نَّحۡنُ أَعۡلَمُ بِمَا يَقُولُونَۖ وَمَآ أَنتَ عَلَيۡهِم بِجَبَّارٖۖ فَذَكِّرۡ بِٱلۡقُرۡءَانِ مَن يَخَافُ وَعِيدِ
Mu ne Muka fi sanin abin da (kafiran Makka) suke faxa; kuma kai ba mai tilasta musu ba ne; saboda haka sai ka yi wa’azi da Alqur’ani ga wanda yake tsoron azabata
وَذَكِّرۡ فَإِنَّ ٱلذِّكۡرَىٰ تَنفَعُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ
Kuma ka yi wa’azi, don ko lalle wa’azi yana amfanar muminai
وَٱصۡبِرۡ لِحُكۡمِ رَبِّكَ فَإِنَّكَ بِأَعۡيُنِنَاۖ وَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ حِينَ تَقُومُ
Kuma ka yi haquri da hukuncin Ubangijika, don ko lalle kana qarqashin lurarmu; kuma ka yi tasbihi da yabon Ubangijinka lokacin da za ka tashi (daga bacci)
وَمِنَ ٱلَّيۡلِ فَسَبِّحۡهُ وَإِدۡبَٰرَ ٱلنُّجُومِ
Da daddare kuma sai ka tsarkake Shi da kuma lokacin da taurari suka ba da baya
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ إِذَا جَآءَكَ ٱلۡمُؤۡمِنَٰتُ يُبَايِعۡنَكَ عَلَىٰٓ أَن لَّا يُشۡرِكۡنَ بِٱللَّهِ شَيۡـٔٗا وَلَا يَسۡرِقۡنَ وَلَا يَزۡنِينَ وَلَا يَقۡتُلۡنَ أَوۡلَٰدَهُنَّ وَلَا يَأۡتِينَ بِبُهۡتَٰنٖ يَفۡتَرِينَهُۥ بَيۡنَ أَيۡدِيهِنَّ وَأَرۡجُلِهِنَّ وَلَا يَعۡصِينَكَ فِي مَعۡرُوفٖ فَبَايِعۡهُنَّ وَٱسۡتَغۡفِرۡ لَهُنَّ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ
Ya kai wannan Annabi, idan muminai mata suka zo maka suna yi maka mubaya’a a kan ba za su yi shirka da Allah ba, kuma ba za su yi sata ba, ba kuma za su yi zina ba, kuma ba za su kashe ‘ya’yansu ba, kuma ba za su zo da wani qage ba wanda za su qirqira (game da xan da suka haifa) a tsakanin hannayensu da qafafuwansu[1], kuma ba za su sava maka ba game da wani aiki na kirki, to sai ka yi musu mubaya’a, ka kuma nema musu gafarar Allah. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin qai
1- Kamar yadda suke yi a jahiliyya idan mace ta yi zina da mazaje da yawa sai ta zavi xaya ta danganta masa xan da ta haifa.
وَأَطِيعُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُواْ ٱلرَّسُولَۚ فَإِن تَوَلَّيۡتُمۡ فَإِنَّمَا عَلَىٰ رَسُولِنَا ٱلۡبَلَٰغُ ٱلۡمُبِينُ
Ku bi Allah kuma ku bi Manzon. To idan kuka ba da baya to abin da yake kan Manzonmu kawai shi ne isar da aike
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ جَٰهِدِ ٱلۡكُفَّارَ وَٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱغۡلُظۡ عَلَيۡهِمۡۚ وَمَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ
Ya kai wannan Annabi, ka yaqi kafirai da munafukai, ka kuma tsananta musu. Makomarsu kuma Jahannama ce; makoma kuwa ta munana
إِلَّا بَلَٰغٗا مِّنَ ٱللَّهِ وَرِسَٰلَٰتِهِۦۚ وَمَن يَعۡصِ ٱللَّهَ وَرَسُولَهُۥ فَإِنَّ لَهُۥ نَارَ جَهَنَّمَ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدًا
“Sai dai isar da aike daga Allah da kuma saqwanninsa. Duk kuwa waxanda suka sava wa Allah da Manzonsa, to lalle suna da wutar Jahannama, suna madawwama a cikinta har abada.”
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡمُزَّمِّلُ
Ya kai wannan mai lulluva[1]!
1- Shi ne Manzon Allah () bayan an saukar masa da wahayin farko a kogon Hira, ya dawo gida a tsorace ya lulluva da tufafinsa.
