فَوَجَدَا عَبۡدٗا مِّنۡ عِبَادِنَآ ءَاتَيۡنَٰهُ رَحۡمَةٗ مِّنۡ عِندِنَا وَعَلَّمۡنَٰهُ مِن لَّدُنَّا عِلۡمٗا
To sai suka sami wani bawa daga bayinmu wanda Muka bai wa rahama daga gare Mu, kuma Muka koyar da shi wani ilimi daga wajenmu
قَالَ لَهُۥ مُوسَىٰ هَلۡ أَتَّبِعُكَ عَلَىٰٓ أَن تُعَلِّمَنِ مِمَّا عُلِّمۡتَ رُشۡدٗا
Musa ya ce da shi: “Shin na iya bin ka don ka koyar da ni (wani abu) daga abin da aka koyar da kai na shiriya?”
قَالَ إِنَّكَ لَن تَسۡتَطِيعَ مَعِيَ صَبۡرٗا
Ya ce: “Lalle ba za ka iya haquri da ni ba
وَكَيۡفَ تَصۡبِرُ عَلَىٰ مَا لَمۡ تُحِطۡ بِهِۦ خُبۡرٗا
“Qaqa kuwa za ka yi haquri kan abin da ba ka kewaye da saninsa ba?”
قَالَ سَتَجِدُنِيٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ صَابِرٗا وَلَآ أَعۡصِي لَكَ أَمۡرٗا
(Musa) ya ce: “Za ka same ni mai haquri in sha Allahu, ba kuma zan sava wa umarninka ba.”
قَالَ فَإِنِ ٱتَّبَعۡتَنِي فَلَا تَسۡـَٔلۡنِي عَن شَيۡءٍ حَتَّىٰٓ أُحۡدِثَ لَكَ مِنۡهُ ذِكۡرٗا
Ya ce, “To idan ka bi ni kada ka tambaye ni game da kowane abu har sai na ba ka labari game da shi.”
فَٱنطَلَقَا حَتَّىٰٓ إِذَا رَكِبَا فِي ٱلسَّفِينَةِ خَرَقَهَاۖ قَالَ أَخَرَقۡتَهَا لِتُغۡرِقَ أَهۡلَهَا لَقَدۡ جِئۡتَ شَيۡـًٔا إِمۡرٗا
Sai suka tafi, har lokacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, to sai ya huda shi; sai (Musa) ya ce: “Yanzu ka huda shi ne don ka nutsar da waxanda suke cikinsa? Haqiqa ka zo da babban abu.”
قَالَ أَلَمۡ أَقُلۡ إِنَّكَ لَن تَسۡتَطِيعَ مَعِيَ صَبۡرٗا
Ya ce: “Ban faxa maka ba cewa kai ba za ka iya haquri da ni ba?”
قَالَ لَا تُؤَاخِذۡنِي بِمَا نَسِيتُ وَلَا تُرۡهِقۡنِي مِنۡ أَمۡرِي عُسۡرٗا
(Musa) ya ce: “Kada ka kama ni da abin da na manta, kada kuma ka xora mini abu mai wahala game da al’amarina.”
فَٱنطَلَقَا حَتَّىٰٓ إِذَا لَقِيَا غُلَٰمٗا فَقَتَلَهُۥ قَالَ أَقَتَلۡتَ نَفۡسٗا زَكِيَّةَۢ بِغَيۡرِ نَفۡسٖ لَّقَدۡ جِئۡتَ شَيۡـٔٗا نُّكۡرٗا
Sai suka ci gaba da tafiya har dai suka gamu da wani yaro, to sai ya kashe shi, (Musa) ya ce: “Yanzu ka kashe rai tsarkakakke ba tare da (ya kashe) wani rai ba? Haqiqa ka zo da wani abu mummuna!”
۞قَالَ أَلَمۡ أَقُل لَّكَ إِنَّكَ لَن تَسۡتَطِيعَ مَعِيَ صَبۡرٗا
Ya ce: “Shin ban faxa maka cewa lalle kai ba za ka iya haquri da ni ba?”
