Surah: Suratul Hajji

Ayah : 12

يَدۡعُواْ مِن دُونِ ٱللَّهِ مَا لَا يَضُرُّهُۥ وَمَا لَا يَنفَعُهُۥۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلضَّلَٰلُ ٱلۡبَعِيدُ

Yana bauta wa wanin Allah, abin da ba zai cuce shi ba kuma ba zai amfane shi ba. Wannan kuwa shi ne vata mai nisa



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 13

يَدۡعُواْ لَمَن ضَرُّهُۥٓ أَقۡرَبُ مِن نَّفۡعِهِۦۚ لَبِئۡسَ ٱلۡمَوۡلَىٰ وَلَبِئۡسَ ٱلۡعَشِيرُ

Yana bauta wa abin da cutarsa ta fi kusa fiye da amfaninsa. Tabbas mataimaki ya munana, kuma tabbas aboki ya munana



Surah: Suratul Ankabut

Ayah : 10

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَقُولُ ءَامَنَّا بِٱللَّهِ فَإِذَآ أُوذِيَ فِي ٱللَّهِ جَعَلَ فِتۡنَةَ ٱلنَّاسِ كَعَذَابِ ٱللَّهِۖ وَلَئِن جَآءَ نَصۡرٞ مِّن رَّبِّكَ لَيَقُولُنَّ إِنَّا كُنَّا مَعَكُمۡۚ أَوَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِأَعۡلَمَ بِمَا فِي صُدُورِ ٱلۡعَٰلَمِينَ

Kuma cikin mutane akwai mai cewa: “Mun yi imani da Allah,” to idan aka cuce shi a kan hanyar Allah sai yakan xauki fitinar mutane kamar azabar Allah, lalle kuwa idan wata nasara ta zo daga Ubangijinka, tabbas zai riqa cewa: “Lalle mu mun kasance tare da ku.” Yanzu Allah ba Shi Ya fi kowa sanin abin da ke cikin zukatan talikai ba?



Surah: Suratu Luqman

Ayah : 6

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يَشۡتَرِي لَهۡوَ ٱلۡحَدِيثِ لِيُضِلَّ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَيَتَّخِذَهَا هُزُوًاۚ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عَذَابٞ مُّهِينٞ

Daga mutane kuma akwai wanda yake sayen zantuka na sharholiya[1] don ya vatar (da mutane) daga hanyar Allah ba tare da wani ilimi ba, yana kuma riqon ta abar yi wa izgili. (Irin) waxannan azaba mai wulaqantarwa ta tabbata gare su


1- Watau kamar waqoqin banza da kaxa-kaxe da labaru marasa manufa, don ya shagaltar da mutane daga sauraren Alqur’ani, ya vatar da su daga addinin Allah.


Surah: Suratu Luqman

Ayah : 20

أَلَمۡ تَرَوۡاْ أَنَّ ٱللَّهَ سَخَّرَ لَكُم مَّا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ وَأَسۡبَغَ عَلَيۡكُمۡ نِعَمَهُۥ ظَٰهِرَةٗ وَبَاطِنَةٗۗ وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُجَٰدِلُ فِي ٱللَّهِ بِغَيۡرِ عِلۡمٖ وَلَا هُدٗى وَلَا كِتَٰبٖ مُّنِيرٖ

Yanzu ba kwa gani cewa Allah Ya hore muku abin da yake cikin sammai da kuma abin da yake cikin qasa, Ya kuma cika muku ni’imominsa na sarari da na voye? Daga mutane kuma akwai waxanda suke jayayya game da Allah ba tare da wani ilimi ko wata shiriya ba, ba kuma tare da wani littafi mai haskakawa ba



Surah: Suratu Luqman

Ayah : 21

وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱتَّبِعُواْ مَآ أَنزَلَ ٱللَّهُ قَالُواْ بَلۡ نَتَّبِعُ مَا وَجَدۡنَا عَلَيۡهِ ءَابَآءَنَآۚ أَوَلَوۡ كَانَ ٱلشَّيۡطَٰنُ يَدۡعُوهُمۡ إِلَىٰ عَذَابِ ٱلسَّعِيرِ

Idan kuma aka ce da su: “Ku bi abin da Allah Ya saukar”, sai su ce: “A’a, mu muna bin abin da muka sami iyayenmu ne a kansa.” Yanzu (sa yi haka) ko da Shaixan ya zamanto yana kiran su zuwa ga azaba ta (wuta) mai ruruwa?



Surah: Suratu Faxir

Ayah : 28

وَمِنَ ٱلنَّاسِ وَٱلدَّوَآبِّ وَٱلۡأَنۡعَٰمِ مُخۡتَلِفٌ أَلۡوَٰنُهُۥ كَذَٰلِكَۗ إِنَّمَا يَخۡشَى ٱللَّهَ مِنۡ عِبَادِهِ ٱلۡعُلَمَـٰٓؤُاْۗ إِنَّ ٱللَّهَ عَزِيزٌ غَفُورٌ

Daga mutane kuma da dabbobi da kuma dabbobin ni’ima su ma launinsu daban-daban ne kamar waxancan. Malamai ne kawai suke tsoron Allah daga bayinsa. Lalle Allah Mabuwayi ne Mai gafara



Surah: Suratuz Zukhruf 

Ayah : 54

فَٱسۡتَخَفَّ قَوۡمَهُۥ فَأَطَاعُوهُۚ إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَوۡمٗا فَٰسِقِينَ

Sai ya yi wasa da hankalin mutanensa sai suka bi shi. Lalle su sun kasance mutane ne fasiqai



