Surah: Suratul Baqara

Ayah : 82

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ أُوْلَـٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡجَنَّةِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ

Waxanda kuma suka yi imani kuma suka yi ayyuka na qwarai, to waxannan ‘yan Aljanna ne, kuma su masu dawwama ne a cikinta



Surah: Suratu Ali-Imran

Ayah : 198

لَٰكِنِ ٱلَّذِينَ ٱتَّقَوۡاْ رَبَّهُمۡ لَهُمۡ جَنَّـٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا نُزُلٗا مِّنۡ عِندِ ٱللَّهِۗ وَمَا عِندَ ٱللَّهِ خَيۡرٞ لِّلۡأَبۡرَارِ

Amma waxanda suka bi dokokin Ubangijinsu suna da gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, za su dawwama a cikinsu, wannan liyafa ce ta musamman daga wajen Allah. Kuma abin da yake wajen Allah shi ne mafi alheri ga masu biyayya



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 13

تِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِۚ وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ يُدۡخِلۡهُ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ

Waxannan iyakoki ne na Allah. Wanda duk yake bin Allah da Manzonsa, to zai shigar da shi gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu. Kuma wannan shi ne rabo mai girma



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 57

وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ سَنُدۡخِلُهُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ لَّهُمۡ فِيهَآ أَزۡوَٰجٞ مُّطَهَّرَةٞۖ وَنُدۡخِلُهُمۡ ظِلّٗا ظَلِيلًا

Waxanda suka yi imani kuwa, kuma suka yi aiki nagari, to za Mu shigar da su gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har abada; suna da mata tsarkaka a cikinsu; kuma za Mu shigar da su cikin wata inuwa, inuwa mayalwaciya marar gushewa



Surah: Suratun Nisa’i

Ayah : 124

وَمَن يَعۡمَلۡ مِنَ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ مِن ذَكَرٍ أَوۡ أُنثَىٰ وَهُوَ مُؤۡمِنٞ فَأُوْلَـٰٓئِكَ يَدۡخُلُونَ ٱلۡجَنَّةَ وَلَا يُظۡلَمُونَ نَقِيرٗا

Kuma wanda ya yi wani aiki nagari, namiji ne ko mace, alhali yana mumini, to waxannan za su shiga Aljanna, kuma ba za a zalunce su gwargwadon xigon bayan qwallon dabino ba



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 85

فَأَثَٰبَهُمُ ٱللَّهُ بِمَا قَالُواْ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ وَذَٰلِكَ جَزَآءُ ٱلۡمُحۡسِنِينَ

Sai Allah Ya saka musu saboda abin da suka faxa, da gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dauwama a cikinsu, kuma wannan shi ne sakamakon masu kyautatawa



Surah: Suratul Ma’ida

Ayah : 119

قَالَ ٱللَّهُ هَٰذَا يَوۡمُ يَنفَعُ ٱلصَّـٰدِقِينَ صِدۡقُهُمۡۚ لَهُمۡ جَنَّـٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ رَّضِيَ ٱللَّهُ عَنۡهُمۡ وَرَضُواْ عَنۡهُۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ

Allah zai ce: “Wannan ita ce rana wadda gaskiya za ta amfani masu ita. Suna da gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, za su dawwama a cikinsu har abada. Allah Ya yarda da su, su kuma sun yarda da Shi. Wannan shi ne rabo mai girma.”



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 20

ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَهَاجَرُواْ وَجَٰهَدُواْ فِي سَبِيلِ ٱللَّهِ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡ أَعۡظَمُ دَرَجَةً عِندَ ٱللَّهِۚ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡفَآئِزُونَ

Waxanda suka yi imani kuma suka yi hijira suka yi jihadi saboda Allah da dukiyoyinsu da kawunansu su suka fi girman daraja a wurin Allah kuma waxannan su ne marabauta



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 21

يُبَشِّرُهُمۡ رَبُّهُم بِرَحۡمَةٖ مِّنۡهُ وَرِضۡوَٰنٖ وَجَنَّـٰتٖ لَّهُمۡ فِيهَا نَعِيمٞ مُّقِيمٌ

Ubangijinsu Yana yi musu albishir da rahama da yarda daga gare Shi, kana da gidajen Aljanna (waxanda) a cikinsu suke da ni’imomi masu xorewa



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 22

خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدًاۚ إِنَّ ٱللَّهَ عِندَهُۥٓ أَجۡرٌ عَظِيمٞ