قَالَ إِن سَأَلۡتُكَ عَن شَيۡءِۭ بَعۡدَهَا فَلَا تُصَٰحِبۡنِيۖ قَدۡ بَلَغۡتَ مِن لَّدُنِّي عُذۡرٗا
(Musa) ya ce: “Idan na sake tambayar ka wani abu bayansa, to kada ka tafi tare da ni; haqiqa ka sami (cikakken) hanzari a kaina.”
فَٱنطَلَقَا حَتَّىٰٓ إِذَآ أَتَيَآ أَهۡلَ قَرۡيَةٍ ٱسۡتَطۡعَمَآ أَهۡلَهَا فَأَبَوۡاْ أَن يُضَيِّفُوهُمَا فَوَجَدَا فِيهَا جِدَارٗا يُرِيدُ أَن يَنقَضَّ فَأَقَامَهُۥۖ قَالَ لَوۡ شِئۡتَ لَتَّخَذۡتَ عَلَيۡهِ أَجۡرٗا
Sai suka ci gaba da tafiya har suka iso ga mutanen wata alqarya, sai suka nemi mutanen alqaryar su ciyar da su, to sai suka qi su karvi baquntarsu, sai suka samu wani garu a alqaryar yana haramar rugujewa sai (Khadiru) ya tashe shi, sai (Musa) ya ce: “Da ka ga dama ai da sai ka karvi lada a kansa.” (Watau aikin tayarwar)
قَالَ هَٰذَا فِرَاقُ بَيۡنِي وَبَيۡنِكَۚ سَأُنَبِّئُكَ بِتَأۡوِيلِ مَا لَمۡ تَسۡتَطِع عَّلَيۡهِ صَبۡرًا
Ya ce: “Wannan ita ce rabuwata da kai. Zan ba ka labarin abin da ka kasa haquri a kansa.”
أَمَّا ٱلسَّفِينَةُ فَكَانَتۡ لِمَسَٰكِينَ يَعۡمَلُونَ فِي ٱلۡبَحۡرِ فَأَرَدتُّ أَنۡ أَعِيبَهَا وَكَانَ وَرَآءَهُم مَّلِكٞ يَأۡخُذُ كُلَّ سَفِينَةٍ غَصۡبٗا
“To game da shi jirgin ruwan nan ya kasance na wasu miskinai ne da suke aiki a cikin kogi, to sai na yi nufin in lalata shi domin kuwa a gabansu akwai wani sarki da yake qwace kowane jirgin ruwa (lafiyayye)
وَأَمَّا ٱلۡغُلَٰمُ فَكَانَ أَبَوَاهُ مُؤۡمِنَيۡنِ فَخَشِينَآ أَن يُرۡهِقَهُمَا طُغۡيَٰنٗا وَكُفۡرٗا
“To amma kuma game da shi yaron nan, iyayensa sun kasance muminai ne, sai muka ji tsoron kada ya afkar da su cikin shisshigi da kafirci
فَأَرَدۡنَآ أَن يُبۡدِلَهُمَا رَبُّهُمَا خَيۡرٗا مِّنۡهُ زَكَوٰةٗ وَأَقۡرَبَ رُحۡمٗا
“Sai muka yi nufin Ubangijinsu Ya musanya musu (wani xa) wanda ya fi tsarkaka ya kuma fi shi tausayi
وَأَمَّا ٱلۡجِدَارُ فَكَانَ لِغُلَٰمَيۡنِ يَتِيمَيۡنِ فِي ٱلۡمَدِينَةِ وَكَانَ تَحۡتَهُۥ كَنزٞ لَّهُمَا وَكَانَ أَبُوهُمَا صَٰلِحٗا فَأَرَادَ رَبُّكَ أَن يَبۡلُغَآ أَشُدَّهُمَا وَيَسۡتَخۡرِجَا كَنزَهُمَا رَحۡمَةٗ مِّن رَّبِّكَۚ وَمَا فَعَلۡتُهُۥ عَنۡ أَمۡرِيۚ ذَٰلِكَ تَأۡوِيلُ مَا لَمۡ تَسۡطِع عَّلَيۡهِ صَبۡرٗا
“To game da shi garun nan kuwa ya kasance na wasu yara ne marayu a cikin wannan birnin, a qarqashinsa kuwa da akwai wata taska tasu, mahaifinsu kuma ya kasance mutumin kirki ne, to sai Ubangijinka Ya nufi su girma su cika hankalinsu su, kuma fito da taskarsu, don rahama daga Ubangijinka. Ban aikata haka ba ne da raxin kaina. Wannan shi ne fassarar abin da ka kasa haquri a kansa.”
