا تَخَفۡ إِنَّكَ أَنتَ ٱلۡأَعۡلَىٰ

Muka ce: “Kada ka ji tsoro, lalle kai kake da rinjaye



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 69

وَأَلۡقِ مَا فِي يَمِينِكَ تَلۡقَفۡ مَا صَنَعُوٓاْۖ إِنَّمَا صَنَعُواْ كَيۡدُ سَٰحِرٖۖ وَلَا يُفۡلِحُ ٱلسَّاحِرُ حَيۡثُ أَتَىٰ

“Kuma ka jefar da abin da yake hannunka na dama, za ta haxiye abin da suka aikata; lalle abin da suka aikata makircin matsafi ne; matsafi kuwa ba ya rabauta duk ta inda ya zo.”



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 70

فَأُلۡقِيَ ٱلسَّحَرَةُ سُجَّدٗا قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِرَبِّ هَٰرُونَ وَمُوسَىٰ

Sai matsafan suka faxi suna sujjada[1] suka ce: “Mun yi imani da Ubangijin Haruna da Musa!”


1- Watau bayan sun fahimci cewa abin da Musa () ya zo da shi ba tsafi ba ne, wani abu ne daga Allah.