Surah: Suratu Muhammad

Ayah : 38

هَـٰٓأَنتُمۡ هَـٰٓؤُلَآءِ تُدۡعَوۡنَ لِتُنفِقُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ فَمِنكُم مَّن يَبۡخَلُۖ وَمَن يَبۡخَلۡ فَإِنَّمَا يَبۡخَلُ عَن نَّفۡسِهِۦۚ وَٱللَّهُ ٱلۡغَنِيُّ وَأَنتُمُ ٱلۡفُقَرَآءُۚ وَإِن تَتَوَلَّوۡاْ يَسۡتَبۡدِلۡ قَوۡمًا غَيۡرَكُمۡ ثُمَّ لَا يَكُونُوٓاْ أَمۡثَٰلَكُم

To ga ku fa ku xin nan ana kiran ku don ku ciyar a hanyar Allah, to daga cikinku akwai masu yin rowa; wanda kuwa duk ya yi rowa, lalle ya yi wa kansa rowa ne. Allah kuma Mawadaci ne, ku ne mabuqata. Idan kuwa kuka ba da baya to zai canja wasu mutanen ba ku ba, sannan ba za su zama kamar ku ba



Surah: Suratul Hujurat

Ayah : 11

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا يَسۡخَرۡ قَوۡمٞ مِّن قَوۡمٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُونُواْ خَيۡرٗا مِّنۡهُمۡ وَلَا نِسَآءٞ مِّن نِّسَآءٍ عَسَىٰٓ أَن يَكُنَّ خَيۡرٗا مِّنۡهُنَّۖ وَلَا تَلۡمِزُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ وَلَا تَنَابَزُواْ بِٱلۡأَلۡقَٰبِۖ بِئۡسَ ٱلِٱسۡمُ ٱلۡفُسُوقُ بَعۡدَ ٱلۡإِيمَٰنِۚ وَمَن لَّمۡ يَتُبۡ فَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ

Ya ku waxanda suka yi imani, kada wasu mutane su yi wa wasu mutane izgili, mai yiwuwa ne su zamanto sun fi su alheri, kuma kada wasu mata (su yi wa) wasu mata (izgili), mai yiwuwa ne su zamanto sun fi su alheri; kada kuma ku riqa aibata junanku, kuma kada ku riqa jifan juna da munanan laquba (da kuke qi). Tir da sunan fasiqanci bayan imani. Wanda duk bai tuba ba, to waxannan su ne azzalumai



Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 14

۞أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ تَوَلَّوۡاْ قَوۡمًا غَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مَّا هُم مِّنكُمۡ وَلَا مِنۡهُمۡ وَيَحۡلِفُونَ عَلَى ٱلۡكَذِبِ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ

Shin ba ka ga waxanda suka yi abota da wasu mutane da Allah Ya yi fushi da su[1] ba, su ba cikinku suke ba, ba kuma cikinsu suke ba; su kuma riqa rantsuwa a kan qarya, alhali kuwa su suna sane (da yin ta)?


1- Su ne Yahudawa waxanda munafukai suke abota da su.


Surah: Suratul Mujadila

Ayah : 22

لَّا تَجِدُ قَوۡمٗا يُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ يُوَآدُّونَ مَنۡ حَآدَّ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ وَلَوۡ كَانُوٓاْ ءَابَآءَهُمۡ أَوۡ أَبۡنَآءَهُمۡ أَوۡ إِخۡوَٰنَهُمۡ أَوۡ عَشِيرَتَهُمۡۚ أُوْلَـٰٓئِكَ كَتَبَ فِي قُلُوبِهِمُ ٱلۡإِيمَٰنَ وَأَيَّدَهُم بِرُوحٖ مِّنۡهُۖ وَيُدۡخِلُهُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ رَضِيَ ٱللَّهُ عَنۡهُمۡ وَرَضُواْ عَنۡهُۚ أُوْلَـٰٓئِكَ حِزۡبُ ٱللَّهِۚ أَلَآ إِنَّ حِزۡبَ ٱللَّهِ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

Ba za ka tava samun wasu mutane da suke yin imani da Allah da ranar lahira ba, su riqa qaunar waxanda suke gaba da Allah da Manzonsa, ko da kuwa sun kasance iyayensu ne ko ‘ya’yansu ko ‘yan’uwansu ko kuma danginsu. Waxannan Allah Ya rubuta imani a cikin zukatansu, Ya kuma qarfafe su da wani ruhi daga wurinsa[1]; zai kuma shigar da su gidajen Aljanna (waxanda) qoramu suke gudana ta qarqashinsu, madawwama a cikinsu. Allah Ya yarda da su, su ma sun yarda da Shi. Waxannan ne qungiyar Allah. Ku saurara, lalle qungiyar Allah su ne masu samun babban rabo


1- Watau zai qarfafe su da wata hujja daga wurinsa da haske.


Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 1

وَيۡلٞ لِّلۡمُطَفِّفِينَ

Tsananin azaba ya tabbata ga masu tauye ma’auni



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 2

ٱلَّذِينَ إِذَا ٱكۡتَالُواْ عَلَى ٱلنَّاسِ يَسۡتَوۡفُونَ

Waxanda idan suka auna daga wajen mutane suna cikawa fal



Surah: Suratul Muxaffifin

Ayah : 3

وَإِذَا كَالُوهُمۡ أَو وَّزَنُوهُمۡ يُخۡسِرُونَ

Idan kuwa su za su aunar, da mudu ne ko da sikeli, to sai su tauye