Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 163

۞إِنَّآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡكَ كَمَآ أَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ نُوحٖ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ مِنۢ بَعۡدِهِۦۚ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطِ وَعِيسَىٰ وَأَيُّوبَ وَيُونُسَ وَهَٰرُونَ وَسُلَيۡمَٰنَۚ وَءَاتَيۡنَا دَاوُۥدَ زَبُورٗا

Lalle Mun yi maka wahayi irin wahayin da Muka yi wa Nuhu da kuma annabawan da suka biyo bayansa, kuma Mun yi wahayi ga Ibrahimu da Isma’ila da Ishaqa da Ya’aqubu da kuma jikokin (Ya’aqubu) da Isa da Ayyuba da Yunusa da Haruna da Sulaimanu; kuma Muka bai wa Dawuda littafin Zabura



Surah: Suratul An’am

Ayah : 84

وَوَهَبۡنَا لَهُۥٓ إِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَۚ كُلًّا هَدَيۡنَاۚ وَنُوحًا هَدَيۡنَا مِن قَبۡلُۖ وَمِن ذُرِّيَّتِهِۦ دَاوُۥدَ وَسُلَيۡمَٰنَ وَأَيُّوبَ وَيُوسُفَ وَمُوسَىٰ وَهَٰرُونَۚ وَكَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Kuma Muka ba shi Ishaqa da Ya’aqubu. Kowanne daga cikinsu Mun shiryar da shi, kuma Mun shiryar da Nuhu tun gabaninsu. Kuma daga cikin zurriyarsa akwai Dawudu da Sulaimanu da Ayyuba da Yusufu da Musa da Haruna. Kuma kamar haka ne Muke saka wa masu kyautata (ayyukansu)



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 142

۞وَوَٰعَدۡنَا مُوسَىٰ ثَلَٰثِينَ لَيۡلَةٗ وَأَتۡمَمۡنَٰهَا بِعَشۡرٖ فَتَمَّ مِيقَٰتُ رَبِّهِۦٓ أَرۡبَعِينَ لَيۡلَةٗۚ وَقَالَ مُوسَىٰ لِأَخِيهِ هَٰرُونَ ٱخۡلُفۡنِي فِي قَوۡمِي وَأَصۡلِحۡ وَلَا تَتَّبِعۡ سَبِيلَ ٱلۡمُفۡسِدِينَ

Mun kuma yi wa Musa alqawarin dare talatin, muka kuma cika su da goma, sai miqatin Ubangijinsa ya cika darare arba’in cif-cif. Sai Musa ya ce da xan’uwansa Haruna: “Ka wakilce ni a cikin mutanena, kuma ka daidaita (tsakaninsu), kada kuma ka bi tafarkin mavarnata.”



Surah: Suratul A’araf

Ayah : 150

وَلَمَّا رَجَعَ مُوسَىٰٓ إِلَىٰ قَوۡمِهِۦ غَضۡبَٰنَ أَسِفٗا قَالَ بِئۡسَمَا خَلَفۡتُمُونِي مِنۢ بَعۡدِيٓۖ أَعَجِلۡتُمۡ أَمۡرَ رَبِّكُمۡۖ وَأَلۡقَى ٱلۡأَلۡوَاحَ وَأَخَذَ بِرَأۡسِ أَخِيهِ يَجُرُّهُۥٓ إِلَيۡهِۚ قَالَ ٱبۡنَ أُمَّ إِنَّ ٱلۡقَوۡمَ ٱسۡتَضۡعَفُونِي وَكَادُواْ يَقۡتُلُونَنِي فَلَا تُشۡمِتۡ بِيَ ٱلۡأَعۡدَآءَ وَلَا تَجۡعَلۡنِي مَعَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّـٰلِمِينَ

Lokacin kuma da Musa ya dawo wajen mutanensa a fusace yana mai damuwa, sai ya ce: “Tir da abin da kuka aikata bayana. Yanzu kwa gaggauto al’amarin Ubangijinku?” Sai ya jefar da allunan, ya kama kan xan’uwansa yana jan sa zuwa gare shi. Sai (Haruna) ya ce: “Ya kai xan’ummata, mutanen nan haqiqa sun raina ni, har ma sun kusa kashe ni, don haka kar ka sa maqiya su yi min dariya, kuma kada ka sa ni cikin mutane azzalumai.”



