Surah: Suratul A’araf

Ayah : 131

فَإِذَا جَآءَتۡهُمُ ٱلۡحَسَنَةُ قَالُواْ لَنَا هَٰذِهِۦۖ وَإِن تُصِبۡهُمۡ سَيِّئَةٞ يَطَّيَّرُواْ بِمُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُۥٓۗ أَلَآ إِنَّمَا طَـٰٓئِرُهُمۡ عِندَ ٱللَّهِ وَلَٰكِنَّ أَكۡثَرَهُمۡ لَا يَعۡلَمُونَ

Amma yayin da daddaxan abu ya zo musu, sai su ce: “Da ma wannan namu ne.” Idan kuma mummunan abu ya same su, sai su camfa Musa da waxanda suke tare da shi. Ku saurara, kawai dai mummunan abin da ya same su daga wajen Allah yake, amma yawancinsu ba sa sanin (haka)



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 132

وَقَالُواْ مَهۡمَا تَأۡتِنَا بِهِۦ مِنۡ ءَايَةٖ لِّتَسۡحَرَنَا بِهَا فَمَا نَحۡنُ لَكَ بِمُؤۡمِنِينَ

Kuma suka ce: “Kowace irin aya ka zo mana da ita, don ka sihirce mu da ita, to fa mu ba za mu yi imani da kai ba.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 133

فَأَرۡسَلۡنَا عَلَيۡهِمُ ٱلطُّوفَانَ وَٱلۡجَرَادَ وَٱلۡقُمَّلَ وَٱلضَّفَادِعَ وَٱلدَّمَ ءَايَٰتٖ مُّفَصَّلَٰتٖ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمٗا مُّجۡرِمِينَ

Sai Muka aika musu da ambaliyar ruwa da fara da qwarqwata da kwaxi da jini, a matsayin ayoyi daki-daki, sai suka yi girman kai, kuma suka kasance mutane masu babban laifi



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 134

وَلَمَّا وَقَعَ عَلَيۡهِمُ ٱلرِّجۡزُ قَالُواْ يَٰمُوسَى ٱدۡعُ لَنَا رَبَّكَ بِمَا عَهِدَ عِندَكَۖ لَئِن كَشَفۡتَ عَنَّا ٱلرِّجۡزَ لَنُؤۡمِنَنَّ لَكَ وَلَنُرۡسِلَنَّ مَعَكَ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ

Kuma yayin da azaba ta sauka a kansu, sai suka ce: “Ya kai Musa, ka roqa mana Ubangijinka, saboda alqawarin da Ya yi maka; lalle idan har ka yaye mana wannan azaba, to tabbas za mu yi imani da kai, kuma za mu sakar maka Banu Isra’ila.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 135

فَلَمَّا كَشَفۡنَا عَنۡهُمُ ٱلرِّجۡزَ إِلَىٰٓ أَجَلٍ هُم بَٰلِغُوهُ إِذَا هُمۡ يَنكُثُونَ

To yayin da Muka yaye musu wannan azaba zuwa wani lokacin da za su kai gare shi, sai ga shi suna warware alqawarin da suka yi



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 136

فَٱنتَقَمۡنَا مِنۡهُمۡ فَأَغۡرَقۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡيَمِّ بِأَنَّهُمۡ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا وَكَانُواْ عَنۡهَا غَٰفِلِينَ

Sai Muka azabtar da su, Muka dulmiyar da su a cikin kogi saboda sun qaryata ayoyinmu, kuma sun kasance gafalallu game da su



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 137

وَأَوۡرَثۡنَا ٱلۡقَوۡمَ ٱلَّذِينَ كَانُواْ يُسۡتَضۡعَفُونَ مَشَٰرِقَ ٱلۡأَرۡضِ وَمَغَٰرِبَهَا ٱلَّتِي بَٰرَكۡنَا فِيهَاۖ وَتَمَّتۡ كَلِمَتُ رَبِّكَ ٱلۡحُسۡنَىٰ عَلَىٰ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ بِمَا صَبَرُواْۖ وَدَمَّرۡنَا مَا كَانَ يَصۡنَعُ فِرۡعَوۡنُ وَقَوۡمُهُۥ وَمَا كَانُواْ يَعۡرِشُونَ