وَٱذۡكُرۡ فِي ٱلۡكِتَٰبِ مُوسَىٰٓۚ إِنَّهُۥ كَانَ مُخۡلَصٗا وَكَانَ رَسُولٗا نَّبِيّٗا
Ka kuma ambaci (labarin) Musa cikin (wannan) Littafi (Alqur’ani). Lalle shi zavavve ne, ya kuma kasance Annabi ne Manzo
وَنَٰدَيۡنَٰهُ مِن جَانِبِ ٱلطُّورِ ٱلۡأَيۡمَنِ وَقَرَّبۡنَٰهُ نَجِيّٗا
Muka kuma kira shi a gefen dutsen Xuri na dama, Muka kuma kusanto shi yana mai ganawa (da Mu)
وَوَهَبۡنَا لَهُۥ مِن رَّحۡمَتِنَآ أَخَاهُ هَٰرُونَ نَبِيّٗا
Kuma cikin rahamarmu Muka yi masa baiwa da xan’uwansa Haruna (shi ma) Annabi
وَهَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ مُوسَىٰٓ
Shin kuwa labarin Musa ya zo maka?
إِذۡ رَءَا نَارٗا فَقَالَ لِأَهۡلِهِ ٱمۡكُثُوٓاْ إِنِّيٓ ءَانَسۡتُ نَارٗا لَّعَلِّيٓ ءَاتِيكُم مِّنۡهَا بِقَبَسٍ أَوۡ أَجِدُ عَلَى ٱلنَّارِ هُدٗى
Lokacin da ya gano wuta sai ya ce da iyalinsa: “Ku zauna (a nan), lalle ni fa na hangi wuta, (zan je) ko na zo muku da garwashinta ko kuma in sami mai nuna mini (hanya) a wurin wutar.”
فَلَمَّآ أَتَىٰهَا نُودِيَ يَٰمُوسَىٰٓ
To lokacin da ya zo wurinta (wato wutar), sai aka kira shi (cewa): “Ya Musa
إِنِّيٓ أَنَا۠ رَبُّكَ فَٱخۡلَعۡ نَعۡلَيۡكَ إِنَّكَ بِٱلۡوَادِ ٱلۡمُقَدَّسِ طُوٗى
“Lalle Ni, Ni ne fa Ubangijinka, sai ka tuve takalmanka; lalle kana a tsarkakakken kwarin Xuwa ne
وَأَنَا ٱخۡتَرۡتُكَ فَٱسۡتَمِعۡ لِمَا يُوحَىٰٓ
“Kuma Ni Na zave ka (da manzanci), sai ka ji abin da za a yiwo ma wahayi (da shi)
إِنَّنِيٓ أَنَا ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّآ أَنَا۠ فَٱعۡبُدۡنِي وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ لِذِكۡرِيٓ
“Lalle Ni, Ni ne Allah, babu wani abin bauta sai Ni, to ka bauta mini, kuma ka tsai da salla don tuna Ni
إِنَّ ٱلسَّاعَةَ ءَاتِيَةٌ أَكَادُ أُخۡفِيهَا لِتُجۡزَىٰ كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا تَسۡعَىٰ
“Lalle alqiyama za ta zo, ina nufin voye ta ne don a saka wa kowanne rai da irin abin da yake aikatawa
فَلَا يَصُدَّنَّكَ عَنۡهَا مَن لَّا يُؤۡمِنُ بِهَا وَٱتَّبَعَ هَوَىٰهُ فَتَرۡدَىٰ
“To kada wanda bai yi imani da ita ba ya kuma bi son ransa ya hana ka gaskata ta, sai ka hallaka
وَمَا تِلۡكَ بِيَمِينِكَ يَٰمُوسَىٰ
“Mene ne kuma wancan yake a hannun damanka ya Musa?”