Surah: Suratu Yunus

Ayah : 75

ثُمَّ بَعَثۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِم مُّوسَىٰ وَهَٰرُونَ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ بِـَٔايَٰتِنَا فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمٗا مُّجۡرِمِينَ

Sannan daga bayansu Muka aiko Musa da Haruna zuwa ga Fir’auna shi da jama’arsa da ayoyinmu, sai suka yi girman kai suka kuwa zamanto mutane masu laifi



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 53

وَوَهَبۡنَا لَهُۥ مِن رَّحۡمَتِنَآ أَخَاهُ هَٰرُونَ نَبِيّٗا

Kuma cikin rahamarmu Muka yi masa baiwa da xan’uwansa Haruna (shi ma) Annabi



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 29

وَٱجۡعَل لِّي وَزِيرٗا مِّنۡ أَهۡلِي

“Kuma Ka sanya mini waziri daga dangina



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 30

هَٰرُونَ أَخِي

“(Watau) xau’uwana Haruna



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 31

ٱشۡدُدۡ بِهِۦٓ أَزۡرِي

“Ka qarfafa gwiwata da shi



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 32

وَأَشۡرِكۡهُ فِيٓ أَمۡرِي

“Kuma Ka shigar da shi cikin lamarina[1]


1- Watau shi ma ya ba shi annabta ya aiko su tare.


Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 33

كَيۡ نُسَبِّحَكَ كَثِيرٗا

“Domin mu tsarkake Ka da yawa



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 34

وَنَذۡكُرَكَ كَثِيرًا

“Mu kuma ambace Ka da yawa



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 35

إِنَّكَ كُنتَ بِنَا بَصِيرٗا

“Lalle Kai Ka kasance Kana ganin mu.”



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 36

قَالَ قَدۡ أُوتِيتَ سُؤۡلَكَ يَٰمُوسَىٰ

(Allah) Ya ce: “Haqiqa an ba ka abin da ka tambaya, ya Musa



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 90

وَلَقَدۡ قَالَ لَهُمۡ هَٰرُونُ مِن قَبۡلُ يَٰقَوۡمِ إِنَّمَا فُتِنتُم بِهِۦۖ وَإِنَّ رَبَّكُمُ ٱلرَّحۡمَٰنُ فَٱتَّبِعُونِي وَأَطِيعُوٓاْ أَمۡرِي

Alhali kuwa haqiqa Haruna ya faxa musu tun da wuri cewa: “Ya ku mutanena, an jarrabe ku da shi ne kawai, kuma lalle Ubangijinku (na gaskiya) Shi ne Arrahamanu, sai ku bi ni kuma ku bi umarnina.”



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 91

قَالُواْ لَن نَّبۡرَحَ عَلَيۡهِ عَٰكِفِينَ حَتَّىٰ يَرۡجِعَ إِلَيۡنَا مُوسَىٰ

Suka ce: “Ba za mu gushe muna duqufa wajen bauta masa ba har sai Musa ya dawo mana.”



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 92

قَالَ يَٰهَٰرُونُ مَا مَنَعَكَ إِذۡ رَأَيۡتَهُمۡ ضَلُّوٓاْ

(Musa) ya ce: “Ya Haruna, me ya hana ka lokacin da ka gan su sun vace?



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 93

أَلَّا تَتَّبِعَنِۖ أَفَعَصَيۡتَ أَمۡرِي

“Ka bi ni (don ka sanar da ni)? Ko kuwa ka sava umarnina ne?”



Surah: Suratu Xa Ha

Ayah : 94

قَالَ يَبۡنَؤُمَّ لَا تَأۡخُذۡ بِلِحۡيَتِي وَلَا بِرَأۡسِيٓۖ إِنِّي خَشِيتُ أَن تَقُولَ فَرَّقۡتَ بَيۡنَ بَنِيٓ إِسۡرَـٰٓءِيلَ وَلَمۡ تَرۡقُبۡ قَوۡلِي

(Haruna) ya ce: “Ya xan’ummata, kada ka kama mini gemuna, da kuma (gashin) kaina; lalle ni na ji tsoron ka ce (da ni): ‘Ka rarraba kan Banu-Isra’ila, ba ka kuma kiyaye maganata ba.’”