Mutanen kuma da ake nuna musu fin qarfi a da, Muka gadar musu gabashi da yammacin qasar da Muka yi wa albarka; kuma kalmar Ubangijinka kyakkyawa sai ta tabbata a kan Banu Isra’ila saboda haqurin da suka yi; kuma Muka rushe abin da Fir’auna ya kasance yana yi shi da mutanensa, da abin da suka kasance suna ginawa



Surah: Suratul Anfal

Ayah : 54

كَدَأۡبِ ءَالِ فِرۡعَوۡنَ وَٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡۚ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ فَأَهۡلَكۡنَٰهُم بِذُنُوبِهِمۡ وَأَغۡرَقۡنَآ ءَالَ فِرۡعَوۡنَۚ وَكُلّٞ كَانُواْ ظَٰلِمِينَ

Kamar al’adar mutanen Fir’auna ce da kuma waxanda suke gabaninsu. Sun qaryata ayoyin Ubangijinsu, sai Muka hallaka su saboda zunubansu, Muka kuma nutsar da mutanen Fir’auna (a cikin kogi). Dukkaninsu kuwa sun kasance azzalumai



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 75

ثُمَّ بَعَثۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِم مُّوسَىٰ وَهَٰرُونَ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ بِـَٔايَٰتِنَا فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمٗا مُّجۡرِمِينَ

Sannan daga bayansu Muka aiko Musa da Haruna zuwa ga Fir’auna shi da jama’arsa da ayoyinmu, sai suka yi girman kai suka kuwa zamanto mutane masu laifi



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 76

فَلَمَّا جَآءَهُمُ ٱلۡحَقُّ مِنۡ عِندِنَا قَالُوٓاْ إِنَّ هَٰذَا لَسِحۡرٞ مُّبِينٞ

To lokacin da gaskiya ta zo musu daga wurinmu sai suka ce: “Lalle wannan tabbas tsafi ne bayyananne.”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 77

قَالَ مُوسَىٰٓ أَتَقُولُونَ لِلۡحَقِّ لَمَّا جَآءَكُمۡۖ أَسِحۡرٌ هَٰذَا وَلَا يُفۡلِحُ ٱلسَّـٰحِرُونَ

Musa ya ce: “Yanzu kwa riqa ce wa gaskiya (tsafi) lokacin da ta zo muku? Yanzu wannan ne tsafin, alhali kuwa matsafa ba sa cin nasara?”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 78

قَالُوٓاْ أَجِئۡتَنَا لِتَلۡفِتَنَا عَمَّا وَجَدۡنَا عَلَيۡهِ ءَابَآءَنَا وَتَكُونَ لَكُمَا ٱلۡكِبۡرِيَآءُ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَمَا نَحۡنُ لَكُمَا بِمُؤۡمِنِينَ

Suka ce: “Yanzu ka zo mana ne don ka raba mu da abin da muka sami iyayenmu a kansa, ku kuma (kai da Haruna) ku zamanto ku ne masu girma a bayan qasa? Mu kam ba za mu yi imani da ku ba!”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 79

وَقَالَ فِرۡعَوۡنُ ٱئۡتُونِي بِكُلِّ سَٰحِرٍ عَلِيمٖ

Fir’auna kuma ya ce: “Ku zo mini da duk wani qwararren matsafi.”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 80

فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلۡقُواْ مَآ أَنتُم مُّلۡقُونَ

To lokacin da matsafan suka zo, sai Musa ya ce da su: “Ku jefa duk abin da za ku jefa.”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 81

فَلَمَّآ أَلۡقَوۡاْ قَالَ مُوسَىٰ مَا جِئۡتُم بِهِ ٱلسِّحۡرُۖ إِنَّ ٱللَّهَ سَيُبۡطِلُهُۥٓ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يُصۡلِحُ عَمَلَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