Su madawwama ne a cikinsu har abada. Lalle lada mai girma yana wurin Allah



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 72

وَعَدَ ٱللَّهُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا وَمَسَٰكِنَ طَيِّبَةٗ فِي جَنَّـٰتِ عَدۡنٖۚ وَرِضۡوَٰنٞ مِّنَ ٱللَّهِ أَكۡبَرُۚ ذَٰلِكَ هُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ

Allah Ya yi wa muninai maza da muminai mata alqawarin gidajen Aljanna da qoramu suke gudana ta qarqashinsu suna masu dawwama a cikinsu, da kuma wuraren zama masu kyau a cikin gidajen Aljanna na dawwama. Yardar Allah kuwa ita ce fiye da komai. Wannan shi ne rabo mai girma



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 88

لَٰكِنِ ٱلرَّسُولُ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥ جَٰهَدُواْ بِأَمۡوَٰلِهِمۡ وَأَنفُسِهِمۡۚ وَأُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمُ ٱلۡخَيۡرَٰتُۖ وَأُوْلَـٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ

Sai dai shi Manzo da waxanda suka yi imani tare da shi sun yi yaqi da dukiyoyinsu da kuma kawunansu. Waxannan kuwa suna da alherai; kuma waxannan su ne marabauta



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 89

أَعَدَّ ٱللَّهُ لَهُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَاۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ

Allah Ya tanadar musu da gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu. Wannan shi ne rabo mai girma



Surah: Suratut Tauba

Ayah : 100

وَٱلسَّـٰبِقُونَ ٱلۡأَوَّلُونَ مِنَ ٱلۡمُهَٰجِرِينَ وَٱلۡأَنصَارِ وَٱلَّذِينَ ٱتَّبَعُوهُم بِإِحۡسَٰنٖ رَّضِيَ ٱللَّهُ عَنۡهُمۡ وَرَضُواْ عَنۡهُ وَأَعَدَّ لَهُمۡ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي تَحۡتَهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ

Magabata kuwa na farko daga cikin masu hijira da Ansaru[1] da kuma waxanda suka biyo bayansu da kyautatawa, (duka) Allah Ya yarda da su, su ma sun yarda da Shi, Ya kuma tanadar musu gidajen Aljanna da qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna madawwama a cikinsu har abada. Wannan shi ne rabo mai girma


1- Masu hijira su ne Musulmin da suka yiwo hijira daga Makka zuwa Madina. Ansaru kuwa su ne mutanen Madina waxanda suka karvi baquncin mutanen Makka, suka ba su matsugunnai.


Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 22

وَٱلَّذِينَ صَبَرُواْ ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ رَبِّهِمۡ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنفَقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ سِرّٗا وَعَلَانِيَةٗ وَيَدۡرَءُونَ بِٱلۡحَسَنَةِ ٱلسَّيِّئَةَ أُوْلَـٰٓئِكَ لَهُمۡ عُقۡبَى ٱلدَّارِ

Waxanda kuma suka yi haquri don neman yardar Ubangijnsu, suka kuma tsai da salla, kuma suka ciyar daga abin da Muka arzuta su da shi a voye da sarari, suke kuma ingije mummunan aiki da kyakkyawa, waxannan suna da (kyakkyawar) makoma ta gidan (Aljanna)



Surah: Suratur Ra’ad

Ayah : 23

جَنَّـٰتُ عَدۡنٖ يَدۡخُلُونَهَا وَمَن صَلَحَ مِنۡ ءَابَآئِهِمۡ وَأَزۡوَٰجِهِمۡ وَذُرِّيَّـٰتِهِمۡۖ وَٱلۡمَلَـٰٓئِكَةُ يَدۡخُلُونَ عَلَيۡهِم مِّن كُلِّ بَابٖ

Gidajen Aljanna na dawwama, za su shiga su da waxanda suka kyautata (aiki) daga iyayensu da matansu da kuma zuriyarsu; mala’iku kuma za su riqa shigowa wurinsu ta kowace qofa



Surah: Suratu Ibrahim

Ayah : 23

وَأُدۡخِلَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا بِإِذۡنِ رَبِّهِمۡۖ تَحِيَّتُهُمۡ فِيهَا سَلَٰمٌ

Aka kuma shigar da waxanda suka yi imani, suka kuma yi aiki nagari gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, suna masu dawwama a cikinsu da izinin Ubangijinsu; gaisuwarsu a cikinsu ita ce: “Aminci (ya tabbata a gare ku).”