Surah: Suratul Anbiya

Ayah : 48

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ ٱلۡفُرۡقَانَ وَضِيَآءٗ وَذِكۡرٗا لِّلۡمُتَّقِينَ

Haqiqa Mun ba wa Musa da Haruna (Attaura) mai rarrabewa (tsakanin qarya da gaskiya) da kuma haske da shiriya ga masu taqawa



Surah: Suratul Mu’uminun

Ayah : 45

ثُمَّ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ وَأَخَاهُ هَٰرُونَ بِـَٔايَٰتِنَا وَسُلۡطَٰنٖ مُّبِينٍ

Sannan Muka aiko Musa da xan’uwansa Haruna da ayoyinmu da kuma hujja bayyananniya



Surah: Suratul Mu’uminun

Ayah : 46

إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمًا عَالِينَ

Zuwa ga Fir’auna da manyan (‘yan majalisarsa), sai suka yi girman kai kuma suka kasance mutane masu haike wa (jama’a da zalunci)



Surah: Suratul Mu’uminun

Ayah : 47

فَقَالُوٓاْ أَنُؤۡمِنُ لِبَشَرَيۡنِ مِثۡلِنَا وَقَوۡمُهُمَا لَنَا عَٰبِدُونَ

Sai suka ce: “Yanzu ma ba da gaskiya da mutum biyu irinmu, alhali kuwa mutanensu masu yi mana bauta ne?”



Surah: Suratul Mu’uminun

Ayah : 48

فَكَذَّبُوهُمَا فَكَانُواْ مِنَ ٱلۡمُهۡلَكِينَ

Sai suka qaryata su (wato Musa da Haruna), sannan suka kasance daga waxanda aka hallaka



Surah: Suratul Furqan

Ayah : 35

وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ وَجَعَلۡنَا مَعَهُۥٓ أَخَاهُ هَٰرُونَ وَزِيرٗا

Haqiqa kuma Mun bai wa Musa Littafi muka kuma sanya xan’uwansa Haruna tare da shi a matsayin Waziri



Surah: Suratul Furqan

Ayah : 36

فَقُلۡنَا ٱذۡهَبَآ إِلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلَّذِينَ كَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا فَدَمَّرۡنَٰهُمۡ تَدۡمِيرٗا

Sai Muka ce: “Ku tafi zuwa ga mutanen da suka qaryata ayoyinmu, sai Muka hallaka su hallakarwa mai tsanani!”



Surah: Suratul Qasas

Ayah : 34

وَأَخِي هَٰرُونُ هُوَ أَفۡصَحُ مِنِّي لِسَانٗا فَأَرۡسِلۡهُ مَعِيَ رِدۡءٗا يُصَدِّقُنِيٓۖ إِنِّيٓ أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ

“Kuma xan’uwana Haruna shi ya fi ni fasahar harshe, sai Ka aike shi tare da ni ya zama mataimakina yana gaskata ni; lalle ni ina jin tsoron su qaryata ni.”



Surah: Suratul Qasas

Ayah : 35

قَالَ سَنَشُدُّ عَضُدَكَ بِأَخِيكَ وَنَجۡعَلُ لَكُمَا سُلۡطَٰنٗا فَلَا يَصِلُونَ إِلَيۡكُمَا بِـَٔايَٰتِنَآۚ أَنتُمَا وَمَنِ ٱتَّبَعَكُمَا ٱلۡغَٰلِبُونَ

(Sai Allah) Ya ce: “Za Mu qarfafa dantsenka da xan’uwanka kuma za Mu sanya muku wata hujja, don haka ba za su isa gare ku (da cuta) ba. Da ayoyinmu - ku da waxanda suka bi ku - ku ne masu yin galaba.”



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 114

وَلَقَدۡ مَنَنَّا عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ

Haqiqa kuma Mun yi ni’ima ga Musa da Haruna



Surah: Suratus Saffat

Ayah : 120

سَلَٰمٌ عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ

Aminci ya tabbata ga Musa da Haruna