To lokacin da suka jefa (kayan tsafinsu), sai Musa ya ce: “Ai abin da kuka zo da shi tsafi ne; lalle ko Allah zai vata shi. Lalle Allah ba Ya gyara aikin mavarnata



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 82

وَيُحِقُّ ٱللَّهُ ٱلۡحَقَّ بِكَلِمَٰتِهِۦ وَلَوۡ كَرِهَ ٱلۡمُجۡرِمُونَ

“Allah zai tabbatar da gaskiya da ikonsa ko da kuwa masu manyan laifuka sun qi.”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 83

فَمَآ ءَامَنَ لِمُوسَىٰٓ إِلَّا ذُرِّيَّةٞ مِّن قَوۡمِهِۦ عَلَىٰ خَوۡفٖ مِّن فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِمۡ أَن يَفۡتِنَهُمۡۚ وَإِنَّ فِرۡعَوۡنَ لَعَالٖ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَإِنَّهُۥ لَمِنَ ٱلۡمُسۡرِفِينَ

To ba wanda ya yi imani da Musa sai wasu ‘yan samari daga mutanensa don tsoron kada Fir’auna da mutanensa su azabtar da su. Kuma lalle Fir’auna ya tabbata mai girman kai ne a bayan qasa. Lalle kuma shi yana cikin mavarnata



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 84

وَقَالَ مُوسَىٰ يَٰقَوۡمِ إِن كُنتُمۡ ءَامَنتُم بِٱللَّهِ فَعَلَيۡهِ تَوَكَّلُوٓاْ إِن كُنتُم مُّسۡلِمِينَ

Musa kuma ya ce: “Ya ku mutanena, idan har kun yi imani da Allah, to a gare Shi kawai za ku dogara in kun kasance Musulmai



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 85

فَقَالُواْ عَلَى ٱللَّهِ تَوَكَّلۡنَا رَبَّنَا لَا تَجۡعَلۡنَا فِتۡنَةٗ لِّلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Sai suka ce: “Ga Allah kaxai muka dogara. Ya Ubangijinmu, kada ka sanya mu zama fitina ga mutane azzalumai



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 86

وَنَجِّنَا بِرَحۡمَتِكَ مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ

“Ka kuma tserar da mu da rahamarka daga mutane kafirai.”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 87

وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰ وَأَخِيهِ أَن تَبَوَّءَا لِقَوۡمِكُمَا بِمِصۡرَ بُيُوتٗا وَٱجۡعَلُواْ بُيُوتَكُمۡ قِبۡلَةٗ وَأَقِيمُواْ ٱلصَّلَوٰةَۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Kuma Muka yi wa Musa wahayi shi da xan’uwansa cewa: “Ku tanadar wa mutanenku gidaje a Masar, ku kuma sanya gidajenku wurin salla.” Ka kuma yi wa muminai albishir (da samun nasara)



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 88

وَقَالَ مُوسَىٰ رَبَّنَآ إِنَّكَ ءَاتَيۡتَ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَأَهُۥ زِينَةٗ وَأَمۡوَٰلٗا فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا رَبَّنَا لِيُضِلُّواْ عَن سَبِيلِكَۖ رَبَّنَا ٱطۡمِسۡ عَلَىٰٓ أَمۡوَٰلِهِمۡ وَٱشۡدُدۡ عَلَىٰ قُلُوبِهِمۡ فَلَا يُؤۡمِنُواْ حَتَّىٰ يَرَوُاْ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَلِيمَ

Musa kuma ya ce: “Ya Ubangijinmu, lalle Ka bai wa Fir’auna da mutanensa kayan ado da kuma dukiyoyi a rayuwar duniya; ya Ubangijimu, don su vatar (da jama’a) daga hanyarka; ya Ubangijimu, Ka shafe dukiyoyinsu Ka kuma qeqasar da zukatansu ba za su yi imani ba har sai sun ga azaba mai raxaxi.”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 89

قَالَ قَدۡ أُجِيبَت دَّعۡوَتُكُمَا فَٱسۡتَقِيمَا وَلَا تَتَّبِعَآنِّ سَبِيلَ ٱلَّذِينَ لَا يَعۡلَمُونَ