قُمِ ٱلَّيۡلَ إِلَّا قَلِيلٗا
Ka yi tsaiwar dare sai xan kaxan (daga cikinsa)
نِّصۡفَهُۥٓ أَوِ ٱنقُصۡ مِنۡهُ قَلِيلًا
Rabinsa ko kuma ka rage kaxan daga gare shi
أَوۡ زِدۡ عَلَيۡهِ وَرَتِّلِ ٱلۡقُرۡءَانَ تَرۡتِيلًا
Ko ka qara a kansa, ka kuma karanta Alqur’ani daki-daki
إِنَّ لَكَ فِي ٱلنَّهَارِ سَبۡحٗا طَوِيلٗا
Lalle da rana kana da harkoki masu yawa
وَٱذۡكُرِ ٱسۡمَ رَبِّكَ وَتَبَتَّلۡ إِلَيۡهِ تَبۡتِيلٗا
Ka kuma ambaci sunan Ubangijinka kuma ka yanke alaqarka da komai don bautarsa
وَٱصۡبِرۡ عَلَىٰ مَا يَقُولُونَ وَٱهۡجُرۡهُمۡ هَجۡرٗا جَمِيلٗا
Kuma ka yi haquri a kan abin da suke faxa, kuma ka qaurace musu kyakkyawar qauracewa[1]
1- Watau qauracewar da babu cutarwa a cikinta.
يَـٰٓأَيُّهَا ٱلۡمُدَّثِّرُ
Ya kai mai lulluva[1]
1- Shi ne Annabi () wanda ya lulluva da tufafinsa don tsoron mala’ikan da ya yi idon huxu da shi a karon farko a kogon Hira.
قُمۡ فَأَنذِرۡ
Tashi ka yi gargaxi
وَرَبَّكَ فَكَبِّرۡ
Kuma ka girmama Ubangijinka
وَثِيَابَكَ فَطَهِّرۡ
Ka kuma tsarkake tufafinka
وَٱلرُّجۡزَ فَٱهۡجُرۡ
Ka kuma qaurace wa (bautar) gumaka
وَلَا تَمۡنُن تَسۡتَكۡثِرُ
Kada kuma ka goranta wa (Ubangijinka) da ganin yawan (ayyukanka na qwarai)[1]
1- Watau kada yawansu ya ruxe shi har ya yi rauni wajen tsayuwa da ayyukan da’awa.
وَلِرَبِّكَ فَٱصۡبِرۡ
Ka kuma yi haquri game da Ubangijinka
لَا تُحَرِّكۡ بِهِۦ لِسَانَكَ لِتَعۡجَلَ بِهِۦٓ
(Allah ya ce da Annabinsa): Kada ka motsa harshenka da shi (Alqur’ani) don gaggauta (karanta) shi
إِنَّ عَلَيۡنَا جَمۡعَهُۥ وَقُرۡءَانَهُۥ
Lalle tattara shi (a zuciyarka) da karanta shi yana kanmu
فَإِذَا قَرَأۡنَٰهُ فَٱتَّبِعۡ قُرۡءَانَهُۥ
Saboda haka idan Muka karanta (maka) shi sai ka bi karatunsa
ثُمَّ إِنَّ عَلَيۡنَا بَيَانَهُۥ
Sannan kuma bayaninsa yana kanmu
فَٱصۡبِرۡ لِحُكۡمِ رَبِّكَ وَلَا تُطِعۡ مِنۡهُمۡ ءَاثِمًا أَوۡ كَفُورٗا
Saboda haka ka yi haquri da hukuncin Ubangijinka kada kuwa ka bi mai yawan savo ko mai yawan kafircewa daga cikinsu
وَٱذۡكُرِ ٱسۡمَ رَبِّكَ بُكۡرَةٗ وَأَصِيلٗا
Ka kuma ambaci sunan Ubangijinka safe da yamma
وَمِنَ ٱلَّيۡلِ فَٱسۡجُدۡ لَهُۥ وَسَبِّحۡهُ لَيۡلٗا طَوِيلًا
Da daddare kuma sai ka yi sujjada a gare Shi, ka kuma yi nafiloli saboda Shi a tsawon dare
فَذَكِّرۡ إِن نَّفَعَتِ ٱلذِّكۡرَىٰ
To ka yi wa’azi idan wa’azin zai yi amfani