Surah: Suratul Hijr

Ayah : 45

إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّـٰتٖ وَعُيُونٍ

Lalle masu kiyaye dokokin Allah suna cikin gidajen Aljanna da idanuwan (ruwa)



Surah: Suratul Hijr

Ayah : 46

ٱدۡخُلُوهَا بِسَلَٰمٍ ءَامِنِينَ

(A ce da su): “Ku shige ta lafiya lau kuna amintattu.”



Surah: Suratul Hijr

Ayah : 47

وَنَزَعۡنَا مَا فِي صُدُورِهِم مِّنۡ غِلٍّ إِخۡوَٰنًا عَلَىٰ سُرُرٖ مُّتَقَٰبِلِينَ

Muka kuma cire abin da ke cikin zukatansu na qullata (suka zama) ‘yan’uwa a kan gadaje suna fuskantar juna



Surah: Suratul Kahf 

Ayah : 107

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ كَانَتۡ لَهُمۡ جَنَّـٰتُ ٱلۡفِرۡدَوۡسِ نُزُلًا

Lalle waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari to Aljannar Firdausi[1] ita ce ta kasance masaukinsu


1- Aljannar Firdausi ita ce qololuwar Aljanna mafi daraja.


Surah: Suratul Kahf 

Ayah : 108

خَٰلِدِينَ فِيهَا لَا يَبۡغُونَ عَنۡهَا حِوَلٗا

Suna masu dawwama a cikinta, ba sa neman wani musaya da ita



Surah: Suratu Maryam

Ayah : 60

إِلَّا مَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَأُوْلَـٰٓئِكَ يَدۡخُلُونَ ٱلۡجَنَّةَ وَلَا يُظۡلَمُونَ شَيۡـٔٗا

Sai dai wanda ya tuba ya yi imani ya kuma yi aiki na gari, to waxannan za su shiga Aljanna, kuma ba za a tauye musu komai ba



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 14

إِنَّ ٱللَّهَ يُدۡخِلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَفۡعَلُ مَا يُرِيدُ

Lalle Allah Yana shigar da waxanda suka yi imani kuma suka yi aiki na gari gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu. Lalle Allah Yana aikata abin da Ya ga dama



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 23

إِنَّ ٱللَّهَ يُدۡخِلُ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ يُحَلَّوۡنَ فِيهَا مِنۡ أَسَاوِرَ مِن ذَهَبٖ وَلُؤۡلُؤٗاۖ وَلِبَاسُهُمۡ فِيهَا حَرِيرٞ

Lalle Allah Yana shigar da waxanda suka yi imani kuma suka yi ayyuka na gari gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, ana yi musu ado a cikinsu da awarwaro na zinare da kuma lu’ulu’u; tufafinsu kuwa a cikinsu alharini ne



Surah: Suratul Hajji

Ayah : 24

وَهُدُوٓاْ إِلَى ٱلطَّيِّبِ مِنَ ٱلۡقَوۡلِ وَهُدُوٓاْ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡحَمِيدِ

Kuma an shiryar da su zuwa ga magana mai daxi (a duniya, wato Kalmar Shahada), an kuma shiryar da su zuwa ga tafarkin (Allah) Sha-yabo



Surah: Suratud Dukhan

Ayah : 51

إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي مَقَامٍ أَمِينٖ

Lalle masu taqawa suna cikin wani amintaccen wuri



Surah: Suratul Fat’h

Ayah : 17

لَّيۡسَ عَلَى ٱلۡأَعۡمَىٰ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡأَعۡرَجِ حَرَجٞ وَلَا عَلَى ٱلۡمَرِيضِ حَرَجٞۗ وَمَن يُطِعِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ يُدۡخِلۡهُ جَنَّـٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۖ وَمَن يَتَوَلَّ يُعَذِّبۡهُ عَذَابًا أَلِيمٗا

Babu wani laifi a kan makaho, babu kuma wani laifi a kan gurgu, kuma babu wani laifi a kan marar lafiya (game da rashin fita yaqi). Wanda kuwa ya bi Allah da Manzonsa to zai shigar da shi gidajen Aljanna waxanda qoramu suke gudana ta qarqashinsu, wanda kuma ya ba da baya to zai azabtar da shi azaba mai raxaxi



Surah: Suratux Xur

Ayah : 17

إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّـٰتٖ وَنَعِيمٖ

Lalle masu tsoron Allah suna cikin gidajen Aljanna da ni’ima



Surah: Suratul Qamar

Ayah : 54

إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي جَنَّـٰتٖ وَنَهَرٖ

Lalle masu taqawa suna cikin gidajen Aljanna da qoramu