(Allah) Ya ce: “Haqiqa an amsa addu’arku, sai ku tsaya qyam (a kan tafarkinku), kada kuwa ku bi hanyar waxanda ba sa sanin (gaskiya).”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 90

۞وَجَٰوَزۡنَا بِبَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ ٱلۡبَحۡرَ فَأَتۡبَعَهُمۡ فِرۡعَوۡنُ وَجُنُودُهُۥ بَغۡيٗا وَعَدۡوًاۖ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَدۡرَكَهُ ٱلۡغَرَقُ قَالَ ءَامَنتُ أَنَّهُۥ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا ٱلَّذِيٓ ءَامَنَتۡ بِهِۦ بَنُوٓاْ إِسۡرَـٰٓءِيلَ وَأَنَا۠ مِنَ ٱلۡمُسۡلِمِينَ

Muka kuma qetarar da Banu Isra’ila kogi, sai Fir’auna ya bi su shi da rundunarsa don zalunci da ta’addanci, har sai lokacin da nutsewa ta riske shi sai ya ce: “Na yi imani cewa babu wani abin bauta sai wanda Banu Isra’ila suka yi imani da shi, kuma ni ina cikin Musulmai.”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 91

ءَآلۡـَٰٔنَ وَقَدۡ عَصَيۡتَ قَبۡلُ وَكُنتَ مِنَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

Sai yanzu kuma, bayan da can ka yi ta savo, ka kuma kasance cikin masu varna?



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 92

فَٱلۡيَوۡمَ نُنَجِّيكَ بِبَدَنِكَ لِتَكُونَ لِمَنۡ خَلۡفَكَ ءَايَةٗۚ وَإِنَّ كَثِيرٗا مِّنَ ٱلنَّاسِ عَنۡ ءَايَٰتِنَا لَغَٰفِلُونَ

To a yau kam za Mu tserar da gangar jikinka don ka zamanto aya ga na bayanka. Lalle kuwa yawancin mutane masu gafala ne ga lura da ayoyinmu



Surah: Suratu Hud

Ayah : 97

إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ فَٱتَّبَعُوٓاْ أَمۡرَ فِرۡعَوۡنَۖ وَمَآ أَمۡرُ فِرۡعَوۡنَ بِرَشِيدٖ

Zuwa ga Fir’auna da manyan fadawansa, sai suka bi umarnin Fir’auna; amma kuma umarnin Fir’auna ba a kan hanya yake ba



Surah: Suratu Hud

Ayah : 98

يَقۡدُمُ قَوۡمَهُۥ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ فَأَوۡرَدَهُمُ ٱلنَّارَۖ وَبِئۡسَ ٱلۡوِرۡدُ ٱلۡمَوۡرُودُ

Zai jagoranci mutanensa ranar alqiyama sai ya shigar da su wuta. Kuma tir da shiga wannan mashiga



Surah: Suratu Hud

Ayah : 99

وَأُتۡبِعُواْ فِي هَٰذِهِۦ لَعۡنَةٗ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ بِئۡسَ ٱلرِّفۡدُ ٱلۡمَرۡفُودُ

Aka kuma bi su da la’ana a wannan (duniyar) da kuma ranar alqiyama. Irin wannan kyauta kuwa da aka yi musu ta munana



Surah: Suratul Isra’i

Ayah : 101

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَىٰ تِسۡعَ ءَايَٰتِۭ بَيِّنَٰتٖۖ فَسۡـَٔلۡ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ إِذۡ جَآءَهُمۡ فَقَالَ لَهُۥ فِرۡعَوۡنُ إِنِّي لَأَظُنُّكَ يَٰمُوسَىٰ مَسۡحُورٗا

Kuma haqiqa Mun bai wa Musa ayoyi tara bayyanannu; to ka tambayi Banu Isra’ila lokacin da ya zo musu, sai Fir’auna ya ce da shi: “Lalle ni fa ina tsammanin kai Musa sihirtacce ne!”